Ranakun Waliyyai



Amsar wannan a fili yake, domin kuwa kowa ya san cewa wannan yana daya daga cikin girmama Manzo da nuna soyayya a gare shi, sannan yana taimaka wa wajen daga sunan Manzo (s.a.w), don haka shin zai yiwu a haramta wadannan bukukuwa?

Dalilan Masu Haramta Bukin Ranar Haihuwar Manzo

Masu sabani a kan yin bukin ranar haihuwar bayin Allah na kwarai, suna labewa da wasu dubaru guda biyu domin ba ma zamu kira su da dalilai ba domin kuwa sam ba dalilai ba ne, abubuwan da suke kawowa kuwa guda biyu su ne kamar haka:

1-Bukin ranar haihuwa ba bai zo ba a cikn addini!

Bukin ranar haihuwar Manzo bai zo ba a cikin Kur’ani da Sunna, don haka wannan buki bidi’a ne!

Amsar wannan kuwa a fili take, tare da kula da bahsin da muka yi a baya dangane da “bidi’a”, domin kuwa bidi’a ita ce yin wani abu a cikin addini wanda bai zo ba daga Kur’ani ko kuma ba shi da asali daga Kur’ani ko Sunna, alhalin cewa nuna soyayya ga manzon Allah da girmama shi yana da tushe daga Kur’ani.

Amma a cikin ruwayoyin musulunci dangane da musamman maulidin Manzo ruwaya ba ta zo ba a kan haka, sannan babu wani musulmi da yake da’awar cewa akwai wani dalili wanda yake magana musamman a kan bukin ranar haihuwar Manzo. Sai dai musulmai suna cewa ne Allah madaukaki ya umurce su da su girmama Manzo a duk tsawon shekara a ko’ina ne, wanda daya daga cikin wadannan wurare shi ne bukin ranar haihuwar Manzo, wato yana daga cikin aikata wannan umarni na Allah madaukaki.

Daga karshe yana da kayau mu yi nuni da wannan abu daga Kur’ani mai girma inda yake maganar cewa: Annabi Isa (a.s) ya nema wa sahabbansa abinci daga sama, sakamakon haka ne sai sahabbansa suka ce, zamu rika yin bukin ranar da wannan abinci ya sauka daga sama muka cika cukkunanmu da shi ga abin da Kur’ani yake cewa a kan haka:

“Ya Ubangiji ka saukar mana da abinci daga sama, ta yadda zai zama idi gare mu ga kuma na farko da karshemmu, sannan aya ce daga gare ka, ka azurta mu, kuma kai ne fiyayyen mai azirtawa”.[7]

Babu shakka idan har ranar da a ka saukar da abinci daga sama, wanda yake wata ni’ima mai wucewa, ya cancanci a yi bukin shekara saboda shi, me zai hana ayi bukin ranar haihuwar Manzo da murna a kowace shekara kasantuwar wata ni’ima ce daga Allah kuma madawwamiya wacce ya yi ga dukkan ‘yan Adam?

2- Girmama ranar haihuwa wani nau’i ne na bauta

Abin da ya fi komai abin mamaki a nan shi ne wai yin rin wadannan bukukuwa na ranar haihuwar Manzo wai sun dauke shi a matsayin bauta ga shi Manzo (s.a.w) a kan haka ne suke cewa: Bukukuwan da suka cika garuruwan musulmai da sunan waliyyai, nau’i ne na bautarsu da girmama su.[8]

Kuskurensu a nan shi ne duk wani nau’i na girmamawa sun dauke shi a matsayin bauta, alhalin cewa bauta bayan girmamawa tana bukatar wani abu daban kafin ta zama bauta, wannan kuwa shi ne mutum ya yi imani da cewa wannan abin da yake girmamawa Allah ne kuma ya cancanci a bauta masa. Amma idan ya zamana kawai girmamawa ce zai mai da shi bauta, to tabbas ba za a samu wani mai kadaita Allah ba a duniya!

Hafiz Muhammad Sa'id - hfazah@yahoo.com – www.hikima.org

Haidar Center for Islamic Propagation (HAIDARCIP)

Facebook: Haidar Center - December, 2012



 



back 1 2 3