Auren Mace Fiye Da Daya



Raddin Sukan Auren Mace Fiye Da Daya

Hafiz Muhammad Sa’id

hfaza@yahoo.com

Kuma idan kuka ji tsoron ba zaku yi adalci ba a game da marayu, to sai ku auri abin da ya yi muku dadi daga mata, biyu-biyu, ko uku-uku da hudu-hudu, amma idan kuka ji tsroron ba zaku yi adalci ba, to (ku auri mace) daya ko abin da hannayenku suka mallaka…[1].

Gabatarwar Mawallafi

Muna godiya ga Allah da ya ba ni damar rubuta wannnan littafi da na rubuta mai suna “Raddin Sukan Auren Mace Fiye Da Daya” kuma mai muhimmanci matuka a wajena saboda abin da ya kunsa na kariya ga Manzo (S.A.W) da kuma Addinin Musulunci musamman abin da ya shafi Auratayya da kuma Raddi kan sukan yawaitar matan Mafificin halitta.

Mun yi amfani da misalai domin cimma abin da muke son isarwa na fahimtarsa don kawar da shubuha da soke-soke da ake jifan musulunci da su, kuma da saukaka karanta shi ta yadda kowa zai iya karantawa kuma ya fahimta. Mun sanya yawancin dalilai da muke kawo wa domin tabbatar da hujjarmu da misalai da yawa a littafin domin ya zama ya fi dadin karantawa ga masu karatu.

 Muna son tunatar da masu karatu cewa wannan littafin an rubuta shi domin kowane irin mutum ya karanta shi koda ba musulmi ba ne, don haka idan ya saba wa mazhabarka sai ka sani yana kariya ga musulunci ne ba tare da la’akari da mazhaba ba.  Ina rokon Allah ya bayar da ladan rubuta wannan littafi ga Dan’uwana Ahmad Muhammad ya haskaka kabarinsa da shi.

Hafiz Muhammad Sa’id Kano Nigeria

 hfazah@yahoo.com

Rabi’ul Awwal 1424

Khurdad 1382

 Mayu 2003

Soke-Soke A Kan Auren Mace Fiye Da Daya

A wannan littafi zamu yi kokarin amsa wasu daga cikin soke-soke da ake jifan Musulunci da su a kan mas’aloli kamar haka.



1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14 15 16 17 next