Bidi’a A Cikin AddiniAbin jin dadi a nan wasu daga cikin masanan yammacin duniya sun fahimci wannan sharudda na sama Sakamkon haka ne John Jak a cikin littafinsa (dokin zaman tare) ga abin da yake cewa: Wajen gane dokokin da zasu yi wa al’ummu amfani, dole hankali na gaba daya ya kula da duk bukatocin mutane amma ba tare da ya kalli shi kansa ba, sannan ya zamana ba shi da wata alaka da wannan duniya ta dabi’a (nature) Amma kuma yana da cikakkiyar masaniya a kanta, Sannan dacewa ko cin nasararsa ba ta da alaka da mu, amma a shirye yake ya taimake mu domin mu ci nasarar rayuwarmu. Kawai abin da zai wadatar da shi, shi ne alfaharinsa wanda sakamkon wucewar zamani ne zai bayyana, wato mai yiwuwa ya yi hidima a cikin karni guda amma sai a wani[2] karnin ne sakamako zai bayyana. A nan sakamakon ka’idojin na hankali mun ga yadda kafa doka ta takaita kwai ga Allah madaukaki. Abin da ya rage a nan shi ne mu ga me Kur’ani yake cewa dangane da haka: Dangane da wannan magana kuwa Kur’ani shi ma ya karfafa hukuncin da hankali ya yi ne domin kuwa shi ma ya tabbatar da cewa babu wani wanda yake da hakkin kafa doka sai Allah madaukaki. Ayoyi da dama ne kuwa suka bayyanar da wannan magana, a nan dmin mu takaita kawai zamu kawo wasu ne daga cikin wadanda suke yin magana a kan hakan: 1-â€Babu hukunci sai ga Allah, kuma ya yi umrni da cewa kada a bauta kowa sai shi kuma wannan shi ne addini tsayayyeâ€.[3] Jumlar da take cewa “babu hukunci sai ga Allahâ€tana bayyanar da cewa duk wani nau;in hukunci ya kebanta da Allah ne kawai. Sakamakon cewa shi kadai ne yake da wannan ikon don haka ya ce shi kawai za a bauta wa. 2-Ahlul kitab Sun dauki malamansu da Annabi Isa a matsayin ubangijinsu, sabanin Allah madaukaki[4]. Wannan aya tana bayyanar da yadda Ahlul kitab suka dauki hakkin da Allah ne kawai yake da shi suka mika wa malamansu, mai makon su koma zuwa ga Littattafan da aka aiko musu wajen samun hukunce-hukunce, sai su koma zuwa ga malamansu batattu, duk da kuwa sun san cewa wani lokaci sakamakon wasu dalilai suka halatta abin da Allah ya haramta su kuma haramta abin da Allah ya halatta, sakamakon haka ne ta bangaren kadaita Allah a wajen kafa doka suka kasance mushrikai. Addi Bn Hatim ya kasance kirista yana cewa: Yayin da shigo wajen mazon Allah a lokacin yana karanta wannan ayar wacce ma’anar ita ce “Kiristoci da yahudawa sun kasance sun dauki malamansu a matsayin ubangijinsuâ€. Sai na cewa Manzo wannan al’amari ba shi da inganci. Sai Manzo ya ce: Sukan halatta haram su kuma haramta halas, sannan kuma kuna yi musu biyayya ko ba haka ba ne? Sai na ce haka ne. Sai ya ce: to wannan kawai ya wadatar ya zamana kun dauke su matsayin ubangijinku[5]. Tare da la’akari da abin da muka fada a sama a cikin wannan Bahasi zamu fahimta cewa kafa doka kawai ya takaita ne ga Allah mai tsarki. Sannan ayyukan annabawa da imamai ne suke kawai bayyanar da wadannan doki na Allah madaukaki, sannan ba su da ikon sanya hannu a cikin kafa dokokin Ubangiji.
|