Karfafa Ginin Al'umma



NA BIYU: MATAKIN KARFAFA GININ AL’UMMA

TafarkiNa Daban Wajen Karfafa Ginin Al’umma

Amma bisa mataki na daban, wato karfafa ginin al’umma, akwai wasu asasai da tsare-tsare na daban baya ga wadanda suka gabata, wadanda Musulunci da Ahlulbaiti (a.s) suka ba su muhimmanci na musamman:

Shirya Tarurruka

Na Farko: Tafarkin shirya tarurruka don tattaunawa kan lamurran addini da na duniya a matsayin mafi kyawun tsari da tafarkin gina al’umma saliha. Watakila wannan tafarki na daga cikin mafi kwawun tsarin da Ahlulbaiti (a.s) suka ba shi muhimmanci da jaddadawa ta musamman.

A wurare da dama sun sha bayyana cewar wadannan tarurruka suna da tasiri daban-daban a bangaren addini, ruhi da kyawawan dabi’u, kuma dalili na samun kusanci da Allah Madaukaki, kamar yadda hakan yana a matsayin raya al’amurransu, sauki ga rai, gafara ga zunubai, sannan kuma suna sonsu da kuma kwadacin kasantuwa cikin tarurrukan.

An ruwaito Abi Abdillah (a.s) yana cewa: “Ku yawaita ziyarar junanku saboda akwai raya zukatanku cikin hakan, da tunatar da hadisanmu, hadisanmu suna kulla (alaka) tsakaninku, idan kuka yi riko da su kun shiriya kun kuma tsira, idan kuwa kuka yi watsi da su to kun bata da kuma halaka. Don haka ku yi riko da su, ni kuma zan zamanto jagora zuwa ga tsirarku[1]”.

Maisar ya ce Abi Ja’afar (a.s) ya ce min: “Shin kuna kebancewa da kuma fadin abin da kuke so? Sai na ce masa: lalle muna kebantuwa, muna magana da kuma fadin abin da muke so. Sai ya ce: “Wallahi na so da a ce ina tare da ku a irin wadannan wajaje. Amma wallahi lalle ina son kamshinku da ruhinku, don ku kuna a kan addinin (tafarkin) Allah da addini Mala’ikunSa, ku taimake ni da tsantsaini da kokari[2]”.

Abi Abdillah (a.s) yana cewa: “Muminai uku zuwa sama ba za su taru waje guda ba face har sai Mala’iku kwatankwacinsu sun kasance tare da su, idan suka yi addu’ar alheri, za su amsa musu da cewa ‘amin’, idan kuwa suka nemi tsari daga wani sharri, za su roki Allah da Ya tafiyar da shi (sharrin) daga gare su, idan kuma suka roki wata bukata, za su kama kafa da Allah da neman Ya biya musu ita[3]”.

Daga Mu’utab bawan Abi Abdillah (a.s) yana cewa: Ya ji shi yana ce wa Dawud bn Sarhan: “Ya Dawud!, Ka isar da sakon gaisuwata ga mabiyana, sannan ina cewa: Allah Ya yi rahama ga bawan da ya hadu da wani mutum guda don ambaton al’amrinmu, hakika mala’ika shi ne zai kasance na ukunsu yana mai nema musu gafara. Wasu mutane biyu ba za su hadu don raya al’amarinmu ba, har sai Allah Madaukaki Ya yi alfahari da su ga Mala’ika, idan kuwa kuka taru kuka shagaltu da ambaton (al’amarinmu), to lalle akwai raya al’amarinmu cikin wannan taro da ambato naku. Mafi alherin mutane bayanmu shi ne wanda ke raya al’amarinmu da kuma kira zuwa ga ambatonmu[4]”.

Daga Khaithama daga Abi Abdillah (a.s) yana cewa: “Ina isar da sakon gaisuwata ga mabiyanmu, ina kuma yi musu wasicci da tsoron Allah Mai girma da kuma mai halinsu ya saba da fakirinsu, mai karfinsu kuwa da mai rauninsu, kuma rayayyensu ya halarci jana’izar mamacinsu, kuma su dinga haduwa da junansu a gidajensu, saboda cikin saduwa da junansu akwai raya al’amarinmu”, daga nan sai ya ce: “Allah Ya yi rahama ga bawan da ya raya al’amarinmu[5]”.

Daga Shu’aib al-Ukrikufi yana cewa: na ji Aba Abdillah (a.s) yana ce ma sahabbansa: “Ku ji tsoron Allah, ku kasance ‘yan’uwa masu kauna da son juna don Allah, masu ziyartar juna (sada zumunci) masu tausaya wa juna. Ku yawaita ziyara da haduwa da junanku, sannan ku yawaita ambaton al’amurranmu da raya su[6]”.

NasihaGa Musulmi:

Na Biyu: Umarni da yin nasiha wato nuna ikhlasi yayin mu’amala da sauran musulmi da yi musu nasiha wajen aiwatar da ayyuka, gabatar da nasiha da yarda da ita, kai har ma da gode wa wanda yayi ta idan har tana nuni da gazawa da raunin mutum.



1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14 next