Tarihin Mace A Al'adu



Kuma ana iya bayar da rancen mace kamar kaya, ko sayarwa, ko bayarwa kyauta, ko biyan bashi, ko a matsayin haraji, haka nan ba ta tsira daga duka ko kisa ba.

Daga cikin dokokin Rumawa a kan mace shi ne: Ba ta dariya, ba zata ci nama ba, ba ta da ikon magana, shi ya sa ma akan sanya mata mukulli a baki, sannan suna ganin ba ta da komai sai hidima ga miji ko ubangida, kuma suna ganin ta a matsayin wasila ce da shedan yake amfani da ita wajan halakar da mutane[11].

Farisawa Da Larabawa Da Yunan

Amma Yunan da Yankin Larabawa da Tsohuwar Iran a wajansu gida da maza ne ake lissafinsa ba da mata ba, har ma kusancin da a kansa ake gado[12] da maza ne ake la’akari ba mata ba, babu kusancin da ya shafi mace da ake kiyaye shi, kamar na uwa, ko ‘ya, ko ‘yar’uwa, kusancin mace da ake kiyaye wa kusanci ne na dabi’ar jinsi [saduwa] da haihuwa, da auratayya.

Mace A Gun Larabawa

A al’adun Larabawa idan ‘ya tana gidan uba ko miji suna iya yin duk abin da suka ga dama da ita, kimar mace hatta ta ranta ba ta da wani alfarma, duba mana ka gani farkon shahidi a Musulunci mace ce.

Dukiyarta ta namiji ce koda kuwa sadakinta ne, kuma koda kuwa kasuwanci ta yi, balle gado da haramun ne a gare ta, uba ko dan’uwa shi ne zai aurar da ita ko ta ki ko ta so, wannan al’adun na Jahiliyyar larabawa da akwai tsammanin cewa irin su ne suka shiga wasu yankunanmu da sunan Musulunci.

Jaririya kuwa ko yarinya ba ta tsira daga binnewa da ranta ba, suna ganin halittar mace aibi ne, da musifa, da bala’i garesu[13], musamman ma idan an ribace ta a yaki, a wajansu wannan wani aibi ne da babu kamarsa, don haka a binne ta ma da rai don kada ta taso ta zama aibi ga al’ummarsu.

An ce farkon wadanda suka binne ‘ya mace su ne Bani tamim sannan sauran larabawa suka dauka, wannan ya kasance ne sakamakon ribace su da sarki Annu’uman dan Munzir ya yi ne[14], sai wannan abu ya fusata su suka fara binne na raye da ransu, haka nan idan aka yi wa wani albishir[15] da ‘ya mace sai ka ga yana buya daga mutane don kunya na abin aibi da ya samu, amma idan namiji ne yana mai farin ciki komai yawansu, wannan ma ba ya isar sa har sai ya yi da’awar dan zina ma cewa nasa ne, har ma ya kan iya kai wa ga yaki ko fada a kan ‘ya’yan zina[16].

Amma wasu lokuta wasu gidaje sukan ba wa mace dama ta auri wanda take so, ko yaya dai, mu’amalarsu da mata mu’amala ce da ta cakuda da ta al’adun daulolin da suke kewaye da kasashen larabawa kamar Iran da Rum.



back 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14 15 next