Auren Mace Fiye Da Daya



1-Nagetib yana da karfin tafiyar da komai wanda shi pozitib ba shi da shi, shi ya sa siffofinsa suka fi karfi da rinjaye.

2 – Da nagetib ana iya gane dan waye ba da pozitib ba, shi ya sa da mace za ta zowa namiji biyu ba yadda za ta iya sanya su su dauki ciki, kai koda sun kai maza dubu ne ba ta iya yi wa ko dayansu ciki balle ta tara ‘ya’ya ko ta tara zuriya da zasu iya dangantuwa zuwa gareta. Kuma kana iya kaddara gida da za a ce maza hudu ne duk a gidan da mace daya mijinsu ce da ta aure su da abin ya zama sabanin dabi’ar Dan Adam. A wannan yanayi Dan Adam a bisa dabi’arsa yakan zama masa abin mamaki kuma sabanin dabi’a. Sannan danta na waye a cikinsu? Da hakan zai kasance da fitina da fasadi mafi girma sun faru a tarihin dan Adam.

3- Nagetib shi yake iya juya al’amuran al’umma don yana iya dauke nauyin Duniya a kansa amma pozitib yana da iyaka kuma yana da rauni, kuma ya doru ne kan waninsa sai abin da aka ba shi, shi ya sa ma a musulunci ba yadda za a yi mace ta zama shugaba a kan gida.

Namiji shi yake iya daukar nauyin yaki da daukar nauyi, da kare kasa, da tafiye tafiye, da sayar da rai, amma mace ita jikinta laushi ne, da kyau, da ado, shi ya sa Jamalul-Lahi (kyawu da adon Allah) ya bayyana a kanta, kamar yadda Jalalul-Lahi (kwarjinin Allah) ya bayyana a kan namiji, tsakanin Jalal da Jamal kuwa akwai banbanci domin Jalal nagetib ne amma Jamal pozitib ne, shi ya sa ma ake cewa da wadancan siffofin korewa amma wadannan akan ce da su na tabbatarwa[11].

Kasancewar namiji nagetib wannan ya sanya shi da dabi’ar dandano, shi ya sa ba kasafai wasu kan iya isa da mace daya ba, amma mace abin da take nema shi ne gamsuwa, in ko ta samu wannan to tana isuwa da namiji daya, haka nan Allah yayi halittunsa bisa hikima daidai da dabi’arsu.

Abin da ya sa musulunci ya sanya wannan dokoki don yana son a yi rayuwa ta hankali ne ba kawai ta dabi’ar zuciya ba, domin dabi’ar zuciya kamar so da ki duk da ana bukatarsu kuma suna da na su amfani domin so shi ne asasin addinan Allah amma ba a bar su haka nan ba, domin suna da wata akala da ake daure su da ita wato hankali, sai ya zama so ba laifi ba ne, amma idan zaka yi shi sai ya zama bisa hankali, kuma bisa doka, kuma don Allah, haka ma sha’awa da sauransu.

Nazarin Hegel kan nagetib da pozitib duk da ya yi amfani da shi a Falsafarsa wacce ita ce Mandik dinsa kuma Karl Maks ya yi amfani da shi a nazarinsa na tarihin canjin rayuwar dan Adam da fada tsakanin masu arziki da ma’aikata a tsarin tattalin arziki, don haka ne na yi amfani da shi game da yanayin halittar jinsin maza da mata.

Kuma muna iya karawa da cewa[12]; idan muka koma a ka’idar mandik shi namiji jagora ne amma mace mafari ce, ana kuma auna mafari ne da jagora domin samun hukuncinsa. Haka nan aka halicci dabi’arta, shi ya sa take bukatar kariya ta musamman daga namiji da dogaro da shi a abubuwa da dama domin cimma hadafin samar da mu da Allah ya yi, amma shi namiji yakan iya daukar nauyin mata masu yawa a kansa.

Mutum Yana Bukatar Tsari Da Doka

Musulunci ba ya son barin mutum a rayuwa ta gwauranci ko a sake irin wanda su masu sukan suke so, sannan yana son yawaita musulmi musamman a wancan lokuta da karancinsu ya yawaita[13]. Saboda haka masu sukan da sun yi tunani da su suka fi cancanta da suka da zargi su da suka yardar wa dan Adam rashin iyaka ga sha’awarsa, ta yadda yana iya zuwa ya ajiye sha’awarsa ga wacce ya so a duk inda ya so.

 Shi ya sa musulunci ya gindaya doka da tsari don ya zama ta hanyar halal, kuma da wannan ne za a san dan kowa da yake dangantuwa zuwa gareshi, domin rashin sanin salsalar mutum yana daga cikin bala’i a kasa, kuma yakan kawo barna, da fasadi, da lalacewa mai girma.



back 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14 15 16 17 next