Ranakun Waliyyai



Girmama Ranakun Haihuwar Waliyyan Allah

 

Mawallafi: Ayatullahi Ja’afar Subhani

Mai Fassara: Yunus Muhammad Sani

Gyara da Tsarawa: Hafiz Muhammad Sa'id

Tarihi yana nuna cewa tun lokaci mai tsawo musulmai sun kasance duk shekara suna bukin ranar haihuwar Manzo (s.a.w) ta yadda suke ambatar kalmomin yabo ga Manzo a wurin wannan buki. Babu tabbas a kan wane lokaci ne a ka fara wannan buki, amma dai wannan bukin an dauki daruruwan shekaru ana yinsa kuma ya yadu a duk garuruwan musulmai.

Ahmad Bn Muhammad wanda aka fi sani da Kusdalani, (ya rasu a shekara ta 923) Dangane da bukukuwan da mashahuran malaman karni na tara suk kasance suna yi, yana ruwaito cewa: Musulmai sun kasance a kowane lokaci suna yi bukukuwan ranar haihuwar Manzo (s.a.w) suna ciyarwa a wannan rana, sannan suna raba sadaka a dararen wannan ranaku, suna bayyana farin cikinsu a wannan rana, sannan suna ninka kyautatawa a wannan rana, kuma suna yin wakokin yabon Manzo a wannan rana. Sannan albarkar Manzo tana bayyana a kowace shekara, rahamar Allah ta tabbata ga wadanda suka yi bukin daren ranar haihuwar Manzo (s.a.w) sannan ya kara ciwo ga zuciyar makiyansa masu cutar zuci.[1]

Hasan Bn Muhammad Bn Hasan wanda aka fi sani da Dayyar Bukari (ya rasu shekara ta 960) kuma ya kasance daya daga cikin alkalan Makka, a cikin littafinsa na tarihi yana rubuta cewa: Musulmai sun kasance a kowane lokaci suna bukin ranar haihuwar Manzo, suna ciyarwa a wannan rana kuma suna bayar da sadaka a dararen wannan rana, kuma suna bayyanar da farin cikinsu a wannan rana, sannan suna tabbatuwa wajen kyautata wa mabukata, suna karanta tarihin Manzo a wannan rana, sannan karamar Manzo ta kasance tana bayyana a kowane lokaci.[2]

Wannan nassi guda biyu na tarihi wanda dukkansu daga karni na goma suke suna, yana nuna cewa bukin ranar haihuwar manyan bayin Allah wani abu ne wanda yake da tsawon tarihi a tsakanin musulmai, ta yadda manyan masana da malaman musullunci sun kasance suna yin wannan buki na ranar haihuwar Manzo (s.a.w) sannan yin wannan buki na ranar haihuwar Manzo ba ya nuna wani abu sai nuna kauna da soyayya ga Manzo (s.a.w) Dukkammu mun san cewa daya daga cikin ginshikan musulunci shi ne nuna soyayya ga Manzo Allah kamar yadda Kur’ani yake cewa: “Idan har ya kasance iyayenku da ‘ya’yanku da danginku da matayenku da kabilarku, da dukiyarku wacce kuke tara ta, da kasuwancin da kuke jin tsoron faduwa a cikinsa, da gidajen da kuke kauna, sun fi soyuwa gareku a kan Allah da manzonsa, da yin jihadi a tafarkin Allah, sai ku saurara, har sai al’amarin Allah ya zo muku, Kuma lallai Allah ba ya shiryar da mutane fasikai”[3].

Soyayya da kaunar Manzo wani abu ne wanda Kur’ani ya yi umarni da shi kuma hadisai sun zo a kan karfafa hakan, Manzo (s.a.w) yana cewa: “Ina rantsuwa da wanda rayuwata take a hannunsa, dayanku bai yi imani ba har sai na fi soyuwa gare shi a kan iyayensa da ‘ya’yansa”[4].



1 2 3 next