Akidojin Imamiyya



AKIDOJIN IMAMMIYA

Wallafar: Muhammad Ridha Muzaffar

Fassarar: Hafiz Muhammad Sa'id

Imam Mahadi (A.S) Allah ya gaggauta bayyanarsa:

“Kuma Kowane mutum daga cikinku ya yi aiki da abin da zai kusanta da shi zuwa ga soyayyarmu, kuma ya nisanci abin da zai kusantar da shi ga kinmu da fushinmu”

Biharul Anwar: 53, shafi 126.

Gabatarwa

Da mun so karbar izinin bugu ne na littafin da muka fassara na Shahid Sadar mai taken “Dan sako da Sako da Mai sako” wanda yake bincike game da hanyoyin tabbatar da samuwar Allah ta hanyar Mantik istikra’i[1], amma sai muka ga amfaninsa ga mutane duk da yana da yawa amma kadan ne zasu amfana daga gareshi, Domin kuwa duk da ya kasance an fassara shi da harshen Hausa ne amma akwai kalmomi da yawa da sai wanda ya san ilimin Mantik ko Falsafa zai fahimta. Kuma ga wahalar mayar da isdilahohin[2] ilimin daga Larabci zuwa Hausa, al’amarin da in Allah ya yarda a nan gaba zai zama malamai sun fara shi, musamman da yake mafi yawancin kalmomin ilimomi daban-daban ba a yi wani kokarin samar da su a Hausa ba, wanda irin wannan ya taso ne daga sakaci da halin ko-in-kula na Farfesa wane da Dakta wane da Alhaji wane, sa’annan kowanne ya zauna babu kokarin ganin ci gabantar da al’ummar gaba ta fuskacin tunani da ilimi ba, hada da cewa shi Alhaji wane ba zai iya kashe wa Farfesa wane da Dakta wane kudi domin su kawo canjin ilimi cikin al’umma ba[3].

 Tunanin wahalar fahimtar Littafin “Dan sako da Sako da Mai sako” ga masu karatu shi ne ya sanya muka yi tunanin canza littafin da wanda yake da sauki game da Ilimin kalam (Akida) mai suna Akidojin imamiyya na Malam Rida Muzaffar, amma bayan mun fara ba mu yi nisa ba sai aka yi mana ishara da cewa an riga an fassara shi, amma bayan nazari kadan da neman shawarwarin wasu daga abokai suka yi nuni da cewa idan dai zai fi sauki akan wanda aka fassara to yana da kyau, hada da wasu abubuwa da suka hada da hakkin mallaka, da wasu gyare-gyare, sai muka dauki wannan shawarar domin neman lada wajan Ubangiji da kuma fatan ya zama ya fi sauki ga mai nazari, musamman da ya zama abin nufi shi ne amfanar da al’umma da ilimin sanin Allah (S.W.T) da siffofinsa da ayyukansa ta hanyar kalmomi masu sauki da zasu yi saukin fahimta. Da fatan Allah ya sanya shi mai amfani ga al’umma gaba daya.

Littattafan da muka rubuta zuwa yanzu, su ne: “Tarbiyyar Yara A Musulunci” da “Zabar Mace Ko Namijin Aure” da “Raddin Sukan Auren Mace Fiye Da Daya” da “Mace A Tarihin Al’adu Daban-Daban” da “Boyayyar Taska Mai Rabo Kan Gano Ki” da “Addinai Daga Bakin Fiyayyen Halitta” da “Tsari Da Kayyade Iyali” da “Kurkuku Bincike Da Hukunci” da kuma “Hakkoki A Musulunci”.



1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14 15 16 17 18 19 20 21 22 23 24 25 26 27 28 29 30 31 32 33 34 35 36 37 38 39 40 41 42 43 44 45 46 47 48 49 50 51 52 53 54 55 56 57 58 59 60 61 62 63 64 65 66 67 68 69 70 71 72 73 74 75 76 77 78 79 80 81 82 83 84 85 86 87 88 89 90 91 92 93 94 95 96 97 98 99 100 101 102 103 104 105 106 107 108 109 110 111 112 113 114 115 116 117 118 119 120 121 122 123 124 125 126 127 128 129 130 131 132 133 next