Rayuwa Bayan Mutuwa 22-Muminin da ya yi magana bayan mutuwa cikin surar Yasin: Annabi Isa (a.s) ya tura wasu mutane guda uku zuwa wani gari domin su isar da sakon Allah. sai mutanen wannan gari suka yi inkarin wadannan mutane, sai wani mutum guda kawai daga cikin mutanen wannan gari ya karba wannan kira, sai kuwa mutanen wannan gida suka yo ca a kansa, bayan sun kashe shi ga abin da yake cewa: “Ni na yi imani da ubangijinku, ku saurare ni. Sai aka ce ma sa ka shiga al’janna, sai ya ce ina ma mutanena sun sani. Dangane da gafarar da Allah ya yi mini, sannan ya sanya ni a cikin manyan mutaneâ€. [3] Abin da kuwa ake nufi da wannan aljanna wacce aka shigar da shi, aljannace ta barzahu, ba wai aljannar da za a shiga ba a ranar kiyama, wannan kuwa ana iya gane shi ta hanyar abin da yake fata yana cewa ina ma mutanena sun san gafarar da Allah ya yi mini ya kuma sanya ni cikin manyan mutane. Wannan fata tashi ba tana nuna cewa ba mutanensa sun san halin da yake ciki kamar yadda yake a lahira ana yaye duk wani hijabi ga mutane, ta yadda kowa zai san halin da kowa yake, Saboda haka wannan rashin sanin halin da mutum yake ciki a lahira yana faruwa ne a wannan duniya, ta yadda mutanen wannan duniyar ba su san abin da yake faruwa ba a waccan duniyar, sannan ayoyi da dama suna bayyana wannan ma’ana. Bayan wannan abin da muka yi bayani a baya, ayoyin da zamu ambata a nan gaba zasu bayyana mana cewa bayan mutuwa da gafarta masa bayan ya shiga aljanna, zai zamana fitilar rayuwar mutanensa zata mutu sakamakon wata tsawa daga sama, Kamar yadda Kur’ani yake cewa: “Ba mu aiko wa mutanensa runduna daga sama ba bayan rasuwarsa, kuma ba zamu yi hakan ba. Babu wani abu da ya kasance sai tsawar bazata sai ga su dukkansu suka kasance matattuâ€. [4] Wadannan ayoyi guda biyu da muka ambata a sama suna nuna mana cewa, bayan shahadarsa da shiga aljannarsa, mutanensa sun kasance suna rayuwa a cikin wannan duniya kwatsam sai mutuwa ta riske su, saboda haka wannan aljanna da ake ambata a baya ba wata aljanna ba ce sai aljannar barzahu. 3-Za a gabatar da Fir’auna da mutanensa ga wuta Za a gabatar da Fir’auna da mutanensa ga wuta safiya da marece, Sannan lokacin da kiyama ta tsaya za a ce musu ya ku mutanen Fir’auna ku shiga cikin matsananciyar azabaâ€.[5] Tare da kula da bangarori guda biyu na wannan aya zamu iya fahimtar kasantuwar Fir’auna da mutanensa a cikin rayuwar Barzahu, kamar haka: Kafin zuwan ranar kiyama sun kasance ana bijiro su ga wuta safiya da yamma, Sannan bayan kiyama ta tsaya za a shigar da su a cikin matsananciyar azaba. Idan da bangare na biyun wannan aya bai zo ba (Sannan ranar kiyama za a shigar da su cikin matsananciyar azaba) da ba za iya fahimtar haka da sauki ba, amma tare da kula da wannan bangare na aya, zai bayyanar mana da cewa akwai azaba a barzahu, domin kuwa idan ba haka ba ne babu ma’anar a kawo batun cewa sannan idan kiyama ta tsaya za a shigar da su azaba mai tsanani.
|