Boyayyar TaskaBoyayyar Taska

Hafiz Muhammad Sa’id

hfaza@yahoo.com

Kuma muka yayyanka su sibdi goma sha biyu, al’ummu….[1].

Gabatarwar Mawallafi

A wannan littafi muna so mu yi nuni da wasu matakai da marhaloli da wahalhalu da Wasiyyan Annabawa (A.S) suka shiga tun daga wancan lokaci har zuwa irin wannan zamani namu, da matakan da mutane sukan dauka a kan abin da yakan faru a kowane lokaci na rarraba da daukar bangare daban-daban, al’amarin da yakan raba al’ummu gida biyu a Tarihin al’ummu da suka gabata.

Da yake mutane a kowane zamani hali daya ne da su al’ummar karshe ta Manzon Allah (S.A.W) ba ta fita daga irin wannan ba, shi ya sa aka samu sabani da ya kai su ga rarraba zuwa mazhabobi da sabanin akidu. Amma wani abin da za a gode wa Allah shi ne; al’ummar nan ta bambanta da sauran al’ummu, domin su wadancan al’ummu bayan sun yi nesa da Wasiyyan Annabawan sukan kuma yi rashin sa’ar canza Addinin nasu gaba daya kuma a kautar da Akidunsu daga sahihancinta[2], amma wannan al’umma Allah (S.W.T) da ludufinsa ya yi alkawarin kare littafinta, da ba ya karbar canji har kiyama ta tashi, wanda Ahlussunna da Shi'a duk sun hadu a kan hakan.

Ambaton wannan littafi da “Boyayyar Taska” ya zo ne domin wasu dalilai kamar haka;

1-     Bincike domin gano wace taska ce Annabi Muhammad (S.A.W) ya bari wacce mutum ya nutsu har ga Allah da cewa idan ya mutu a kanta ya kubuta. Amma a gane, duk wanda yake kan wata hanya ko wata Mazhaba ba shi da ikon cewa lallai shi kadai ne a kan gaskiya sauran duka sun tabe wuta zasu, domin bai sani ba tayiwu nasu ya fi nasa gamdakatar. Domin haka ne dole a kiyaye hadin kai tsakanin juna da zamantakewa tare da girmama mazhaba da Ra’ayin juna. Muna fatan kafa wani kwamiti na musamman da zai kunshi majalisa ta malamai da ta kunshi malaman kowane mazhaba domin tabbatar da hadin kan al’umma.

2-     Karin haske game da wasu dalilai da mabiya Ahlul Baiti (A.S) suke riko da su daga Kur’ani da Sunna domin samar da karin fahimtar dalilansu game da riko da tafarkinsu, duk da ya kasance a takaice ne kwarai da gaske amma an ce: “Da babu gwara kadan”.1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14 15 16 17 18 19 20 21 22 23 24 25 26 27 28 29 30 31 32 33 34 35 36 next