Rayuwa Bayan Mutuwa 2Rayuwa Bayan Mutuwa 2 Mawallafi: Ayatullahi Ja’afar Subhani Mai Fassara: Yunus Muhammad Sani Gyara da Tsarawa: Hafiz Muhammad Sa'id Asali Na Biyu Menene Hakikanin Mutuwa? Ya bayyana cewa hakikanin mutum ba jiki ba ne, sannan sakamakon kasantuwarsa ya nisanta daga duk wasu siffofi na jiki (kamar abin da ya shafi lalacewa, rarrabuwa, da makamantansu) zai kasance wanzanje tare da izinin Ubangiji bayan mutuwar jiki. Daga wannan abin da muka fada a sama zamu iya fahimtar ma’anar mutuwa, domin kuwa hakikanin mutum shi ne ruhinsa wanda yake madawwami. Hakikanin mutuwa ba wani abu ba ne sai rabuwar ruhi da jiki sakamakon wasu sharudda da suke faruwa. Wato ruhin mutum zai kai wani mataki na kammala wanda ba ya bukatar jiki, wato zai kai wani mataki wanda zai iya ci gaba da rayuwar da ta dace da shi ba tare da jiki ba. Kasantuwar ruhi bayan mutuwa wani abu ne wanda aka tabbatar a cikin falsafa da ilimin kimiyya, manyan malaman falsafa kamar su Sukrat, Filato da Aristo duk sun tabbar da wanzuwar rai bayan mutuwa a cikin falsafar Kasar Girki. Haka Ibn Sina da shehul Ishrak da Sadrul muta’allihin wadanda suke masana falsafa ne na duniyar musulunci duk sun tabbatar da wannan al’amari ta hanyar dalilan hankali. Sannan yau a kasashen yammacin duniya an sanya shi cikin abin da ake bincike a cikin ilimin kimiyya. Idan a karni na sha tara an karkata zuwa ga wannan duniya ta jiki, da mantawa da abin da yake bayan wannan duniyar kamar Allah, mala’ika da ruhi, da sauran abubuwan da suke a duniyar gaibu, ta yadda suke shakku a kan samuwarsu. Amma farkon karni na ashirin koma kafin nan sakamakon kokarin wasu wadanda suke da imani da samuwar wannan duniya sun sake bude wata sabuwar kofa ta shiga wannan duniya ta gaibu. Ta yadda duniyar ruhi da wanzuwarsa bayan mutuwa ta samu karbuwa wanda muka yi bayani kamar yadda aka gani a bahsimmu da ya gabata.
|