Addu’a Ibada ceTarbiyyantarwar Ahlul Baiti Ga Mabiyansu
Shimfida:
Ahlul Baiti (AS) sun sani tun tuni cewa hukumarsu ba za ta taba dawowa garesu a rayuwarsu ba, kuma su da shi’arsu zasu ci gaba da zama a karkashin shugabannin da ba su ba, wadanda suke ganin wajabcin kawar da su da dukkan wata hanyar takurawa da tsanantawa. Don haka a bisa dabi’a suka riki “Takiyyaâ€‌ Addini kuma dabi’a garesu, su da mabiyansu, matukar zata kare masu jininsu kuma ba zata munana wa wasu ko Addini ba, saboda su iya wanzuwa a cikin wannan rutsitsi mai ruruwar fitina mai ingizawa ga kiyayya da Ahlul Baiti (AS). Don haka ya zama tilas suka koma ga koya wa mabiyansu hukunce-hukuncen Shari’ar Musulunci, da kuma fuskantar da su fuskantarwa ta Addini ta gari, da kuma sanya su kan hanya ta tafarkin zamantakewa da jama’a mai amfani, domin su zama misalai na musulmi na gari masu adalci. Wannan dan littafi ba zai iya kawo dukkan bayanai game da tafarkin Ahlul Baiti (A.S) ba, akwai littattafan hadisai masu girma da suka dauki nauyin yada ilimin addini, sai dai ba laifi mu yi nuni da wasu da suke kama da babin akida cikin abin da ya shafi tarbiyyantarwarsu ga shi’arsu da tarbiyyar da zata kai su ga shiga cikin al’amuran zamantakewar al’umma mai amfani, suke kuma kusantar da su zuwa ga Allah madaukaki, suke kuma tsarkake zukatansu daga daudar zunubai da laifuffuka, kuma suke mayar da su adalai masu gaskiya. Kuma magana ta gabata game da takiyya da take daya daga tarbiyya mai amfani ta zamantakewarsu, kuma zamu ambaci sashen abin da ya shafe mu na wadannan ladubban a nan. Imaninmu Game Da Addu’a
Annbin Allah (S.A.W) Ya ce: “Addu’a makamin Mumini ce, kuma jigon Addini ce, kuma hasken sammai da kasa ceâ€‌. Shi ya sa ta zama daga siffofin shi’a da suka kebantu da su, hakika sun wallafa abin da ya kai gomomi na manya da kananan littattafai game da falalarta da ladubbanta, da kuma addu’o’in da aka rawaito daga Ahlul baiti (A.S). Kuma an rabuta abin da manzo da Ahlul Baiti (A.S) suke gurin cim masa na kwadaitarwa a kan yin addu’a a cikin wadannan littattafai. Har ma ya zo daga garesu cewa: “Addu’a ita ce mafifciyar ibadaâ€‌. Da kuma cewa: “Mafi soyuwar aiki a bayan kasa a gun Allah madaukaki ita ce addu’aâ€‌. Kuma ya zo cewa: “Addu’a tana mayar da kaddara da bala’iâ€‌. Da kuma cewa: “Addu’a waraka ce daga dukkan cutaâ€‌. Kuma ya zo game da Amirul Muminin Ali Dan Abi Talib (AS) cewa, ya kasance mutum ne ma’abocin addu’a -Mai yawan addu’a- hakan nan ya kamata shugaban masu Tauhidi kuma shugaban mabiya Ubangiji ya kasance. Kuma addu’o’insa sun zo kamar yadda hudubobinsa suke a matsayin alama daga almomin balagar magana da fasaharta kamar addu’ar Kumail Bn Ziyad wacce ta kunshi ilimin sanin Ubangiji da fuskantarwar Addini, da kuma abin da ya dace ya zamanto madaukakin tafarki ga musulmi na gari. Hakika addu’o’in da suka zo daga Annabi (S.A.W) da Ahlul Baiti (AS) su ne mafificin tsarin rayuwa ga musulmi -idan ya yi tunani a kansu- sukan cusa masa karfin imani, da karfin akida, da ruhin sadaukar da kai a tafarkin gaskiya, da sanin kansa, da dadin ganawa da Allah, da yankewa zuwa gareshi, kuma tana lakkana masa abin da ya wajaba a kan mutum ya san shi a addininsa, da kuma abin da yake kusantar da shi zuwa ga Allah Madaukaki, ya kuma nesata shi daga barna da son zuciya da bidi’a batacciya. A takaice dai wadannan addu’o’in sun kunshi sanin Addini ta fuskar kyawawan dabi’u da tsarkake zukata, ta wata fuskar kuma sun kunshi akidar Musulunci, kai ita ce ma mafi girman madogarar ra’ayoyin falsafa, da binciken ilimi dangane da sanin Ubangiji da kyawawan dabi’u. Idan da mutane sun iya kuma ba dukkansu ne masu iyawa ba, da sun shiriyu da shiriyar da wadannan addu’o’in suke kushe da ita a cikin abin da ta kunsa madaukaka, da ba zaka samu irin wannan fasadin da kasa take cike da shi ba, kuma da wadannan rayukan da sharri ya yi musu katutu sun yi shawagi a sammai domin jin gaskiya, sai dai yaya dan Adam zai saurari maganar salihai da masu kira zuwa ga gaskiya alhalin fadinsa madaukaki ya nuna hakikaninsu da fadinsa: “Hakika rai mai umarni da mummuna ceâ€‌. Surar Yusuf: 53. “Kuma mafi yawancin mutane ko da kayi kwadayi ba masu shiryuwa ba neâ€‌. Surar Yusuf: 103. Na’am abin da ya kawo kafuwa da damfaruwar munanan ayyuka ga mutum shi ne, rudin kansa, da jahiltar munanan ayyukansa, da yaudarar kansa cewa shi yana aikata aikinsa, sai ya yi zalunci ya ketare iyaka, ya yi karya, ya yi kage, ya bi sha’awarsa yadda ransa yake so, tare da haka yana yaudarar kansa da cewa shi bai yi komai ba sai abin da ya dace ya aikata, kuma ya runtse dagangan daga munin abin da ya aikata, ya kuma karanta kuskurensa a idanunsa. Wadannan addu’o’in daga hadisai da suke samun karfafa daga tushen wahayi, sun yi kokarin sanya mutum ya koyi zargin kansa da kadaita zuwa ga Allah (S.W.T), domin su cusa masa furuci da kuskurensa da kuma cewa shi mai aikata zunubi ne, wanda ya wajaba a kansa ya yanke zuwa ga ubangijinsa domin neman tuba da gafara. Kamar misalin fadin mai addu’a a cikin Addu’ar Kumail: “Ya Ubangijina! Ya Majibincina! Ashe zaka gudanar da hukunci a kaina a kan abin da na bi son raina a cikinsa, kuma ban kiyaye kawatarwar abokin gabata ba a cikinsa, don haka ya rude ni da abin da ya so, kuma hukuncinka ya taimake shi a kan haka, har na ketare wasu daga cikin dokokinka saboda abin da ya gudana gare ni na daga hakan, kuma na saba wa wasu daga umarce-umarcen ka.â€‌
|