Rayuwa Bayan Mutuwa 2



“Amincin Allah ya tabbata a gareku ya gidan muminai, kun kasance kun rigaye mu, amma muma munanan zamu riske ku, kuma muna yi muku murna a kan ni’imar da kuke a cikinta”. [7]

2-Lakantawa mamaci kalmomi da ake yi yana daga cikin abubuwan da aka sallama a kansu a cikin fikihun musulunci. Sannan wannan yana nuna wani nau’in rayuwa da mamaci yake a cikinta, Mai lakanta wa mamaci yakan yi amfani da sunansa da siffofinsa yana kiransa da murya sama, yayin da yake cewa, yayin da mala’ikun mutuwa suka zo maka daga Allah, sannan suka tambaye ka dangane da Ubangiji da addini da annabinka da imamai, sai ka ce musu: “Na yarda da Allah a matsayin ubangijina, sannan na yarda da musulunci a matsayin addinina, kuma na yarda da Muhammad (s.a.w) a matsayin annabina, kuma na yarda da Ali (a.s) a matsayin Imamina.

Dukkan wannan yana nuni ne da cewa mutuwa ba wani abu ba ne sai kawai fita daga wannan duniyar da shiga wata sabuwar duniya, ta yadda mamaci a waccan duniyar yana ji yana gani kamar yadda yake a wannan duniyar, harma yakan yi magana da magadansa.

A nan kawai zamu wadatu ne da fassarar lakantawar da AhlusSunna suka kawo a cikin littafansu kamar haka:

Marubucin (al-fikhu ala mazahibul arba’a) yana rubuta cewa; mustahabbi ne bayan an rufe mutum kuma an baje kasar kabarinsa a lakanta masa wadannan kalmomin da zasu zo a kasa, mai lakanta wadannan kalmomi dole ya ambaci sunan mamaci da sunan mahaifiyarsa, idan kuwa bai san sunan mahaifiyarsa ba sai ya ambaci sunan ‘Hauwa’sannan sai ya kira shi ya ce: ka tuna da alkawarin da ka bar duniya da shi, wannan kuwa shi ne shedawa da cewa Allah shi kadai yake ba shi da abokin tarayya, sannan da shedawa da manzancin Manzo Muhammad (s.a.w) Sannan ka sheda da cewa aljanna da azabar lahira gaskiya ne, sannan ka sheda da cewa kiyama zata tsaya, sannan Allah madaukaki zai tayar da kowa, kuma ka yi imani da Allah da gaskiyar addinin musulunci, sannan ka amince da Manzo Muhammad da Kur’ani mai girma, sannan ka yarda da alkiblar ka’aba, da imani da ‘yan’uwantakar sauran muminai. [8]

Sannan Gazali a cikin Ihya’ul ulum yana cewa: mustahabbi ne a yi wa mutum talkini yayin da ya rasu. Sannan sai ya ruwaito wannan hadisi kamar haka:

“Sa’id Bn Abdullah yana cewa, a lokacin da Abu Imam Bahili zai rasu na kasance a bisa shinfidarsa, sai ya yi mini wasiyya da cewa, kamar yadda Manzo ya yi umarni, in yi masa “talkini” yayin da ya rasu. Manzo ya ba da umarni cewa duk lokacin da kuka gama rufe wani a cikin kabari wani ya tsaya a saitin kansa ya kira sunan shi da na mahaifiyarsa, domin kuwa yana ji amma ba shi iya mai da amsa. Sannan ku mai -mai ta wannan aiki har sau uku, ku ce masa: “ka ambaci abin da ka fita duniya tare da shi, kace ka shaida babu wani abin bauta da gaskiya sai Allah, kuma Manzo Muhammad ma’aikinsa, sannan ka yarda da cewa Allah shi ne ubangijinka, kuma ka yarda da musulunci a matsayin addininka, ka kuma shaida Muhammad (s.a.w) annabin Allah ne, ka kuma shaida da shugabancin Kur’ani”. Sai ya kara da cewa, a wannan lokaci sai mala’ikun tambaya zasu ce wa junansu ta shi mu tafi kawai domin kuwa duk abin da muke so mu tambaya an gaya masa.[9]

Hafiz Muhammad Sa'id - hfazah@yahoo.com – www.hikima.org – www.haidarcip.org

Haidar Center for Islamic Propagation (HAIDARCIP)

Facebook: Haidar Center - December, 2012



back 1 2 3 4 5 6 next