Juyayin Zahra



Me ya sanya yayin da aka kai hari gidan Ahlul-baiti (a.s) sayyida Zahra (a.s) ta tafi bayan kofa? Me ya sa Imam Ali (a.s) bai bude kofa ba.

Amma amsar farko tukun dole ne mu san matsayin sayyida Zahra (a.s) tukun kafin bayar da amsa kan hakan:

Tsarki da darajar sayyida Zahra (a.s) a cikin mutane ya kasance kamar na annabin rahama (s.a.w) ne a cikin mutane, kuma annabin rahama (s.a.w) (ta hanyoyi daban-daban masu yawan gaske) ya yi bayanin matsayin wannan mata mai daraja ga mutane, ta yadda hatta da mutumi irin tsenanne Yazidu wanda yake makashin 'ya'yan ta sai da ya ambace ta da tsarki da daraja. Kuma a yau duniyar musulmi baki daya ba zaka samu wani musulmi ba wanda zai jahilci matsayi da darajarta, tare da cewa marubuta a tsawon tarihin shekaru masu yawa a galiban lokuta ba su da wani burin rubuta ko yada falalar Ahlul-baiti (a.s).

A takaice muna iya cewa, alkaluma da harsuna sun gajiya wurin bayanin girma da matsayin 'yar annabin Musulunci sayyida Zahra (a.s).

To da wannan matsayin nata mai daraja da daukaka tabbas babu wani musulmi da yake tunanin cewa wani daga cikin musulmi zai iya yin rashin kunyar keta huruminta ta hanyar yi mata mafi karancin abin da yake nuni da wulakanci gare ta, don haka sayyida ta zo bayan kofa don ta tabbatar da:

Matsayinta da kimarta da dalilinta mai karfi ko zasu iya nesantar da su daga gidan.

Don ta nuna kariya ga shi kansa Imam Ali (a.s) don su san cewa Ali yana da irin wannan matsayi da girma da tsarkakar da mutum kamar sayyida Zahra (a.s) zata iya ba shi kariya da dukkan rayuwarta.

A bisa gaskiya wannan shi ne cika hujja kan wadannan mutanen, idan ma Imam Ali (a.s) ne ya kasance a bayan kofa to wadannan mutanen zasu fi samun jur'ar kai hari gida da karfin tsiya, da neman kona shi, da ma kamashi ko gamawa da shi, sai mas'alar ta kare. Kuma za su iya shelanta cewa 'yar annabi (s.a.w) ma ba tare da shi take ba, kuma da tana tare da shi da mun kyale shi.
Amma domin ta yanke musu hujja sai ta halarci bayan kofa domin dora musu hujja gun Allah (s.w.t) da manzosa (s.a.w) da kuma gun tarihin musulmi ta yadda ba ta ba su kofar samun wani uzuri ba, sai ta tashi da kanta ta dora musu hujjar Allah a kansu, kuma ta nuna wa duniya mugunta da keta da suke cikin zukatan makiyansu da har abada tarihi ya dawwana su ga dukkan duniya.