Hakkoki A Musulunci



Sannan ya rufe maganarsa da cewa: “Idan ka aikata haka to ka hada soyayyarka da soyayyarsa, kuma soyayyarsa da soyayyarka”.

Akwai hadisai da yawa da suka kunshi ma’anar da ta zo a wannan hadisi daga imamanmu (A.S), wasunsu daga littafin Wasa’il a babobi daban-daban.

Tayiwu wasu su yi tsammanin cewa abin nufi da ‘yanuwantaka a hadisin Ahlul Baiti (A.S) ya kebanci tsakanin musulmi ne wadanda suke daga mabiyansu a kebance, amma komawa ga ruwayoyinsu yana kawar da wannan zato, koda yake sun kasance ta wani bangare suna tsananta musantawa ga wanda ya sabawa tafarkinsu kuma ba ya riko da shiriyarsu. Ya wadatar ka karanta hadisin Mu’awiya Dan Wahab da ya ce[53]:

Na ce masa[54]: Yaya ya kamata gare mu mu yi tsakaninmu da mutanenmu, da kuma wadanda muke cudanya da su na daga mutane wadanda ba sa kan al’amarinmu”.

Sai Ya ce: “Ku duba Imamanku wadanda kuke koyi da su ku yi yadda suke yi, na rantse da Allah! su suna gaishe da maras lafiyarsu, suna halartar jana’izarsu, suna ba da shaida garesu da kuma a kansu, kuma suna bayar da amana garesu”.

Amma ‘yan’uwantakar da Imamai suke son ta daga mabiyansu, tana saman wannan ‘yan’uwantaka ta musulunci, Kuma ya isar ka karanta wannan muhawara tsakanin Abana Bn Taglib da Imam Sadik (A.S) daga hadisin[55] da Abana ya rawaito da kansa yana mai cewa: Na kasance ina dawafi tare da Abi Abdullah (A.S) sai wani mutumi daga cikin mutanenmu ya bujuro mini wanda ya riga ya tambaye ni in raka shi wata biyan bukatarsa, sai ya yi mini ishara, sai Abu Abdullahi (A.S) ya gan mu.

Sai ya ce: Ya Abana kai wannan yake nema?

Na ce: Na’am.

Ya ce: Shin yana kan abin da kake kai?

Na ce: Na’am.



back 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14 15 16 17 18 19 20 21 22 23 24 25 26 27 28 next