Kyawawan HalayeRawarDa Zababbu Na Gari Suka Taka A Lokacin Halifofi Uku
Hakika ya bayyana garemu cewa wadannan zababbu na gari suna da rawa mai girma da suka taka wajan zagorantar tunanin musulmi na al’umma wanda ya kasance yana kira zuwa ga halifancin imam Ali (A.S) tun lokacin halifa na biyu Umar dan KhaddAbu, wannan tunani ya takura matuka da ya kasance halifa bayan Umar shi ne imam Ali (A.S). Sai dai zAbun da halifa Umar ya yi ga halifan bayansa a bisa asasin tacewa na shura da kuma sanya ta ta kebanta da mutane shida, haka nan sanya zAbu a hannun Abudrrahman dan Aufi idan al’amari ya kebanta ya juya tsakanin mutum biyu, duk wannna ya kasance ne domin kokarin ganin an kawar da tunanin al’umma ta hanyar take-take da aka tsara masu zurfi. Tare da haka muka samu cewa wannan tunani mai karfi game da halifancin imam Ali (A.S) da al’umma take dauke da shi ya tilasta wa dan Aufi ya nema daga farko daga imam Ali (A.S) da ya karbi halifanci. Sai dai ya sanya masa sharadi na wannan bai’a tare da yana sane da cewa da ma imam Ali ba zai karbi sharadin ba, ya sanya wa imam Ali sharadin bin tafarkin shaihaini, hade da littafin Allah da sunnan Annabi[1] (S.A.W). Karfin wannan tunani ya bayyana a fili yayin da fitinar kashe halifa usman ta auku, yayin da jama’a suka kwararo gaba daya da kadaita bai’a ga imam Ali (A.S) wanda wannan wani abu ne da ya kebanta da shi (A.S) a kan sauran halifofi da suka rigaye shi ko kuma suka zo bayansa, ta yadda bai’ar Abubakar ta zama da daidaiku ‘yan kadan a sakifar bani sa’id, wanda musulmi suka yi sabani a kansa, wasu kuma daga manya shugabannin al’umma suka zama ba sa nan, kamar yadda haka nan bai’ar Umar ta kasance da wasiyya daga Abubakar, da kuma shurun musulmi, bayan Abubakar bai karbi rashin yardar da Dalha ya nuna ba, kuma bai’ar Usman ta kasance ta hanyar shura ta mutum shida da muka riga muka yi nuni zuwa gareta[2]. Amma halifofin da suka zo bayan imam Ali (A.S) su kuma sun kasance suna shugabanci da wasiyya da gado da karfin makami da rinjaye, ta yadda babi wani abu da ya wanzu game da ma’anar shura a tarihin rayuwar siyasar musulmi, kamar yadda aka sani a tarihi. RawarDa Zababbu Na Gari Suka Taka
ALokacin Imam Ali (A.S)
Haka nan wadannan jama’a ta gari ta taka rawar gani ta musamman a yake-yaken da imam Ali ya yi (A.S) tare da masu gaba da shi (A’isha, Dalha, da Zubair, da Umayyawa karkashin jagorancin mu’awiya), ta yadda asasin kyawawan dabi’u da kuma nagartattun dabi’u na musulunci suka zama su ne ma’aunai da imam Ali (A.S) ya dogara a kansu a wannan yake-yake da dauki-ba-dadi da sabanin abin da daya bangaren mai gaba da shi ya dauka na maslaha da amfanin duniya da ake tunanin samu, da kuma kawar duniya da ake gani. A wannan ma’aunin idan muka auna zamu ga cewa imam Ali ba zai yiwu ya ci gaba da wannan yaki ba ko kuma ya samu nasara ba, ba don samun wadannan jama’a ta gari ba da ya riga ya gina ta a cikin al’umma. MisalinWadannan Gwarazan Mazaje
Saboda haka ne muka samu a wannan fage akwai mazaje da suke na musamman kamar Malik Ashtar da Hashim Mirkal da Muhammad dan Abubakar da Kais dan Sa’ad dan Ubbada da Hijr dan Udayy da Sa’asa’a dan Sauhan da Dan’uwansa Zai, da Uwaisul Karni, da Sulaiman da Surad al-khuza’i, da Abul Asawad Addu’ali, da Abdullahi dan Dalha, da Abdullahi dan Ja’afar da Khabbab dan Arat, da dansa Abdullahi, da Udayy dan Hatim Atta’i, da Akil dan Abu dalib, da Amur dan Alhamka Al-khuza’i, da Kumbur bawan imam Ali (A.S) da Muhammad dan Abuhuzaifa, da Zusshahadatain Huzaima dan Sabit Al-ansari, da Al-asbag dan Nabata, da Maisam Attammar, da Kumail dan Ziyad, da Alharis Alhamdani, da Rashid Alhijiri, Abdullahi dan Abbas, da sauransu, balle sauran da suke na gaba na sahabbai kamar: Ammar dan Yasir, da Ibn Taihan, da Usman dan Hanif, da Dan’uwansa Sahl, da JAbur dan Abdullahi da dansa Abdullahi dan JAbur Al’ansari da sauransu. Wadannan imam Ali (A.S) ya kasance yana bakin ciki a kan rashinsu wani lokaci yana kuka garesu yana kuma jin akwai wani gibi mai girma da suka bari a harkar musulunci, haka nan ya kasance yana kebewa da su yana ganawa da su wani lokaci. Wannan lokaci haka ya ci gaba da samuwa ta irin wadannan zababbu har zuwa lokacin imam Husain (A.S) yayin da sadaukarwarsu ta zama kokari na karshe a bayyane na bayar da gudummuwa domin samar da jagoranci na musulunci na gari[3]. B-Kiyaye Samuwar Al’ummar Musulmi
Hakan na kiyaye wa ga samuwar al’ummar musulmi ya zama shi ne hadafi na biyu na gina wannan tarayya ta jama’a ta gari a nazarin imamai (A.S). Hakika wannan jama’a ta gari ta ta ka babbar rawa wajan kare samuwar al’umma musulma a lokacin rayuwar imamai (A.S) ko kuma bayan gaiba babba ta imam mahadi (A.S); wannan kuma ya kasance ne domin shi gina jama’a saliha ba domin a yawaita yawan mabiya mataimaka ba ne ko ganin an yawaita yawan daidaikun mutane na gari da neman taimkonsu a aiki na siyasa wanda wadannan imamai suke yi, kawai al’amarin shi ne akwai wasu hadafofi mafi zurfi da suke damfare da wadancan hadafofi na gaba daya da imamai (A.S) suke da su a kan dukkan kowace matsaya bai daya ta hanyar aiki tare, da su wadannan zababbun mutane suke aiwatarwa ta hanyar samuwarsu da kuma damfaruwar su da al’umma gaba daya a matsayin jama’a ko daidaiku, wanda kiyaye samuwar al’umma musulma yana daga ciki. Kuma zai iya yiwuwa mu yi la’akar da wadannan bayanai muhimmai masu zuwa: 1-Kariya Ga Al’ummar Musulmi
Tsayuwar wadannan na gari da kiyaye karfin musulmi da kuma hadin kansu ta hanyar kariya gareshi a gaban makiya na waje da na ciki: hakika Shi’a sun kasance suna da matsayi babba a fagen yakar makiya na waje da duniyar musulunci ta fuskanta a marhalar karshe ta zamanin abbasawa a yakin salib ta hanyar daular hamdaniyya a kasashen Sham da Siriya ko kuma Adarisa a arwacin Afrika, ko kuma yakar magol a gabascin kasashen musulmi da kuma yanke harinsu na gaba da kuma mayar da su musulmi bayan haka, haka nan kokarin Shi’a wajan kashe motsin nan na ‘yan tawaye Kafirai da masu bautar gumaka a yankin Tabris da Turk da Dailam a yankin Kogin Kazwin da kasashen abin da ya ke bayan Koramu da sauransu.
|