Ziyarar Kaburbura Masu DarajaMutanen da suka rasa wani masoyinsu sakamakon alaka ta jini da soyayyar da take tsakaninsu ba zasu manta da shi ba, zaka ga kodayaushe suna yin taruka domin tunawa da shi sannan suna yin kokari wajen girmama shi. Yayin da mutuwa ta kare su daga saduwa ta jiki, sai suka koma bangaren guda wato ta hanyar ruhi suna saduwa da shi, don haka ne zaka ga suna zuwa wurin da aka rufe shi ta hanyar daidaiku da cikin jama’a domin su ziyarce shi sannan suna yin taruka domin tunawa da shi din. Taron mutuwa da ziyartar kaburburan wadan suka rasu wata al’ada ce wadda ta hade ko’ina a cikin al’ummar duniya, ta haka ne zamu iya cewa wannan al’amari yana da alaka da halittar mutum. Sakamkon soyayyar da take tsakanin mutane da danginsu wadda take janyo su da su zo domin su ziyarce su yayin da suke da rai, wannan shi yake janyo su ziyarci kaburansu yayin da ba su da rai. Musamman kamar yadda yake a musulunci cewa ruhin mutum sabanin jikinsa ba ya lalacewa. Ba ma haka ba kawai yakan kara samun karfi na musamman a wannan duniyar sannan yana jin dadin kulawar da masoya suke yi masa ta hanyar ziyartarsa da yi masa addu’a kamar karanta masa fatiha da makamantanta, ta yadda suke kara masa nishadi da karfi. Don haka bai dace ba mu sha kan mutanen a kan gudanar da irin wannan al’ada wadda take wani nau’in halittar mutum ce, Abin da ya kamata shi ne mu nuna musu yadda ya kamata su aiwatar da hakan, ta yadda sakamakon soyayya ga masoyansu kada su kai zuwa ga sabon Ubangiji. Ziyarar Kaburburan Malamai Abin muka yi Magana a kan shi a sama ya shafi ziyarar sauran mutane ne da suke da alaka ta jini da take tsakanin mamaci da mai ziyararsa. Ta yadda sakamakon wannan ziyara zai biya bukatun wanda ya ziyarta ta hanya kulawar da ya yi masa, ta yadda masu ziyara zasu tsabtace kabarinsa har ma su sanya wa kabarin turare da sauransu. Amma a cikin wadannan masoya akwai wadanda suke malamai ne da wadanda suka kawo gyara a cikin duniya wadanda suke da wani matsayi na musamman wanda ya sha bamban da wadanda suka gabata. Wadannan sun kasance tamkar kamar kyandir ne wanda ya kone kansa domin ya haskaka wa waninsa, haka suma suka haskaka wa mabiyansu ta yadda suka yi rayuwa a cikin kunci, amma suka bai wa mabiyansu taskar ilimi madawwamiya. Sakamakon haka ne suka cancanci yabo da girmamawa. Musamman malamai wadanda suka koyar da al’umma littafin Allah da Sunnar Manzo (s.a.w) ta yadda suka bai wa al’umma abin da zai kai su zuwa ga cin nasarar rayuwar duniya da lahira kuma madawwamiya. Don haka halartar kabarin irin wadannan malaman yana nufin girmama wadanda suke cikin kabarin ne, Sannan kuma sakamakon abin suka yi na yada ilimi ne ya janyo soyuwar al’umma zuwa gare su ta yadda suka yi hidima da kare wadannan ayyuka na su (Littattafai da makamantansu kamar kaburburansu). Hakika duk al’ummar da suke girmama ilimi da malamai ba zasu taba shiga cikin tarkon kuncin ilimi ba. Ziyarar Kaburburan Shahidai Haka nan ziyartar kaburburan Shahidai wadanda suka bayar da jininsu domin kare al’ummarsu da addinin Allah shi ma yana da matsayi na musamman wanda ya fi na sauran mutanen da ba su ba. Ziyartar kaburburan shahidai wadanda suka rasa rayukansu a kan tafarkin Ubangiji, bayan tasirin da yake ga ruhin mutum, sannan yana nuna rikon alkawari a kan tafarkin da suka bayar da jininsu a kai. Wato mai ziyara kamar yana cewa ne yana nan kan tafarkinsu sannan zai yi kariya a kan wannan abin mai tsarki da suka bayar da jininsu. Domin mu kara fahimtar abin da kyau bari mu ba da wani misali wanda yake raye a halin yanzu: Mutumin da ya ziyarci Dakin Allah kafin ya yi dawafi yakan yi wa Hajrul Aswad sallama ya kuma sanya hannu ya shafe shi da ma’anar cewa yana yin bai’a ne ga Annabi Ibrahim (a.s) gwarzon tauhidi, da nufin cewa tauhidi shi ne abu na gaba a wajensa. Ta yadda zai yi iya kokarinsa wajen yada shi, amma tunda yanzu ba zai iya kai hannunsa ba zuwa ga Annabi Ibrahim ta yadda zai yi masa bai’a wajen daukar alkari domin wannan aiki shi ne sai ya kai hannunsa ga abin da shi Annabi Ibrahim (a.s) ya bari ta yadda zai gabatar da bai’arsa ta hanyar wannan abin da ya bari. Ya zo a cikin hadisi cewa yayin da mutum yake mika hannunsa zuwa ga Hajrul Aswad yana cewa ne: “Na mika amana da alwakarin da na dauka, sannan na jaddada bai’ata ka sheda a kan hakanâ€.[3] Ziyartar shahidan Badar da Uhud da Karbala da sauran masoyan da suka bayar da jininsu a tafarkin Allah yana bayyanar da wannan al’amari. Masu ziyarar wadannan wurare masu tsarki sukan yi wa masu wannan wuri sallama da mika gaisuwa zuwa ga ruhinsu tsarkaka, sannan suna daukar alkawari ne a kan cigaba da hanyarsu.
|