Kamun kafa Da Annabawa Da Waliyan Allah 2



A nan akwai abin tambaya: shin sakamakon tafiyar Manzo zuwa ga rahamar Ubangiji wannan kofar gafarar da jin kai shi kenan ta kulle, ta yadda babu wani musulmi da zai je wajen Manzo ya roke shi da ya nema masa gafara a wajen Allah, ko kuwa wannan kofar albarka tananan bude kamar lokacin da yana raye? Wato musulmi har yanzu idan suka je haraminsa suna iya neman addu’arsa, ta yadda wannan ayar da muka ambata; “Da wadanda suka zalunci kansu sun zo wajenka suka neme ka da nema musu gafarar..”. tana amfani a dukkan lokuta guda biyu, wato zamanin raywarsa da kuma bayan wafatinsa?

A wajen bayar da wannan masa dole ne a ce: Musulmi daga sahabbai da tabi’ai har zuwa yanzu sun kasance a aikace suna daukar wannan kofa a bude take, sannan musulmai a lokacin da suka ziyarci raudhar Manzo bayan yi wa manzon tsira sallama sukan karanta wannan ayar da muka ambata, tare da neman gafara daga Allah kuma suna rokon Manzo da ya nema musu gafara a wajen Allah madaukaki, saboda haka duk lokacin da mutum ya je ziyarar Manzo zai ga wannan al’amari daga al’ummar musulmi.

Bayan abin da tarihi yake nunawa ta hanyar ayyukan al’ummar musulmi danagane da neman addu’ar Manzo, addu’ar ziyarar Manzo ma wacce sunna da Shi’a suka ruwaito wannan addu’a tana tabbatar da wannan magana ta neman addu’ar Manzo. Domin jan hankalin masu karatu kuma suka kara natsuwa da abin da muke magana a kai, zamu kawo wassu daga cikin maganganunsu, ta yadda zai bayyanar mana yadda manyan malamai tun tsawon zamani suke neman kamun kafa da Manzo wajen yi musu addu’a:

 

1-Zakariya Muhyiddin Nawawi (631-676) Yana rubuta cewa: Mai ziyara yakan fuskanci Manzo ya yi kamun kafa da Manzo a kan abin da yake bukata kuma ta hanyarsa ya nemi ceto daga Allah, yana daga abu mafi kyau kasantuwar Mawardi, Alkali Abu Tayyib da wasu daga cikin manyan malamai suka ruwaito daga Utba tare da yabo suna cewa:

Utba yana cewa: Na kasance a wajen Manzo (s.a.w) wani mutum daga daji ya zo wajen Manzo ya ce “Assalamu alaika ya rasulullah, na ji Allah yana cewa: “Da wadanda suka zalunci kansu sun zo wajenka suka nemi gafara, kuma Manzo ya nema musu gafara, da sun samu Allah yana mai karbar tuba kuma mai jin kai”Lallai na zo wajenka ina mai neman gafara daga zunubaina sannan mai neman ceto a wajen Allah tare da kamun kafa da kai”. [14]

Kada mu yi tunanin cewa Nawawi ne kawai da malamansa suka tafi a kan ingancin kamun kafa da neman ceto daga Manzo. Malaman fikhu da na hadisi da dama sun kawo wannan a cikin littafansu na ziyara.

2-Kuddama Hambali (ya rasu shekara ta 620) a cikin ladubban ziyarar kabarin Manzo inda yake kawo maganar cewa”Mustahabbi ne ziyarar Manzo” Yaruwaito daga Abu Huraira yana cewa Manzo (s.a.w) ya ce: Duk wanda ya yi mini sallama, zan amsa masa sallamarsa. Sannan sai ya ruwaito daga Utba abin da muka ambata a baya kadan cikin hadisin Nawawi. Ya ce manufarsa wajen kawo wannan hadisi shi ne, don ya nuna cewa ana gabatar da ziyarar Manzo kamar haka:

3-Samhudi a cikin littafin “Mustau’ab” wanda Muhammad Bn Abdullah Samiri Hambali ya rubuta, yana ruwaito yadda ake ziyarar Manzo kamar haka:

Assalamu Alaika ya Rasulallah, assalamu alaika ya Nabiyyallah! Ya Allah kai ne ka fada a cikin littafinka ga annabinka cewa: “Da wadanda suka zalunci kawunansu…Ya Allah ga ni na zo wajen manzonka (s.a.w) ina mai neman gafara, ya Allah ina rokonka a kan ka wajabta mini rahamarka, kamar yadda ka wajabta ga wanda ya zo wajensa yayin da yake a raye, ya Allah ina ina kamun kafa da annabinka zuwa gare ka”. [15]



back 1 2 3 4 5 6 7 8 next