Jagorancin Imam Sadik (a.s)



Shekara goma sha tara ana gudanar da wannan tafiya mai tattare da kaya da munin hanya wanda yake bukatar kokari da ijtihadi mai yawa. Lokacin da wadannan shekaru suka kawo karshe, ranar rayuwarsa mai albarka ta zo faduwa, sai abokan gabansa suka yi ajiyar zuciya domin a zatonsu idan wannan jagora mai shiryarwa ya tafi za su huta da tushen farkarwa da izawa wanda ya dade yana hana su hutu da barci.

Amma hakan bai yiwu ba domin Imam ya tabar da burinsu ya kuma sa wannan dama ta kubuce  musu saboda ya sanya wafatinsa ya zama tushen shiryarwa, musabbabin farkawa sannan kuma hanyar wayar da kai mai dorewa. Imam ya umarci dan sa Sadik(a.s) a karshen rayuwarsa, ya umarce shi da wani aiki wanda samfuri  ne mai gwanin ban  sha’awa daga samfur-samfur na takiyya da kuma salon kira wadanda Imam Bakir (a.s) ya yi amfani da su  a zangon zamani  wanda ya kebance shi . A cikin ruwaya daga Abu Abdillah Sadik (a.s)  ya ce: ‘Babana ya ce da ni: Ka ware abu kaza daga dukiyata saboda a mini zaman makoki  na tsawon shekara goma a Mina a ranakun Minan”.[25]  ..Ita wannan ruwaya , wadanda suka yi bincike kan rayuwar Imam Bakir basu dube ta da kyau ba kuma sun gafala ga barin ma`anoni masu girma wadanda ta kunsa.  Imam ya rasu ya bar dirhami dari takwas, yayi umarni da aware wani abu daga ciki a baiwa masu kukan mutuwarsa a Mina. Yin kukan rasuwar Imam a Mina ya kunshi ma`ana mai girma .Lallai shi aiki ne na raya tushen nan da ya kasance a ko yaushe yana watsa hasken wayar da kai da farkarwa da kuma sanya ruhin kamuji da gwagwarmaya.

Zaben Mina kuwa yana nufin wanzar da aikin a tsakiyar taron jama`a masu tahowa daga dukkanin sassan duniyar musulunci a dai dai lokaci guda daya tak da ake zaune wuri guda yayin aikin haji. Saboda dukkan ayyukan haji ana gabatar da su ne cikin halin motsawa ba tare da sararawa ba idan ba a Mina ba, inda ake kwana biyu ko uku, saboda  haka alhazai suna samun isashshen lokaci domin sauraro da ganin kukan rasuwar Imam a wannan wuri zai kuma sa a yi tambaya kan ko wane ne wannan mamacin? Za’a kuma sami jawabi wajen mutanen Madina wadanda suka yi zamani da shi. Za su ce shi daya daga ‘ya’yan Manzon Allah ne, kuma shi ne malamin fukaha`u da masana hadisi. Za’a kuma tambayi dalilin da ya sa ake makokinsa a wannan guri, shin mutuwarsa ta bambanta da ta saura ne? To wane ne ya kashe shi ko ya sanya masa guba? Shin ya kasance wata barazana ga mulkin Umayyawa ne? Da dai sauran su. Gomonin tambayoyi aka yi ta jefowa yayin da ake kukan rasuwar Imam a wannan wuri, sannan masu tambaya suna samun amsa. Kuma labarin ya yi ta watsuwa cikin garuruwa, sako sako, bayan komawar alhazai kasashensu. Akwai kuma masu zuwa daga Kufa da Madina takanas saboda amsa wadannan tambayoyi da yada ruhin shi’a suna daukar damar taron musulmi, damar da ba’a samun tamkar ta a wancan lokacin.

 Haka Imam ya rayu, haka kuma ya tsara al’amura domin abin da zai zo bayan wafatinsa. Tsira ta tabbata gare shi ranar da aka haife shi da ranar da ya yi jihadi da ranar da ya yi shahada a tafarkin Allah da kuma ranar da za’a tashe shi rayayye.

Imam Bakir (a.s) ya rasu yana da shekara hamsin da bakwai a duniya,  a zamanin Hisham bin Abdulmalik, wanda yake daya ne daga sarakunan Banu Umayya wadanda suka fi iko. Duk da matsaloli da wahalhalun da suka addabi sarautar Banu Umayya a wancan zamanin wannan bai hana su aikata makida ga zuciyar shi’an nan mai bugawa, watau Imam Bakir, ba. Hisham ya yi ishara ga barorinsa cewa su sanya wa Imam guba, da haka ne kuma ya cimma burinsa na hallaka mafi hadarin abokan gabansa.

JOGARANCIN IMAM SADIK (A.S).

Imam Sadik (a.s) ya dauki nauyin ci gaba da wannan tafiya a cikin yanayi mai tsananin sarkakiya da wahala.

Bore ya kunno kai a ko ina a daular musulunci, hakimai sun shagaltu da tara kazamar dukiya alhali ga annoba da fari sun aukawa yanki mai yawa wanda ya hada da Kurasan da Irak. Masu mulki kuwa suna tursasawa da zalunci ba tare da rahama ba ko kankani, da haka suke jefa mutane cikin halin kaskanci da mika wuya. Kuma galibi hadarin masu shagaltuwa da ilmomin musulunci kamar fikihu da hadisi da tafsiri bai kasa na ‘yan siyasa da mahukunta ba. Alhali kuwa su ake tsammanin zamansu mafaka ga mutane. Yawa yawan wadannan malamai na kawata fatawowi saboda dadada wa sarki da hakimansa. Da yawa daga cikinsu suna shagaltar da kansu da ma mutane da mas’alolin da basu taka kara sun karya ba, suna ta da jayayyar da ba bakin komai take ba cikin mas’alolin ilmul kalam kuma babu abin da ya danganta ta da musulunci ko wahalhalun da al’umma ke ciki.

Nauyin da ya rataya a wuyan Imam Sadik (a.s) a wannan yanayi mai duhu shi ne abin da muka ambata kan sha’anin nauyin imamanci.A takaice shi ne bijiro da ingantaccen tunanin musulunci, watau bayyana musulunci kamar yanda ya zo cikin Alkur’ani dasunnarMa’aiki(s.a.w.a) gami da yaki da dukkanin baude-baude da gurbatarwar jahiliyya mai bin son rai. Haka nan kuma da shirya dabarun kafa tsarin adalcin musulunci da kuma kare wannan tsarin yayin kafa shi.Duk wannan nauye-nauye guda biyu watau nauyin wanzar da tsarin tunani da nauyin tsarin siyasa suna matsayin wani hadari mai girma ne ga tsarin da yake mulki. Ba nauyin siyasa kadai yake tunzura fushin sarauta ba, a’a shi ma nauyin tsarin tunani wanda yake jifa da baudaddun tunane-tunane da manufofin da sarki da  masu wa’azinsa ke gabatar wa al’umma da sunan addini, yana fusata ta. Wannan ya nuna cewa aikin kyautata tunani abin fifitawa ne domin yana kawar da karkatarwa da sunan addini wacce tsarin sarauta ke dogaro da ita wajen wanzarda zaluncin da yake yi wa jama’a. Ta wata fuska kuma yanayin da ake cikinsa a shirye yake ya saurari tunanin shi’a mai  neman sauyi, domin yaki da talauci da danniya sabubba ne masu habaka ruhin sauyi, ga kuma share fage da ayyukan Imam Bakir (a.s) suka yi a yankuna dabam-dabam. Dabarar cimma manufar Imamanci a game ita ce yunkurin sauyin tauhidi irin na Imam Ali. Bukatunta su ne:-Na farko: Samarda wata jama’a wacce za ta dauki tunanin imamanci, ta yanda zai saje da ita, sannan ta zama mai begen aiwatar da shi.

Na biyu: Samar da wata jama’a tsararriya mai jihadi da sadaukarwa. Shi kansa cimma wadannan bukatu yana bukatar yada kiran gaskiya a sassan duniya da shirya zukata domin karbar tunanin musulunci mai ra’ayin sauyi a dukkanin wurare. Har ila yau yana bukatar wani kiran daban wanda zai tanadi daidaiku masu sadaukarwa da fana’i, wadanda za su zama mambobin shirin tsare-tsaren kiran na sirri.Wannan shi ne sirrin wahalar kira bisa tafarkin imamancin gaskiya. Saboda kira mai dauke da sako, mai zimmar kawar da dagutu da fir’aunanci da jabberanci da dagawa da zalunci a cikin al’umma tare da cewa tana riko da ma’aunan musulunci wajen ayyukanta dole ne ta yi dogaro da zabin (irada) talakawa da karfinsu da imaninsu da nunarsu. Sabanin kiraye-kirayen da suke dauke da taken yaki da masu dagawa alhali su ma suna aikata irin ayyukan dagutai da azzalumai, basu lura da dokokin kyawawan dabi’u da na halin zaman jama’a. Irin wadannan kiraye-kiraye basu fuskantar wahalhalun da kira mai dauke da sako, mai manufa, take fuskanta. Wannan shine sirrin rashin tabbatar manufofin harakar Imamanci cikin gaggawa, shi ne kuma sirrin samun nasara nan take na harakokin da suka yi hannun riga da harakar imamanci, kamar ta Banu Abbas.



back 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14 15 16 17 18 19 20 21 22 23 24 25 26 27 28 29 30 31 32 33 34 35 36 37 38 next