Gudummawar Mace



Da wannan mace ke samun wannan matsayi na shakalin ginin zamantakewa, take kuma da nauyin da ya hau kanta ta hanyar alakar kauna ga daidaiku da al'umma da dukkan jinsosin biyu namiji da mace.

2-Dokoki da tsare-tsare: Ana ta'arifin doka da cewa ita ce: "Wasu gungun ka'idoji da aka tsara don halayyar daidaiku a cikin al'umma, wadanda kuma hukuma ke tilasta mutane a kan mutuntasu ko da kuwa ta hanyar yin amfani da Rarfi ne a lokacin da haka ya zama dole. "[4]

Don haka dokar zamantakewa ita ce hanyar da ke tsara harkokin al'umma, take kuma hada daid'aikunta, kuma take fuskantar da su da sha'anoninsu, kamar yadda dokokin dabi'a (na halitta) ke tsara motsin rana da wata da sauran irinsu. In ba tare da doka ba ba, za a iya gina surar zamantakewa ko bunkasata ba.

Dokokin Musulunci kuwa, su ne dokokin da aka ciro daga AIKur'ani mai girma da Sunna mai tsarki don tsara al'ummar Musulmi daidai da tunani da manufofin Musulunci, don su suna magance matsaloli a kan asasin ilimi; don haka ne ma (dokokin) suka yi la'akari da dabi'ar rai da jiki ga kowane daya daga namiji da mace.

Bayan an gina su a kan kai'doji na ilimi, ana kasa dokokin Musulunci zuwa kashi uku kamar haka:­

a-Dokoki da hukunce-hukunce da suka kebanci mace. b-Dokoki da hukunce-hukunce da suka kebanci namiji. c-Dokoki da hukunce-hukunce gamammu da ke hawa kan namiji da mace baki daya, wadannan su ke da fadi a fagagen dokoki da hukunce-hukuncen Musulunci. Wannan nau'i na tsari mai la'akari da jinsi, yana kallafa wa mace, kamar yadda yake kallafa wa namiji, wanda kowannensu ke motsawa a fagage biyu, na farko a fagen da ya ke6anta da jinsinsa kuma da yanayinsa na jiki; na biyu kuma ya hado dukkan al'umma da duk gininshi da haduwarsa.

3-AI'adun Musulunci: AI'ummar Musulmi na da al'adunta wadanda ke matsayin wani tubali na asasi daga tubalan gininta wadanda suka kebanta da ita, wadanda kuma ya wajaba a kwadaitar a kansu a kuma tabbatar da su don kiyaye ka'idojinta.

4-Hidima da musayar amfanoni: Ta bayyana gare mu ta hanyar ayar nan mai girma:

"..kuma muka daukaka darajojin sashinsu a kan wani sashi don wani sashin ya riki wani mai yi mishi hidima..." Surar Zukhrufi, 43:32.

Cewa bukatar zuwa ga wasu shi ne sababin asasi na shigar mutum cikin taron mutane da hada ginin Zamantakewa; don su shiga aikin musayar amfanoni, kamar yadda rayayyun abubuwa da dabi'a ke musayar amfanoni tsakaninsu a fagensu na dabi'a da ya kebanta da su. Ta haka mutum zai sami biyan bukatarsa, kuma ya taimaka wajen cikar rayuwar dan Adam.



back 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14 15 16 17 18 19 20 21 22 23 24 25 26 27 28 29 30 31 32 33 34 35 36 37 38 next