Asasin Kiyayya



Kiyayya saboda Allah tana nufin cewa; wanda yake kin ba shi da wata gaba ta gashin kansa tare da wanda yake ki, kuma babu wata maslahar kansa a gabar da yake da shi, kawai yana kin sa ne yana gaba da shi domin Allah, ba don kansa ba, don haka a irin wannan akwai bambanci mai nisa tsakanin kiyayya don Allah da kuma kiyayya domin kansa.

Kiyayya saboda kansa tana faruwa ne domin maslhar kansa ko ta jama’arsa wanda wannan shi ne asaslin dukkan fasadi da fitina, amma kiyayya saboda Allah tana kasancewa kamar soyayya ce saboda Allah wacce take mabubbugar dukkan alherai da albarkai da kuma gina mutum da al’umma. Muna iya cewa; hakika kiyayya saboda Allah tana nufin lamunin maslahar al’umma; domin kiyayyar dan’Adam ga mahallicinsa ba zai iya amfanar (mahaliccin)sa ba, domin shi mawadaci ne tsantsa, kuma mutum da al’ummarsa su ne wadanda suke girbar amfanin wannan soyayyar da kiyayyar saboda Allah.

Don haka ne bisa al’ada son wadanda ba sa tausaya wa al’umma a bisa zahiri yana da matukar hadari, kuma imam Ali (A.S) ya yi nun da wannan ma’ana da fadinsa: “Tausayin wanda ba ya tausayi yana hana rahama ne, kuma wanzar da wanda ba ya wanzarwa yana halakar da al’umma ne”[3]. Kuma babu makawa cewa; soyayyar al’umma tana wajabta kiyayya da irin wadannan mutane ne masu hadarin gaske, kuma da yanke hannayensu daga ta’adi da keta hurumin ‘yan’adamtaka.

A kan haka ne muke cewa; hikimar kiyayya saboda Allah tana kunshe ne cikin hikimar nan ta yakar dukkan miyagun abubuwan da suke iya hana samun habakar abubuwan alheri na al’umma, da kuma tsarkake al’umma daga dukkan wasu miyagun da suke hana kyawawa da madaukakan al’amura cikin al’umma, kuma wannan kokarin bai kasance mafi karancin muhimmanci ba fiye da kokarin ganin an gina al’umma a kan soyayya saboda Allah madaukaki, kai wannan shi ne wani bangare mai muhimmanci na wannan al’amarin ma.

Kiyayya Tana Da Asasi A Cikin Soyayya

Bayan abin da aka ambata a cikin hikimar kiyayya saboda Allah, hakika kiyayya tana da rassa a cikin soyayya, kuma so na hakika an hada shi ne har abada da kiyayya, idan mutum ya so abu to kai tsaye zai samu kiyayya da abin da yake kishiyantarsa, don haka ne ma ba zai yiwu ba mutum ya so wani so na hakika kuma ya kasance ba ya kin makiyinsa, kuma kin makiya yana daya daga mafi girman dalilai a kan gaskiyar son wanda yake da’awar soyayya.

Don gane da wannan mahanga ne; Littattafan addinin musulunci suka karfafa a kan (tsayuwa bisa) asasin nan na ki saboda Allah a matsayinsa na (abu ne mai nuni ga) tsantsar so saboda Allah.

 


[1] Alma’izul adadiyya: 420.

[2] Zukhurufi: 67.

[3] Gurarul hikam: 5430.

 



back 1 2