Rayuwa Bayan Mutuwa 2Kur’ani Da Wanzuwar Ruhi Kamar yadda ya zamana tushen bincikemmu a wannan magana shi ne Kur’ani da hadisan Manzo da magadnsa Ahlul baiti (a.s) dan haka tare da amfani da wadannan dalilai zamu ci gaba da binckemmu a kan wannan magana. Ayoyi da dama a cikin Kur’ani suna bayar da sheda a kan cigaban rayuwa bayan mutuwa wadanda ba zamu iya kawo dukkansu ba a cikin wannan ‘yar karamar kasida, saboda haka zamu takaita da kawo wasu daga cikinsu a matsayin misali: 1-Shahidai a tafarkin Allah: Ayoyi da dama a cikin Kur’ani suna ba da shedar cewa shahidai zasu ci gaba da rayuwa bayan tsallaka gadar mutuwa da suka yi, saboda haka zamu yi nuni da ayoyi uku da suka yi magana a kan hakan: A- “Kada ku ce wa wanda aka kashe a tafarkin Allah matacce, domin kuwa rayayye ne, sai dai kune ba ku fahimtar hakanâ€.[1] Ba tare da kula da jumlar “sai dai ku ne ba ku fahimta ba†wacce ta zo a cikin wannan aya, zai iya yiwuwa a yi tunanin cewa ana nufin rayuwarsu ta zamantakewa, domin kuwa kasantuwar sadaukantarwar da suka yi, zai zamana kodayaushe suna raye a cikin zukatan al’umma, ta yadda kodayaushe za a rika tunawa da sunayensu, sannan sadaukarwarsu zata zama rubutun zinari a cikin Littattafan tarihi. Amma abin da ya zo bayan wannan aya yana kore wannan tunanin, domin kuwa idan da ana nufin rayuwarsu ta hanyar tunawa da su da ake yi a cikin al’umma, wannan ba zai zama wani boyayyen abu ba ga al’umma wanda sai Allah madaukaki ya ce, “sai dai ku ne ba ku fahimtaâ€domin kuwa wannan rayuwar kowane mutum yana iya fahimtar hakan. B-“Kada ku yi tsammanin wanda aka kashe a tafarkin Allah ya mutu, domin kuwa rayayye ne ana azurta shi a wajen Ubangijiâ€. C-Suna farin ciki da abin da Allah ya ba su na daga falala, kuma suna albishir ga wadanda ba su riske su ba wadanda zasu daga baya, da cewa kada su ji tsoro ko bakin cikiâ€. “Suna albishir da abin da Allah ya yi musu ni’ima da shi na falala, kuma lallai Allah ba ya tauye ladan muminaiâ€.[2] Wadannan ayoyi na sama suna daraja ta musamman wajen bayyana wannan ma’ana. A cikin wadannan ayoyi ba kawai Allah ya nuna cewa Shahidai suna raye ba ne, ya nuna yadda suke amfanuwa da abubuwan rayuwa, domin kuwa ya nuna yana azurta su kuma sunacikin farin ciki, wanda wannan ya nuna abubuwan da suke nuna rayuwar mutum ta jiki da ta ruhi.
|