Koyarwar Ahlul Baiti (A.S)Shimfida
Hakika Ahlul Baiti (A.S) sun yi aiki ga al’ummar musulmi a kan tafarki biyu manya a kuma cikin gewaye biyu masu shigar juna wadanda su ne: Na farko: Aiki a kan tafarki na gaba daya na al’umma kuma a cikin da’ira mai fadi na ita al’ummar. Yayin da suka kasance suna da alaka mai fadi da ita al’umma ba tare da ganin sun bambanta masu bin su na daga muminai masu imani da su (A.S) da kuma sauran mutane na daga ‘ya’yan al’umma, sai daidai gwargwadon kusanci na akida da ruhi da halayen zuciya da yake tabbatuwa cikin biyayya ta akida a siyasa da so da ji a zuciyarsa da lizimtar kyawawan ayyuka da bin umarninsu. Na biyu: Aiki a kan wani tsari na musamman a kuma cikin zababbu na musulmi da suka kasance suna da alaka da su (A.S) da matsayinsu, kuma suka yi imani da hikimar matsayinsu da gudummuwarsu ta musamman a nazarin musulunci wanda ya tsayu a kan jagorancin al’ummar musulmi da halifanci bayan manzo (S.A.W) da ake da nassi kanta daga Allah (S.W.T). abin la’akari da lura shi ne bangare na biyu wanda ya zama ita ce jama’a ta gari saliha da take da samuwarta da jama’arta madaukakiya da kuma alamominta na musamman, da kuma aka santa a cikin musulmi da shi’ar Ahlul Baiti (A.S) ita wannan jama’a bayyanarta da daduwarta da cigabanta bai cika ba, shi ya sa ma ba a tantanceta da bambanta ta daga sauran jama’a a cikin maganar farko da tasirantuwar jama’ar al’umma gaba daya da harkar Ahlul Baiti (A.S), wannan ma ya faru da kokari ne da kuma shiri daga imamai (A.S) domin samar da wannan jama’a. A takaitaccen bayani samuwar wannan jama’a bai tabbata ba tare da dalili ba, kuma sakamakon aikin imamai a tsarin al’umma na gaba daya, ta yadda ya fitar da wadannan zababbun mutane daga muminai, sai dai wannan ya kasance bayan haka bisa hadafi da manufa da kuma sakamakon tsari da imamai suka tsara suka kuma zartar domin gina jama’a ta gari da samar da ita. Wannan kuwa saboda Ahlul Baiti (A.S) sun fahimci cewa hadafin na gaba daya gama-gari wanda daga cikinsa akwai kariya ga samuwar musulunci, da kuma kare samuwar al’ummar musulmi ba zai yiwu ya tabbata ba da aiki kawai da gabatar da hidima ga al’umma a matsayinta na gaba daya, domin tabbatar wannan hadafi dukkansa ba ya yiwuwa ne ya dore sai idan an samar da sharuddan wayewa na dindindin, da kuma zuciya mai son ci gaba, da kuma jagororin shugabanci na al’ummma da zasu tsayu da wayarwa da cigaban wannan al’amari na imani, da kuma jagorancin al’umma mai dorewa har abada da zai tsaya da wayar da ita da ilmantarwa. Saboda haka muka samu Ahlul Baiti (A.S) suna fuskantar wannan tafarki mai motsi da aiki a fage na musamman tun farko. Hakika manzo (S.A.W) ya bayar da muhimmanci ga wannan maudu’i tun farkon rayuwarsa, da haka ne ya assasa shi’anci da goyon baya zuwa ga Ali (A.S) a matsayin madogar da za a bi a tsarin tunani da shugabanci a rayuwarsa, bai isu da wannan ba har sai da ya fuskantar da wasu zababbu daga sahabbansa ga irin wannan tarbiyya, sai suka zama iri na gari ga hakan[1], sannan sai ga shi shi ma imam Ali (A.S) yana tsayuwa da wannan aikin, yana mai gina jama’a ta gari a Madina munawwara, yana mai fadadawa ga jagorancinta bayan nan a cikin kufa a hannun Huzaifa Alyamani da Salmanil farisi, da Ammar dan Yasir, a labanon a hannun Abu Zarril Gifari, a yaman a tsawon zaman da imam Ali ya yi yana mai jagorantar sha’anonin wannan yanki, haka nan a Misra da Basara da wasunsu. Da sannu zai bayyana gareka dalla-dalla ta hanyar bijiro da bayanan aikin ginin wannan al’umma da kuma ayyukan da Ahlul Baiti (A.S) suka gabatar da su a wannan fage yayin gabatar maka da su a wannan littafi. Hadafofin Jama’a Ta Gari
Zai iya yiwuwa a takaita hadafofi na asali domin gina jama’a ta gari wadanda muka sani na rawar da imamai (A.S) gaba daya suka taka domin samar da ita, wacce ita ce asasin kafa hujja ga al’umma, da jagorancin musulunci, da kuma marja’anci na gaba daya na akida da addini ga musulmi, da kuma kariya ga musulunci da akidar musulunci, da kuma kare cigaban samuwar jagorancin musulmi ta hanyar kare hukunce-hukuncen musulunci, da kuma al’ummar musulmi, da kuma misalta jagaronci na gari, da sannu zaka san da yawa da ga wadannan hadafofi a bayanai da zasu zo dalla-dalla game da tarbiyyar jama’a ta gari, sai dai domin mu bayyana maka hakan zamu yi nuni a nan da wadannan bayanai. A-Gudummuwa Wajan Jagorancin Musulunci
(Jagorancin Hukumar Musulunci)
|