Bada'i(Canjawa)Bada

Mawallafi: Majma’al Alami Li AhlilBait (A.S)

Mafassari: Hafiz Muhammad Sa’id

“Allah yana shafe abin da yake so, kuma yana tabbatarwa, kuma a gunsa akwai Ummul Kitabi”

Surar Ra’adi: 39[1].

“Wanda ya raya cewa, Allah madaukakin sarki yana samun canaji a wani abu, da bai san shi ba jiya, to ka barranta da shi” [2].

Biharul Anwar: 4\111, H 30.

 

Gabatarwar Majma

Lallai yana daga cikin dabi’ar mutane su yi sabani a junansu, sai dai Allah yana son wannan sabanin ya takaita a cikin kewayen ingantaccen imani, saboda haka ne ba makawa ya zamanto akwai ma’auni tabbatacce da masu sabani zasu koma zuwa gare shi. Allah madaukakin sarki ya saukar da littafi da gaskiya domin ya yi hukunci tsakanin mutane da gaskiya cikin abin da suka saba a cikinsa[1].

Da babu wannan gaskiya guda daya, to da al’amarin rayuwa ba zai daidaitu ba, Wannan shi ne abin da Kur’ani yake tabbatar da shi kuma yake bisa ka’idar tauhidi, sannan sai daga baya aka samu karkata da sabani da camfe-camfe har mutane suka nisanta daga wannan asasi nisanta mai girma.

Ta haka ne ta bayyana cewa mutane ba su ne masu cancantar su yi hukunci da gaskiya ko karya ba matukar sun kasance suna iya biye wa son rai da bata da zalunci.

Duk da littafin Allah ya sauka da shiriya ya kuma isa zuwa ga mutane…. tare da hakan son rai ya rinjayi mutane nan da can, kwadayi da tsoro da bata suka nisantar da mutane ga karbar hukuncin littafi da komawa zuwa ga gaskiya da yake dawo da su zuwa gareta.

Bata shi ne ya jagoranci mutane a tsawon zamani zuwa ga sabani da shisshigi da kin Allah, Jahilci ya zama wani sababin sabani da rarraba, sai dai shi jahili ya kamata ne ya tambayi malamai kamar yadda Allah ya fada: “Ku tambayi ma’abota sani idan ba ku sani ba[2]”.

Ta haka ne ketare iyakar jahili ya kasance zalunci da shisshigi ga wannan asali wanda hankali yake amincewa da shi, kuma ma’abota hankula suke karkata zuwa gareshi, kuma lallai wannan shi ne mafi bayyanar ka’idoji da hanyoyi wadanda zasu toshe hanyar rarraba da sabani.1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 next