Akidojin Imamiyya



 

15- Mu’ujizar Annabawa

Mun yi imani da cewa yayin da Ubangiji (S.W.T) yake sanya wa bayinsa mai shiryarwa ko manzo, to babu makawa ya sanar da shi gare su ya kuma nuna musu shi a ayyane. Wannan kuwa ya takaita ne a kan sanya musu wani dalili da kuma kafa musu hujja a sakon domin cika tausasawarsa da kuma kammala rahamarsa. Kuma wannan dalilin dole ya kasance ya zo daga mahaliccin halittu mai juya al’amuran samammu[23], wato ya zama abin da ya gagari kudurar dan Adam, sai ya sanya shi a hannun shi Manzon mai shiryarwa domin a san shi da shi, kuma mai shiryarwa zuwa gare shi, wannan dalili shi ake kira mu’ujiza saboda kasancewarsa ya gagari dan Adam ya gudanar da irinsa, ko kuma ya zo da misalinsa.

Kamar yadda babu makawa ga Annabi ya zo da mu’ujiza ya bayyana ta ga mutane domin ya kafa musu hujja, haka nan babu makawa wannan mu’ujizar ya bayyanar da ita ta yadda za ta gagari malamai da kuma kwararrun zamaninsa ballantana sauran mutane, tare kuma da danganta wannan mu’ujizar da da’awar Annabci daga shi mai mu’ujizar saboda ta kasance dalili a kan da’awarsa.

Idan irin wadancan kwararru suka gaza zuwa da irinta sai a sani cewa ta fi karfin ikon dan Adam, kuma ta keta al’ada, daga nan sai a san cewa ma’abocinta yana sama da kudurar dan Adam, kuma yana da alaka da mai juya al’amuran samammu. Idan wannan ya tabbata ga mutum -bayyanar mu’ujiza wadda ta saba wa al’ada- ya kuma yi da’awar Annabci da sako, to sai ya zamanto abin gaskatawar mutane ga kiran da yake yi tare da yin imani da sakon nasa da bin maganarsa da umarninsa, sai wanda zai gaskata shi ya yi imani da manzancinsa da kaskan da kai ga umarninsa, wanda zai yi imani da shi ya yi, wanda kuma zai kafirce masa ya kafirce.

Wannan shi ne abin da ya sa muka ga cewa mu’ujizar kowane Annabi ta dace da abin da ya shahara a zamaninsa na ilimi da fasaha, mu’ujizar Annabi Musa ita ce sanda wanda take hadiye sihiri da abin da suke yin baduhunsa saboda kacancewar sihiri a zamaninsa shi ne fannin fasaha da yake mashahuri, yayin da sandan ya zo sai dukan abin da suke aikatawa ya baci, suka san cewa wannan abu ya fi karfinsu, kuma yana saman fannin fasaharsu, kuma dan Adam ya gajiya ya kawo shi, kuma kwarewa da ilimi sun gajiya a gabansa[24].

Hakanan mu’ujizar Annabi Isa (A.S) ita ce warkar da makafi da masu baras, da raya matattu, saboda shi ya zo ne a lokacin da likitanci ne yake ya yadu a tsakanin mutane, kuma akwai malamai likitoci da suke da kwarewa mai girma, sai iliminsu ya kasa gogayya da abin da Isa (A.S) ya zo da shi[25].

Mu’ujizar Annabinmu madawwamiya ita ce Kur’ani mai girma mai gajiyarwa -ga waninsa na daga fasahohi- da balagarsa da fasaharsa a lokacin da balagar magana ta kasance ita ce fanni sananne, ma’abota ilimin balaga da azancin magana su ne kan gaba a tsakanin mutane da kyawun bayaninsu da daukakar fasaharsu, sai Kur’ani ya zo musu kamar tsawa, ya dimautar da su, ya fahimtar da su cewa su ba zasu iya fito na fito da shi ba. Don haka suka sallama masa rinjayayyu bayan sun gaza gasa da shi, suka ma gaza isa ga kurar da ya tile su da ita ya wuce ya barsu[26].

Ya kuma kalubalance su da su kawo sura goma suka kasa, yayin da muka ga sun gajiya sai muka ga sun koma fada da shi da takobi maimakon harshe, sai muka san cewa lallai Kur’ani wani abu ne na mu’jiza da ya zo daga Muhammad dan Abdullahi hade da da’awar manzanci, sai muka san cewa ya zo ne da gaskiya kuma ya gasgata shi.

 



back 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14 15 16 17 18 19 20 21 22 23 24 25 26 27 28 29 30 31 32 33 34 35 36 37 38 39 40 41 42 43 44 45 46 47 48 49 50 51 52 53 54 55 56 57 58 59 60 61 62 63 64 65 66 67 68 69 70 71 72 73 74 75 76 77 78 79 80 81 82 83 84 85 86 87 88 89 90 91 92 93 94 95 96 97 98 99 100 101 102 103 104 105 106 107 108 109 110 111 112 113 114 115 116 117 118 119 120 121 122 123 124 125 126 127 128 129 130 131 132 133 next