Tambayoyi da Amsoshi



T90-muna fatan za a yi mana bayanin bambancin da ke tsakanin alwalar maza da ta mata. A : babu wani bambanci tsakanin mace da namiji wajan ayyukan alwala da kuma yanayin alwala .sai dai kawai mustahabbi ne ga maza yayin wanke damtsensu da su fara da wajensa , su kuma mata mustahabbi ne su fara da cikinsa.

TABA SUNAYEN ALLAH DA KUMA AYOYINSA

T91: Mene ne hukuncin taba lamiran da suke komawa ga zatin Allah Ta'ala kamar lamirin da ke cikin "Bismihi Ta'ala" (wato "hi" da ya zo a wannan lafazi.)?

A: Lamiri ba shi da hukuncin lafazin sunan Allah.

T92: A wasu lokuta akan rubuta (الله) da haka (...ا) kamar yayin rubuta (اية الله  ) sai a rubuta (...I اية) kana da kuma ( اله), to shin mene ne hukuncin taba wadannan kalmomi ba tare da alwala ba?

A: Wannan Alif (hamza) da kuma wadannan digo guda uku ba sa da hukuncin sunan Allah sabanin kalmar (اله)

T93: Mene ne hukuncin taba sunayen mutane kamar Abdullahi ko Habibullah.... ba tare da alwala ba?

A: Ba ya halatta ga mara alwala da ya taba sunan Allah ko da kuwa ya kasance wani bangare ne na hadadden suna (kamar Abdullah).

T94: Shin ya halatta ga mace mai haila ta sanya abin wuyan da aka rubuta sunan manzon Allah (saw) a jiki?

A: Sanya shi a wuya ba matsala, sai dai wajibi ne kada sunan ya tabajikinta.

T95: Shin haramcin taba rubutun al-kur'ani mai girma ba tare da tsarki ba ya kebanta ne kawai idan rubutun na cikin littafin al-kur'anin ne ko kuma ya hada da ko da yana jikin wani littafi ne daban, ko allo, ko katanga da dai sauransu ?



back 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14 15 16 17 18 19 20 21 22 23 24 25 26 27 28 29 30 31 32 33 next