Umar da Ra'ayin Shari'a



A cikin abin da Umar dan Khaddabi ya saba wa nassin shari'a na fifita ra'ayinsa da son ransa:
Daga ciki, Mutu'ar Hajji
Mutu'ar hajji, manzon Allah (s.a.w) ya yi aiki da ita da umarnin Allah madaukaki, kuma tana daga cikin abin da nassin kur'ani ya zo da ita da fadinsa madaukaki a bakara: kuma duk wanda ya yi tamattu'I da umara zuwa hajji to sai ya yanka abin da ya sauwaka na daga hadaya, wanda kuwa bai samu ba, to sai ya yi azumin kwana uku a hajji da kuma bakwai idan kuka koma, wannan shi ne goma ke nan cikakkiya, wannan kuwa ya hau kan wanda gidansa ba ya masallaci mai alfarma, kuma ku ji tsoron Allah, ku sani Allah mai tsananin ukuba ne. bakara: 196.
Amma siffar tamattu'I da umara zuwa hajji shi ne ya fara yin hajjin tamattu'I da yin harama da umara a watannain hajji daga mikati  sai ay zo makka ya yi dawafi da daki, ya yi sa'ayi tsaknain safa da marwa, sannan sai ya yi kasaru da hajji a makka, abin da ya fi shi ne ya zo masallaci ya fita daga daga nan zuwa arafa, sannan sai ya yi ifadha zuwa masha'ar alharam, sannan sai ya zo da yin ayyukan hajji kamar yadda ya zo dalla –dalla  mahallinsa. Wannan shi ne umarar ta mattu'I da hajjinsa.
Ibn abdulbar alkurdabi yana cewa: babu sabani tsakanin malamai cewa tamattu'I a fadin Allah madaukaki : duk wanda ya yi tamattu'I da umara zuwa hajji to yana kansa abin da ya sauwakka na hadaya. Bakara: 196. Yana nufin shi ne yin umara a watannin hajji kafin yin hajji .
Na ce: wannan shi ne hukuncin wanda yake nesa da makka sama da mil arba'in da takwas ta kowane janibi bisa magana mai inganci .
Kuma an kira hajji ne da wannan yanayin da hajjin tamattu'I saboda a cikinsa akwai jin dadin halaccin abubuwan da aka haramta a muddar tsakanin ihrami da umara, da ihrami da hajji, wannan shi ne abin da umar ya ki shi da wasu mabiyansa. Yana fada kamar yadda ya zo a abubu dawud da wasu littattafan sunan  cewa: a yanzu zamu je yin aikin hajji zakarorinmu suna diga?
A cikin littafin majma'ul bayan wani mutum ya ce: a yanzu zamu fita hajji  kawunanmu suna zuba? Kuam annabi (s.a.w) da  man ya gaya masa cewa: kai ba zaka taba imani da ita (ayar hajjin tamattu'i) ba har abada .
Daga abu musa al'ash'ari ya ce: ya kasance yana bayar da fatawar yin tamattu'I sai wani mutum ya ce: ka yi sannu da wasu fatawowinka, kai ba ka san abin da sarkin musulmi ya yi ba –wato umar- a game da aikin hajji bayan ba ka nan, har sai da abu musa ya hadu da umar sai ya tambaye shi kan wannan, sai umar ya ce: na sani cewa annabi ya yi da shi da sahabbansa, sai dai ni ina kin in ga suan yin angwanci (kusantar matansu) a kan gadaje, sannan sai su tafi kuma yin aikin hajji alhalin kawukan (mazakuntansu) suna diga .
Daga abu musa ta wata hanyar dai cewa umar ya ce: ita sunnan manzon Allah (s.a.w) ce –hajjin tamattu'i- sai dai ni ian jin tsoron kada su kusanci matan karkashin karagu, sannan sai su yammata da su zuwa hajji .
Daga abu nudhrata ya ce: ibn abbas ya kasance yana umarni da yin mutu'a, ibn zubair kuma yana hanawa. Ya ce: sai na gaya wa jabir wannan lamarin, sai ya ce: ni kuwa zan ba ka labarin, mun yi tamattu'I tare da manzon Allah (s.a.w) amma yayin da umar ya tsayu da ikon halifanci sai ya ce: Allah ya kasance yana halattawa manzonsa abin da ya so da abin da ya so, kur'ani yana sauka masaukinsa, ku cika hajji da umara kamar yadda Allah ya umarce ku , ku nisanci auren wadannan matan, ba za a kawo mini wani mutum ba da ya kusanci wata mata zuwa ajali sai na jefe shi da dutse .
Kuma wata rana umar ya yi wa mutane huduba sai ya fada yana kan mimbari da dukkan 'yanci da bayyanawa a fili cewa: mutu'a biyu sun kasance a lokacin manzon Allah (s.a.w) kuma ni ina hana yin su ina kuma yin ukuba  a kan yin su: mutu'ar hajji da mutu'ar mata .
 A wata ruwayar  yana cewa ne: ya ku mutane uku sun kasance a lokacin manzon  Allah (s.a.w) amam ni ina hana su, ina haramta su, ina yin ukuba  a kan su, mutu'ar hajji, da mutu'ar mata, da hayya ala khairil amal.

Fasali game da yi wa Umar inkari kan haramcinsa
Ahlul Baiti (a.s) baki daya sun yi masa inkarin wannan lamarin kuma mabiyansu baki daya sun bi su a kan hakan, babu wani daga manyan sahabbai da ya rdar amsa da wannan kuma labaransu suna da tawaturi.
Abin da muslim ya kawo a babin halaccin mutu'a kawai ya isa a kitabul hajji na littafinsa , a cikin an karbo daga shakik ya ce: usman ya kasance yana hana tamattu'i, Ali kuwa ya kasance yana hanawa, sai usman ya ce da Ali (a.s) wani abu kan hakan. sai Ali (a.s) ya ce: na sani ya kai usman mun yi tamattu'I lokacin manzon Allah (s.a.w) sai usman ya ce haka ne, amma ai muna jin tsoro lokacin!!
Haka nan ya zo daga sa'id dan musayyibi ya ce: Ali da usman sun hadu a asfan, ya kasance usman yana hana tamattu'I da umara, sai Ali (a.s) ya ce: me kake so da al'amarin da manzon Allah (s.a.w) ya aikata shi kai kuma kake hana shi? Sai usman ya ce: rabu da mu. Sai Ali (a.s) ya ce: ni ba zan iya barin ka ba…hadisi.
Haka nan daga gamin dan kais ya ce; na tambayi sa'ad dan abi wakkas game da tamattu'I sai ya ce: mun yi a lokacin manzon Allah (s.a.w), sai dai wannan –yana nufin mu'awiya- shi mai kafirta da mai al'arshi ne.
Haka nan daga abul ala' daga mudrif ya ce: imrana dan hasin ya ce da ni ba na ba ka labari da wani kalami ba a yau da Allah zai amfanar da kai da shi bayan yau, ka sani manzon Allah (s.a.w) ya yi umara da hajjin tamattu'I da shi da wata jama'a daga alayensa da ahlinsa a goman aikin hajji, kuma babu wata aya da ta sauka tana shafe wannan, sannan bai hana shi ba har ya wuce, sai dai bayan nan sai kowane mutum ya ga dama sai ya bi ra'ayin da ya so.
Daga humaid dan hilal daga mudrif ya ce: imrana dan hasin ya ce mini ba na ba ka  labarin da zai sanya ta yiwu Allah ya amfane ka da shi ba , ka sani manzon Allah (s.a.w) ya hada hajji da umara, sannan bai hana shi ba har ya rasu, kuma babu wata aya da ta sauka tana haramta wannan… hadisi.
Daga katada daga mudrif ya ce: imrana dan hasina ya aika mini a rashin lafiyar da ya rasu a cikinsa ay ce: ni ina ba ka labari da ta yiwu ya amfane ka bayana, amma idan na rayu ka boye mini, idan na mutu kuwa ka ba wa duk wanda ka dama labarinsa, ka sani annabin Allah (s.a.w) ya hada hajji da umara, sanna babu wani littafi da ya sauka , sannan annabin Allah (s.a.w) bai hana ba, sai dai kawai wani mutum –yana nufin umar- ya fadai abin da ya ga dama na ra'ayinsa.
Sannan da wani sanadin daban dai ta hanyar imrana dan muslim, daga abu raja' ya ce; imrana dan hasin ya ce: ayar tamattu'I yana nufin hajji da umarar tamattu'I ta sauka sai annabin Allah (s.a.w) ya umarce mu da yin sa, sannan babu wata aya da ta sauka tana shafe wannan ayar ta hajjin tamattu'I , sannan manzon Allah (s.a.w) bai hana ba har ya rasu, sai dai kawai wani mutum ya ga dama ya fadi ra'ayinsa.
Na ce: wannan hadisin yana da hanyoyi masu yawa a littafin muslim daga imrana dan hasin da zamu isu da abin da muka kawo, kuma buhari ma ya kawo shi daga imrana dan hasin a babin tamattu'I daga kitabul hajji a littafinsa, sai a koma wa shafin na 187, a juzu'I na farko.
Da abin da ya zo a babin mutuma daga muwattar maliku  daga Muhammad dan abdullahi dan haris dan naufal dan abdulmutallib ya ce: ya ji sa'ad dan abi wakkas da dhahhak dan kais a shekarr da mu'awiya dan abu sufyan yan yi hajji suna ambaton mutu'ar umara zuwa hajji, sai dhahhak dan kais ya ce: ba mai yin ta sai wanda ya jahilci lamarin Allah mai girma da daukaka. Sai sa'ad ya ce: tir da abin da ka ce ya kai dan dan'uwanak, sai dhahhak ya ce: ai umar dan khaddabi ya hana yin hakan, sai sa'ad ya ce: hakika manzon Allah (s.a.w) ya yi, kuma mu ma mun yi tare da shi (s.a.w).
Haka nan a masnda ahmad daga hadisin inb abbas  ya ce: mun yi tamattu'I tare da manzon Allah (s.a.w) , sai urwa dan zubair ya ce: abubakar da umar sun hana yin tamattu'I, sai ibn abbas ya ce: me urayya  yake cewa? Sai ya ce: ai abubakar da uamr sun hana mutu'a, sai ibn abbas ya ce: ina ganin zasu halaka ke nan. Sai ya ce: annabi (s.a.w) ya ce a yi, su kuma abubakar da umar suna hanawa .
Daga ayyuba ya ce: urwa ya ce da dan abbas: shin ba ka ji tsorn Allah ba? Kana bayar da fatawar yin mut'a?! sai ibn abbas ya ce masa: tambayi babarka ya kai urayya. Sai urwa ya ce: amma abubakar da umar ba su ssyi ta ba. Sai inb abbas ya ce: wallahi ina ganin ba zaku daina ba har sai Allah ya azabatar da ku, muna gaya muku daga annabi (s.a.w) ku kuma kuna gaya mana da abubakar da umar….hadisi .
Haka nan a babin mutu'a daga littafin aure daga lilttafin sahih muslmi  daga wani mutum daga ya tambayi dan abbas game da mutu'a sai ya ba shi fatawar halaccin ta. ibn zubair kuwa ya kasance yana hana yin ta, sai ibn abbas ya ce masa: ga uwar ibn zubair can tambaye ta, zata ba ka labarin cewa manzon Allah (s.a.w) ya halatta. Sai suka shiga wurin ta. ya ce: sai muka shiga, sai ga wata mata makauniya mai kiba, sai ta ce: manzon Allah (s.a.w) ya yi umarni da yin ta.
Ya zo a cikin sahihi tirmizi , an tamayi abdullahi dan umar game da mut'a sai ya ce: halal ce. Sai mai tamaya ya ce masa: ai babanka ya hana yin ta, sai ya ce: to don babana ya hana yin ta fa, ai manzon Allah (s.a.w) ya yi umarni da yin ta, shin umarnin babana za a bi ko kuma umarnin manzon Allah (s.a.w)? sai mutumin ya ce: umarnin manzon Allah (s.a.w) dai. Sai ya ce: to manzon Allah (s.a.w) ya halatta yin ta. da sauran ruwayoyi masu yawa kan hakan, da suka zo a cikin inkari ga umar kan hanin da ya yi wa mutu'a.
Hada da cewa hajji ban kwana akwai isar da sako ga mutune masu imani, ka koma wa hadisin hajjin annabi a sahih musulim  zaka samu ya shelanta hakan a gaban shedu masu yawa, da suka wuce sama da mutane dubu dari maza da mata daga al'ummarsa, sai suka hadu suka yi hajii tare da shi da daga dukkan sassan duniya. Kuam da ya shelanta hakan sai suraka dan malik dan Has'am ya tashi ya ce: ya ma'aikin Allah (s.a.w), shin wannan tamattu'in kawia wannan shekarar ce ko kuwa har abada? Sai manzon Allah (s.a.w) ya sanya yatsunsa daya cikin daya sai ya ce: umara ta shiga cikin hajji, umara ta shiga cikin hajji har abada.
Kuma Ali ya zo daga yaman da taguwowin manzon Allah (s.a.w) sai ya samu fadima (a.s) tana daga cikin wadanda suka sauke harami ta sanya tufafi da aka runa, ta yi kwalli, sai ya musa mata wannan. Sai ta ce: babana ya halatta hakan. sai ya tafi wurin manzon Allah (s.a.w) ya nemi bayaninsa, sai ta ba shi labari, sai ya ce: ta yi gaskiya, ta yi gaskiya…Hadisi.

Daga ciki, akwai auren mutu'a
Allah da manzonsa sun shar'anta kuma musulmi sun yi a lokacinsa, har sai da ya hadu da ubangiji mai daukaka, sannan sai suka yi bayansa a lokaicn abubakar har sai da ya wuce, sai umar ya zo bayansa suna kan yin ta, sai kuma ya hana da fadinsa a kan mimbari yana mai cewa:  mutu'a biyu sun kasance a lokacin manzon Allah (s.a.w) amma ni ina hana su, kuma ina yin ukuba a kan yin su: mutu'ar hajji da mutu'ar mata .
Abin da ya zo a littafin Allah Ambato mai hikima, gaskiya mai girma ya isa hujja yayin da ya yi nassi da halarcinta a fadinsa madaukaki: abin da kuka ji dadi da shi daga gare su, to ku ba su ladansu wajibi ne. nisa'i: 24. Saboda haka aure a musulunci hudu ne da Allah ya halatta shi a ayoyi hudu daga surar nisa', kamar yadda muka kawo dalla – dalla a littafinmu na Mutu'a.
Amma nassin littattafan rawayoyi masu littattafan sihah sun karbo shi da dukkan bayani, kuma hadisin da muslim ya kawo daga abu nudhrata ya ishi hujja da ya zo a babin mu'tar hajji shafi na 467, a juzu'I na farko daga littafinsa yayin da ya ce: ibn abbas ay kasance yana umarni da yin mutu'a, ibn zubair kuma yana hana yin ta, sai na gaya wa jabin wannan , sai ya ce: ni kuwa na san maganar, mun yi mutu'a tare da manzon Allah (s.a.w) , amma yayin da umar ya samu halifanci  sai ya ce: Allah ya kasance yana halatta wa manzonsa abin da ya so, da wanda ya so , don haka ku cika hajji da umara, ku nisanci auren wadannan matan, ku sani babu wani mutum da za a zo mini da ji ya yi wannan auren zuwa wani ajali sai na jefe shi da duwatsu .
Kuma masu bahasin ilimi da zurfafawa ya ishe su hujja idan suka bi abin da muka kawo a wannan bahasin da kuma littafinmu fusulul muhimma, da mas'alolin sabani, da amsar Musa jarullah, da kuma abin da mujallar irfani ta yada a juzu'I na goma na mujalladinta na 36, a gun mun yi bayani mai fadi, haka nan abin da ya zo a fasaloli takwas:
1- Hakikanin wannan aure bisa shari'ar musulunci.
2- Haduwar al'umma kan shar'anta wannan a addinin musulunci.
3- Dalilin kur'ani kan shar'anta shi.
4- Shar'anta shi a nassosin ruwaya.
5- Masu ganin an shafe shi da hujjarsu kan hakan.
6- Littattafai sahihai suna kawo cewa halifa na biyu shi ne ya shafe shi.
7- Masu musunta hakan daga sahabbai da tabi'ai .
8- Ra'yin shi'a da hujjar su kan hakan.
Kamar yadda zamu ga –bisa gaskiya- gaskiya tana tare da mu a wannan fasalolin da dukkan abin da yake karfafarmu na dalilin shari'a na littafin Allah da sunnar annabinsa, da kuma asasin shari'a da al'umma ta yi ittifaki a kansa, da yin aiki da shi, don haka kada wannan ya kubece wa wani mai bahasi daga al'ummar Muhammad (s.a.w), sannan bayan ya bi ya duba, to sai hukunci ya rage nasa bisa haramci ko kuma halacci.

Daga ciki, tasarrufi cikin kiran salla ta hanyar kara wani abu a cikinsa
Idan muka bi sunnar da ta zo agme da lafuzzan kiran salla dana ikama a lokacin manzon Allah (s.a.w) zamu ga babu lafazin "assalatu khairun minan naumi", babu shi a lokacin abubakar ma, kamar yadda dukkan maruwaita sunna da masu nakadin hadisai suka sani, sai dai umar ya yi umarni da yin sa a wani lokaci daga halifancinsa, yayin da ya so shi, ya ga kyawunsa a kiran sallar asuba, sai ya shar'anta shi lokacin kuma ya yi umarni da shi, kuma bayanai a kan haka suna da yawa mutawatirai ne daga suka zo daga imaman gidan shiriya da tsarki.
Kuma abin da aka ruwaito daga masu rubutun ruwayoyi da abin da ake gani a littattafai kamar na Imam malik a muwatta yana cewa: labarin da ya samu shi ne mai kiran salla ya zo wurin umar yana neman izininsa da sallar asuba, sai ya same shi yana mai bacci. Sai ya ce: salla ta fi bacci. Sai umar ya umarce shi ya sanya ta a kiran sallar asuba.
Zarkani yana fada a ta'alikinsa ga wannan kalma a sharhin muwatta cewa: wannan labari ne da darukutni ya ruwaito shi a sunan, daga waki'I a musannaf, daga umari, da nafi'u da ibn umar, daga umar yace: idan ka kai ga hayya alal falah a kiran salla, to ka ce: salla ta fi bacci, salla ta fi bacci (assalatu khairun minan naum).
Na ce: haka nan ibn abi shaiba ya kawo a hadisin hisham dan urwa, haka nan ma da yawa daga malaman ahlussunna wal jama'a sun ruwaito wannan ruwaya.
Don haka babu wata kima ga abin da muhammd dan Khalid da abdullahi alwasiti ya kawo daga babansa daga Abdurrahman dan Ishak, daga zuhuri, daga salim daga babansa cewa annabi (s.a.w) ya nemi shawarar mutane kan abin da yake iya kiran su zuwa ga salla, sai suka fadi busa kaho, sai ya ki hakan saboda abin da yahudawa suke yi ne, sannan sai suka kawo kararrawa, sai ya ki, saboda abin da nasara (kiristoci) suke yi ke nan, sai aka nuna wa wani mutumin madin kiran salla da dare a farki, ana kiran sa da abdullahi dan zaid, da amru dan khidab, sai ya buga wa manzon Allah (s.a.w) kofa da dare, sai manzon Allah (s.a.w) ya umarci bilal sai ya yi kiran salla da shi. Ya ce: zuhuri ya ce: sai bilal ya kara wannan kalma ta "assalatu khairun minan naum" a kiran sallar asuba, sai annabi (s.a.w) ya tabbatar da wannan. Ibn maja ne ya kawo shi a babin kiran salla, a sunan dinsa.
Bacin wannan ruwaya ya isa bisa la'akari da bayanai masu yawa da suka zo a ruwayoyi da tarihi, daga cikin akwai abin da yahaya yake fada game da mai wannan ruwayar ta sama wato muhammd dan Khalid dan abdullahil wasidi. Yake fada cewa: shi mutumin banza ne, wani lokaci ya ce: ba komai ba ne shi. Ibn udayy ya ce: ahmad dan hambal da yahaya bin mu'in sun yi inkarin wannan mutumin da tsanantawa. Abu zur'a ya ce: shi mai rauni ne matuka. Yahaya bin mu'in ya ce: Muhammad dan Khalid dan abdullahi makaryaci ne, idan kun hadu da shi to ku mare shi.
Na ce: haka nan zahabi ya kawo shi a littafinsa na mizan, daga malaman jurhu da ta'adil, sun kawo bayani kansa sai a koma masa. Daga irin wannan bataccen hadisin akwai abin da suka kawo da ya zo daga abu mahzura yayin da ya ce: na ce da manzon Allah (s.a.w) sanar da ni kiran salla, ya ce; sai ya shafa kaina sanna sai ya ce:  ka fadi; allahu akbar, allahu akbar, allahu akbar kana mai daga sauti da shi, sannan sai ka ce: ashhadu an la'ilaha illallah, ashhadu an la'ilaha illallah, ashhadu anna muhammadar rasulullah, ashhadu anna muhammadar rasulullah, hayya alas salat, hayya alas salat, hayya alal falah, hayya alal falah. Idan na sallar asuba ne sai ka ce: assalatu khairun minan naum, assalatu khairun minan naum, allahu akbar, allahu akbar. Abu dawud ya kawo shi ta hanyar abi mahzura ta hanya biyu:
Ta Farko: daga Muhammad dan abdulmaliki daga abi mahzura daga babansa daga kakansa. Shi kuwa Muhammad abdulmalik wannan ba a dogaro da shi kamar yadda zahabi ya kawo a mizanul I'itidal.
Ta biyu: daga usman bin sa'ib daga babansa, kuma babansa sananne ne da munana da karerayi da nassin zahabi da ya kawo a mizan.
Sannan kuma muslim kansa ya kawo wannan hadisin daga abu mahzura da kansa ba tare da wannan lafazin na "assalatu khairun minan naum" a ciki ba.
Da sannu kuma zaka ji abin da abu dawud ya ruwaito da waninsa ma daga Muhammad dan abdullahi dan zaid a lafuzzan kiran salla da bilal ya kasance yana karanta wa abdullahi dan zaid shi, kuma babu wannan Kalmar ta "assalatu khairun minan naum" a ciki.
Tare da cewa wannan abu mahzura din yana daga cikin sakakkun makka kuma daga mu'allafatu kulubahum da suka shiga musulunci bayan bude makka, kuma bayan manzon Allah (s.a.w) ya koma daga hunain yana mia nasara kan hawazinawa, duk a wannan lokacin babu wnai mutum da abu mahzura ya fi ki fiye da manzon alah (s.a.w), kuma ba ya karmar umarnin annabi (s.a.w). ya kasance yana yin isgili da mai yi wa annabi (s.a.w) kiran salla, sai ya rika daga sautinsa yana mai yin isgili. Sai dai jakar azurfa da ganimomi da manzon Allah (s.a.w) ya ba shi yayin da ya ba wa sakakkun yakin makka na daga makiyansa ce ta sanya shi karkata. Da kuma kyawawan halayen manzon Allah (s.a.w) da suka yalwaci dukkan wani wanda ya yi riko da Kalmar shahada daga munafukai, tare da tsanantawarsa kan wanda bai yi  riko da ita ba, da kuma shigar larabawa cikin addinin Allah jama'a jama'a, duk wannan shi ne ya sanya abu mahzura da ire irensa rusanawa da shiga cikin abin da mutane suka shiga cikinsa, kuma bai yi hijira zuwa madina ba har ya mutu a makka . Allah ne ya san badininsa.
Hada da cewa manzon Allah (s.a.w) ya gaya wa mutane uku; wato abuhuraira, da abu mahzura, da samura dan jundub, cewa wanda ya mutu daga karshe a cikinku dan wuta ne .
Wannan kuwa usulubi ne na mai hikima da annabi (s.a.w) ya yi domin ya nesantar da munafukai daga kama ikon tafiyar da sha'anin daula da al'ummar musulmi, yayin da ya san badinin wadannan mutane ba shi da kyau, sai ya so ya sanya kokwanton su a zukatan musulmi don a guje masu, don tsoron kada wani daga wannan al'umma ya karkata zuwa gare su a kan wani abu da ya shafi musulmi, sai ya yi alkawarin shiga wuta ga kowannensu ta hanyar nuni da cewa na karshen su yana cikinta. Don haka ne sai ya sanya lamarin tsakanin wadannan mutane uku bisa daidaito, kuma bai bi wannan lamarin da wani bayani daban ba, har dai lokaci ya tsawaita kan wannan lamarin, har manzon Allah (s.a.w) ay hadu da ubangijinsa madaukaki, sai wannan ya sanya masu hankali daga al'ummarsa su nesantar da wadannan baki daya daga dukkan wani abu na matsayi da ake ba wa mutane amintattu masu adalci daga hakkokin al'umma a addinin musulunci, domin ilimi a dunkule yana wajabta nisantar da dukkan su uku saboda rashin sanin hakikanin su. Ba don halaccin nesantar dukkan su ba, da mai hikima annabi rahama (s.a.w) bai yi irin wannan bayani kansu ba.
Idan ka ce: ya yi haka ne saboda wani abu da ya boyu gare mu tsawon zamani.
Sai in ce: da akwai wani dalili da babu yadda zai sanya wadannan mutane uku dukansu cikin a nesanta da su bisa daidaito .
Hada da cewa babu wani bambanci a gun mu na yin bayanin dalili ko rashin sa bayan mun samu zuwansa daga annabi (s.a.w) saboda daidaiton natija ga mutanen uku baki daya, domin babu makawa sai dai mu yi aiki da abin da muka samu na ilimin a dunkule.
Idan kuwa ka ce: ai an yi musu alkawarin wuta a dunkule ne kafin mutuwar na farko da na biyu ta yadda da sun mutum sai mu samu bayani da ilimi dalla dalla, sai ya ayyana a kan na karshe ke nan, don haka babu matsalar dunkulewar bayani.
Sai mu ce: na farko dai annabawa (a.s) kamar yadda ya hanu a kansu su bar wani bayani alhalin akwai bukata gare shi, haka nan ya hanu gare su su yi jinkirnsa daga lokacin da ya dace. Kuma lokacin da ake bukatar a nan yana hade da lokacin da gargadi ya zo daga nisantar kowannensu, domin tun lokacin da suka musulunta sun kasance mahallin ibtila'in sauran musulmi, don haka sai aka dauki matakin hana su wasu hakkokin  shari'a da suka hada da limanci a sallar jam'I, da karbar shedarsu a kotun shari'a, da bayar da fatawa da yin hukunci, tare da cewa ko da ma suna da sharuddansu, da sauran abubuwna da ake shardanta adalci da tsentseni a cikinsu. Ba don wajabcin nesantar da su ba, da bayanin hakan bai jinkirta ba, don haka ya nisanta ga manzon Allah (s.a.w) ya hana wani hakkinsa na shari'a ba tar da wani dalili na shari'a ba, kuma ya nisanta ga annabi (s.a.w) ya kunyata wanda bai cancanci kunyatuwa ba har ya mutu da kaskanci, don ba mu san kubutarsa ba sai da gabatuwar mutuwarsa.
Na biyu: Allah yana shaidawa mun yi iyakacin kokarinmu mu gano wnda ya riga mutuwa da na karshen mutuwa mun kasa samun tabbaci, domin maganganu suna karo da juna a nan kamar yadda ya zo a tarihin da marubuta rayuwarsu suka rubuta .
Na uku: bai kasance daga dabi'ar manzon Allah (s.a.w) wanda yake rahama ne mai tausayi ga al'umma ya tozarta wani da magana, alhalin Allah (s.w.t) yana fada game da shi cewa: lallai kai mai dabi'u ne masu girma. Don haka da wani daga cikin wadannan ukun ya kasance akwai wani alheri tare da shi, da bai yi wannan magana game da shi ba, wacce zata sanya al'umma ta nesantar da shi, sai dai wahayi ne ya sanya manzon Allah (s.a.w) fadin wannan wanda shi mai daraja; ba ya magana da son rai. Najm: 3, sai dai idan wahayi ne aka yi masa shi.
Fadakarwa:
Duk wanda ya san ra'ayin 'yan'uwanmu ma'abota mazhabobi hudu tun farkon kiran salla da ikama da shar'anta su ba zai mamakin yadda suak sallama wa wannan dadin ba, domin dadi da ragi su a wurinsu tun farko ba sa ganin kiran salla daga abin da Allah ya shar'anta wa manzonsa da yin wahayi ba, kuma ba sa ganin sa abin da manzon Allah (s.a.w) da kansa ya fara shi kamar sauran hukunce-hukuncen shari'a, suna ganin ya faru ne sakamakon wani mafarki da wani sahabi ya yi a bacci ne kamar yada suak kawo suak hadu a kansa, suka ruwaito shi a abin da suka inganta shi na ruwayoyi.
Duba abin da ya zo daga gaer su na daga abin da ya fi inganci gun su, daga abu umair dan anas daga ammarsa daga mutanen madina, ya ce: manzon Allah (s.a.w) ya himmantu da sha'anin salla yaya za a hada mutane gare ta, sai aka ce masa: kafa wata tuna, idan suka hango ta sai kowa ya sanar da kowa, sai wanan bai kayatar da shi ba, sai suka gaya masa busa kahon yahudawa sai bai kayatar da shi ba saboda na yahudawa ne. sai uska kawo masa shawarar buga kararrawar kiristoci, da farko kamar ya ki shi, sai ya yi aiki da shi na katako amma, sai abdullahi dan zaid ya juya yana mai damuwa saboda bakin cikin manzon Allah (s.a.w) sai aka nuna masa kiran salla a mafarkinsa. Sa ya ce: sai ya yi sammako wurin annabi (s.a.w) ya ba shi labari. Sai ya ce masa: ya ma'aikin Allah ni ina cikin bacci tsakanin bacci da farke sai wani mai zuwa ya zo mini ya nuna mini kiran salla. Ya ce: umar dan khaddabi shi ma ya taba ganin haka amma sai ya boye har kwana ishirin, sannan sai ya ba wa annabi (s.a.w) labarin hakan. sai ya ce masa: me ya sa ba ka gaya mini ba? Sai ya ce: abdullahi dan zaid ya riga ni, sai na ji kunyar in gaya maka!! Sai manzon Allah (s.a.w) ya ce: kai bilal tashi ka ga me abdullahi dan zaid zai umarce ka da shi sai ka yi shi, ya ce: sai bilal ya yi kiran salla... hadisi .
Daga Muhammad dan abdullahi dan ziyad ansari daga babansa abdullahi dan zaid, ya ce: yayin da manzon Allah (s.a.w) ya yi umarni da kararrawa da za a buga wa mutane don su taru don yin salla, sai wani mutum ya yi dawafi da ni ina bacci yana dauke da wata kararrawa a hannunsa, sai na ce masa: shin zaka sayar mini da ita? Sai ya ce: me zaka yi da shi? Sai na ce: mu kira mutane zuwa salla da shi. Sai ya ce: shin ba na gaya maka abin da ya fi wannan alheri ba? Sai na ce: na'am. Sai ya ce: ka ce: Allahu akbar, Allahu akbar, Allahu akbar, Allahu akbar, Ash hadu an la ilaha illal Lah, Ash hadu an la ilaha illal Lah, Ash hadu anna Muhammadar rasulul-Lah, Ash hadu anna Muhammadar rasulul-Lah, Hayya‘alas salah, Hayya‘alas salah, Hayya‘alal falah, Hayya‘alal falah, Allahu akbar, Allahu akbar, La ilaha illal-Lah, La ilaha illal-Lah . Sannan sai ya dan jirkita gaer ni ba da nisa ba, sai ya ce: idan kuma ka tashi zaka yi salla sai ka ce: Allahu akbar, Allahu akbar, Ash hadu an la ilaha illal Lah, Ash hadu an la ilaha illal Lah, Ash hadu anna Muhammadar rasulul-Lah, Ash hadu anna Muhammadar rasulul-Lah, Hayya‘alas salah, Hayya‘alas salah, Hayya‘alal falah, Hayya‘alal falah, Kad kamatis salah, Kad kamatis salah, Allahu akbar, Allahu akbar, La ilaha illal-Lah, La ilaha illal-Lah. Ya ce: da safe sai na zo wa manzon Allah (s.a.w) na ba shi labarin abin da na gani, sai ya ce: wannan shi ne mafarkin gaskiya in Allah ya so, tashi tare da bilal ka karanta masa abin da ka gani sai ya yi mana kiran salla da shi, domin ya fi ka dadin sauti, sai na tashi tare da bilal ina gaya masa shi kuma yana kiran salla da shi. Ya ce: sai umar dan khaddabi ya ji wannan yana gidansa sai ya fita yana jin mayafinsa yana cewa: na rantse da wanda ya aiko ka da gaskiya ya ma'aikin Allah ni ma na ga irin wannan… hadisi .
Maliku dan anas ya takaita shi cikin abin da ya zo cikin babin kiran salla a muwattarsa, ya karbo daga yahaya dan sa'id ya ce: manzon Allah (s.a.w) ya so ya riki wasu kwatakaye guda biyu  da zai rika buga su don mutane su taru don yin salla, sai aka nuna wa abdullahi dan zaid al'ansari daga banil haris dan khazraj da kwatakaye biyu a bacci, sai ya ce: wadannan sun yi kama da kwatakaye biyu irin wanda manzon Allah  (s.a.w) yake son ya rika domin mutane su rika taruwa don yin salla, sai aka ce mini shin ba ka yi kiran salla ba? Sai ya jiyar da shi kiran salla, sai ya zo wa manzon Allah (s.a.w) yayin da ya tashi daga bacci ya gaya masa hakan, sai manzon Allah (s.a.w) ya yi umarni da yin kiran salla .
Imam ibn abdul barr yana cewa: wannan kissar ta abdullahi dan zaid akwai wasu mutane daga sahabbai da suak ruwaito ta da lafuzza mabambanta, da ma'anoni makusanta, da ma'anoni masu kama da juna, da sanadodi masu tawaturanci da suke nuna suna da kyau ta wata fuska .
Na ce: akwai abubuwan da zamu duba don tabbatar da wadannan hadisai:
Na daya: annabi (s.a.w) ba yana bawa mutane umarni ne cikin shar’anta dokokin musulunci ba, abin da yake yi shi ne bin wahayin da aka yi masa ne. ba ya magana da son rai. Sai dai wahayi ne da aka yi masa. Mai tsananin karfi ne ya sanar da shi. Najmi: 3 – 5. Haka nan annabawa baki daya ba sa bayar da umarni sai da abin da aka yi musu wahayin sa, fadin Allah madaukaki: ba sa rigon sa fa magana, kuma su masu aiki ne da umarninsa. Anbiya: 26 – 27. Kuma fadinsa madaukaki ya wadatar da mu game da bawansa cikon manzanninsa da fadinsa: ka ce ni ina bin abin da aka yi mini wahayi ne daga ubangijina, wannan haskaka ne daga ubangijinku da shirya da rahama ga mutane da suke yin imani. A’araf: 203. Da fadinsa: ka ce ba zai yiwa ba in canja shi da kaina, ina bin abin daaka yi mini wahayi ne kawai, kuma ni ina jin tsoron azabar rana mai grima didan na saba wa ubangijina. Yunsu: 15. Ka ce ba ni ne farkon manznni ba, kuma ban san me za a yi da ku ba, ko da ni, kuma ni kawai ai gargadi ne mabayyani. Ahkaf: 9. Kuam ya hana annabinsa gaggautawa ko da kuma da harshe ne yayin da ya ce: kada ka gaggauta harshen ka da shi. Mu ne masu tara shi da karanta shi. Idan mun karanta shi sai ka bi karatunsa. Sannan bayaninsa yana kanmu. Kiyama: 16 – 19. Kuma ya yabi annabinsa (s.a.w) da fadinsa: shi zance ne na manzo mai girma. Kuma shi ba maganar mawaki ba ne, sai dai kadan ne kuke imani. Kuma ba maganar boka ba ce, sai dai kadan ne kuke tunatuwa. Saukarwa ne daga ubangijin talikai. Hakka: 40 – 43. Shi maganar manzo ne mai grima. Mai karfi mai daraja gun mai al’arshi. Abin bi ne a can amintacce. Kuma ma’abocinku ba mahaukaci ba ne. takwir: 19 – 22.
Na biyu: shurar da aka fada a wannan hadisai na kiran salla wata aba ce da hankali yake musun ta ko la’akari da ita a cikin shari’ar Allah, hankali yana ganin mustahili ne wannan ya faru daga manzon Allah (s.a.w), domin wanan yana daga cikin fadin magana ga Allah. Allah yana cewa: kuma da ya yi mana kagen wasu maganganu. Da mun rike shi da (azaba da) dama sannan da mun yanke masa laka. Kuma babu wani daga cikinku da ya isa ya kange shi. Hakka: 44 – 48.
Na’am manzon Allah (s.a.w) ya kasance yana saba wa sahabbansa da yin shawara da su a cikin lamurran duniya, kamar haduwa da makiyi, da matakan yaki, da sauran ayyuka da fadinsa madaukaki: ka yi shawar da su, idan ka yi niyya sai ka dogara ga Allah. Aali imaran: 159. A irin wannan ya halatta ya saba musu da shawara da su tare da yana wadatuwa daga ra’ayoyinsu, sai da shari’ar Allah ita babu wani abu da za a bi sai wahayi a cikinta.
Na uku: wadannan ruwayoyi sun nuna yadda annabi (s.a.w) ya samu dimuwa bai san me zai yi ba, wannan kuwa bai halatta ga irinsa ba da dukkan wanda yake da alakar wahayi da Allah madaukaki, har mai ya kai ga kunci da neman shawarar mutane, har ya ki kararrawa da farko sannan sai ya yi umarni da yin ta bayan ya ki ta, sannan kuam bayan ya yi umarni da shi sai ya fasa saboda wani mafarki da abdullahi dan zaid ya gani, kuam fasa yin aiki da kararrawa ya kasance kafin zuwan lokacin yin aiki da ita ne, wannan kuwa duk yana daga abin da ba zai yiwu ba ga Allah da manzonsa, wanda yake masaukar mala’iku, da wahayinsa , kuma shugaban annabawansa cikon manzanninsa.
Hada da cewa wannan mafarkin babu wani abu da ake gina shari’a a kansa a addinin Allah da ittifakin al’umma.
Na hudu: wannan hadisin yana da karo da juna a taskaninsu da abin da zai sanya faduwarsu gaba daya, musamman hadisan da aka kawo daga abu umair dan anas daga wata ammarsa ‘yar madina. Da kuma hadisin Muhammad dan abdullahi dan zaid daga babansa – sai ka kula sosai da duba da karo da ya yi da mafarkin umar a zahiri.
Haka nan kuma wadannan hadisai biyu da aka yi nuni da su sunn takaita ga dan zai da dan khaddabi ne, sai dai hadisin mafarki na dabrani a littafin ausad ya bayyana cewa wannan mafarkin daga abubakar ne kuma, sannan akwai hadisai masu yawa da suka nuna wannan mafarkin cewa mutum goma sha hudu ne daga sahabbai kowanne shi ne ya gani kamar yadda ya zo a sharhin tambih na jubaili; ya ruwaito cewa masu ganin wannan mafarkin su goma sha bakwai ne daga mutanen madina kawai, kuma umar ne kawai daga muhajirai, a wata ruwayar kuma bilal yana daga wadanda suak ga wannan mafarkin da suarna karo da juna masu yawa a ruwayoyin da suke da ban mamaki, kuma ya  yi kokarin hada su sai ya rushe aikinsa .
Idan ya tashi yana hada taro da bai hadu ba
Daga gare su yana dora karayar da ba ta karye ba
Na biyar: buhari da muslim, sun jefar da wannan mafarkin wani lokaci ba su akwo shi ba, ba daga dan zaid ba, ba daga umar ba, ba daga waninsu ba, wannan kuwa saboda rashin tabbatar wanna gun su. Sai dai sun fitar da shi a fakron fara kiran salla daga dan uamr. Sai ya ce: musulmi sun kasance yayin da suka zo madina suna haduwa su yi salla ne, kuma ba mai yin kira da ita, sai suka yi magana kan haka wata rana, sai wa su suka ce mu dauki kararrawar kiristoci, wasu kuams uak ce akwai kahon yahudawa. Sai uamr ya ce: shin ba kwa aika wani mutum ya yi shelar salla ba, sai manzon Allah (s.a.w) ya ce: ya bilal ta shi ka yi shelar salla, sai ya yi shelar salla.
Wannan kuwa shi ne abin da ya shafi kiran salla da shar’anta shi, kuma buhari da muslim sun yi ittifaki kansa, kamar yadda suka yi ittifaki wurin wurga da wanin hakan, kuma abin da suka kawo ya yi karo da hadisan duka baki daya, domin wannan hadisin yana nuna cewa fara kiran salla ya faru da shawarar umar ne ba da mafarkinsa ba, ba kuma da mafarkin abdullahi dan zaid ba ko da mafarkin waninsu. Su kuma wadancan ruwayoyin suna nuan cewa rara kiran salla da ikama ya kasance skamakon mafarki ne da abdullahi dan zaid da umar dan khaddab suka yi, don haka a gun su ake ce masa mai mafarkin kiran salla, ko suke ce masa ma’abocin kiran salla.
Kuma a cikin hadisin shaihaini akwai bayani a fili cewa annabi ya umarci bilal da yin kiran salla a majalisin yin shawara ne, kuam umar yana wurin yayin daaka bayar da umarnin, amam wadancan hadisai su kuam suan nuan cewa ya umarci bilal da yin kiran salla ne da asuba yayin da dan zaid ya ba shi labarin wannan lamarin, wannan kuwa bayan shura ne da dare daya mafi karancin abin da za a iya sauwarawa ke nan, kuma umar ba ya wurin, sai dai ya ji kiran salla ne yana gidansa sai ya fito yana jan mayafinsa yana cewa: na rantse da wanda ya haiku ka da gaskiya ya ma’aikin Allah ni ma na ga misalin abin da ya gani.
Gaya mini gaskiya shin zai yiwu a hada wannan ruwayar da wadancan? Ba zai yiwu ba, kuam ya kamata a samu adalci da gaskiya a nan.
Hada da cewa hatta da hakim ya yi wurgi da hadisan mafarkin kiran salla da ikama ba kawo su a cikin littafinsa ba kamar yadda shaihaini suka yi watsi da su gefe, wannan yana daga abin da yake yi maka nuni da rashin ingancin su, domin hakim ya yi alkawarin fitar da duk wani hadisi ne da ya inganta bisa sharadin shaihaini (buhari da muslim) amma ba su kawo shi ba ne, kuma ya yi kokari matuka ya fitar da dukkan wannan. Kuma d da yake bai fitar da wadancan ruwayoyin ba, sai muka san cewa ya yi haka ne saboda rashin ingancinsu gun shaihaini.
Kuma akwai wata magana da ya yi da take nuna bacin wadancan ruwayoyin yayin da yake cewa: shaihaini sun bar hadisin abdullahi dan zaid ne da mafarkin da ya yi, saboda gabatuwar mutuwar abdullhi wannan kafin wannan lokacin.
Wannan ne kuwa lafazin hakim da kansa.
Kuma abin da yake karfafa hakan shi ne fara kiran salla gun jamhurin malami ya fara ne bayan yakin uhud. Ga shi kuwa abu na’im ya kawo a tarhin umar dan abdul’aziz a littafinsa na hilyatul auliya da sanadi sahihi daga abdullahi umairi ya ce: na shiga wurin ‘yar abdullahi danzaid dan sa’alaba gun umar dan abdul’aziz sai ta ce masa: ni ce ‘yar abdullahi dan zaid, babana ya halacci badar, an kashe shi a uhud. Sai ya ce mata: tambayi abin da kike so, sai ya ba ta.
Da abdullahi dan zaid ya ga kiran salla da ‘yarsa ta kawo wannan lamarin (saboda girman sa), kamar yadda ta kaow zuwansa badar da uhud.
Na shida: Allah madaukaki ya yi gargadi ga wadanda suak yi imani da kada su shiga bagan Allah da maznonsa ko su daga sauti kan sautinsa, ko su bayyana masa magana kamar yadda suke yi wa sauran, da cewa wannan zai iya shafe ayyukan su idan suak yi hakan. yana fada madaukaki: ya ku wadanda kuka yi imani kada ku gabata gaban Allah da manzonsa ku ji tsoron alah, hakika Allah mai ji ne masani. Ya ku wadanda kuka yi imani kada ku daga sautinku kan sautin annabi ko ku bayyana masa magana kamar yadda kuke gayyana wa sashenku , sai ayyukanku su rushe ku ba ku sani ba. Hujurat: 1 -2.
Asalin saukarta ya kasance ne yayin da wasu jama’a daga banu tamim suak zo wurin annabi (s.a.w) suna tambayarsa ya sanya musu wani jagora, sai abubakar ya ce (kamar yadda ya zo a buhari a tafsirin surar hujurat, j 3, s 127) ya ma’aikin Allah (s.a.w) ka sanya musu ka’ka’u dan ma’abad bayan ya kawo ra’ayinsa kan hakan, sai umar ya yi maza ya ce: ka sanya musu akra’ dan habas dan’uwan banu mujashi’ ya ma’aikin Allah, sai abubakar ya ce: ba komai kake nufi ba sai saba mini. Sai suak yi jayayya da husuma, sautinsu ya daga kan haka, sai Allah ya saukar da aya yana mai sukan gaggauta fadin ra’ayi kan ra’ayin annabi (s.a.w) ko daga murya gun sa.
Sai Allah ya yi wa muminai baki daya magana kan wannan doka da za su kiyaye game da ladabinsu da halayen su tare da manzon Allah (s.a.w), wannan kuwa duka ayoyin sun hana duk wani mumin da wata mumna shiga gaban manzon Allah (s.a.w) don yin wani , wato kada k bayar da ra’ayi da fatawa har sai Allah ya yi hukunci ta harshin annabinsa da abin daya so, don haka masu bayar da shawara kan addini suna shiga gaban Allah da manzonsa ne, sai alah ya fadakar da mumain wannan kuskure ya tsayar da su gun haddinsu.
Sai kuma ya hana daga murya da yake nuna cewa suna da wani abu kan maganar annabi (s.a.w), sai ya han su wannan, don haka su daukar wani matsayi ga kansu ko wani cancantar yin haka, sannan kuma ya tsoratar da su kada su rushe ayyukansu.
Wanda duk ya san cewa Allah bai yarda da abin da abubakar da uamr suak yi ba na gabatar kansu gaban Allah da manzonsa kan jagorantar da wani mutum kan mutanensa to ya san cewa Allah da manzonsa ba sa tattabar da wani a kan ya ba su shawara kan shar’antawa, da tsara dokokinsa, da mutanenmu suna fahimta.
Na bakwai: kiran salla da ikama suan daga asasin sallolin farilla ne, mafara su ita ce mafarar farillai, duk wani masalni da lafuzz da ma’anoni da usulubinsu ya san wannan suan daga sha’ir na Allah da wannan al’ummar musulmi suka kebanta da shi da fifita kan sauran addinai, masu lura su lura da lafuzzansu da balaga da fasahar maganar da suka kunsa, da daukakarsu da shelanta Kalmar gaskiya da suka kunsa a cikinsku.
Kiran salla:
Allahu akbar, Allahu akbar, Allahu akbar, Allahu akbar, Ash hadu an la ilaha illal Lah, Ash hadu an la ilaha illal Lah, Ash hadu anna Muhammadar rasulul-Lah, Ash hadu anna Muhammadar rasulul-Lah, Hayya‘alas salah, Hayya‘alas salah, Hayya‘alal falah, Hayya‘alal falah, Hayya‘ala khairil ‘amal, Hayya‘ala khairil ‘amal, Allahu akbar, Allahu akbar, La ilaha illal-Lah, La ilaha illal-Lah.

Ikama:
Allahu akbar, Allahu akbar, Ash hadu an la ilaha illal Lah, Ash hadu an la ilaha illal Lah, Ash hadu anna Muhammadar rasulul-Lah, Ash hadu anna Muhammadar rasulul-Lah, Hayya‘alas salah, Hayya‘alas salah, Hayya‘alal falah, Hayya‘alal falah, Kad kamatis salah, Kad kamatis salah, Hayya‘ala khairil ‘amal, Hayya‘ala khairil ‘amal, Allahu akbar, Allahu akbar, La ilaha illal-Lah, La ilaha illal-Lah.
Kiran salla da ikama suna da lafuzza kamar ana kiran mutum zuwa ga rayuwa baki dayanta, kamar mutum zai gaggauta zuwa ga duniyar gaibi daga zaran ya ji wadannan lafuzzan. Kira ne da amsawa ce da sama take haduwa da kasa. Wannan shi ne kiran da musulmi suka amfani da shi don zuwa salla, wanan shi ne rayayyen kira zuwa ga dawwama.
Duba kiran salla da ikama da sannu zai bayyana gare ka cewa da mutane sun hadu da ba zasu iya zuwa da kamarsa ba.
Ta takwas: ruwayoyin da suka kawo a farkon kiran salla da ikama duk suna saba wa da abin da ya zo daga Ahlul Baiti (a.s), kuma wurinmu abin da ya saba musu ba shi da wata kima.
Ka koma wa kiran salla da ikama daga littafin wasa’ilus shi’a ila ahkamis shari’a, da sanadinsa daga Imam Ja'afar (a.s) ya ce: yayin da jibril ya sauka gun manzon Allah (s.a.w) da kiran salla, sai jibril ya yi kiran salla ya yi ikama, sai manzon Allah (s.a.w) ya umarci Ali (a.s) ya kira masa bilal, sai manzon Allah ya koya masa kiran salla ya umarce shi da shi. Wannan shi ne abin da kulain ya ruwaito, da saduk muhamad bin Ali bin babawaihi kummi da sheikh Muhammad bin Hasan tusi. Da muhamamd bn makki a zikra, cewa Imam Sadik (a.s) ya zargi wasu mutane da suak dauka cewa annabi (s.a.w) ya karbi kiran salla daga abdullahi dan zaid ne. ya ce: Wahayi yana sauka kan annabinku kuna dauka cewa ya karbo shi daga dan zaid ne.
Daga abul’ala -kamar yadda ya zo a sirar halbiyya- ya ce: na ce da Muhammad dan hanafiyya: mu muna magana game da faruwar kiran salla shin wani mafarki ne da wani mutumin madina ya gani a baccinsa, sai ya ce: sai Muhammad ya ji takaici mai tsanani saboda wannan maganar. Ya ce: kun  samu wani asasi daga addininku sai kuka raya cewa wani mtumin madina ne ya gani a baccinsa, kuan daukar karya da kage. Sai na ce masa: maganar ta yadu cikin mutane. Sai ya ce: wallahi karya ce.
Daga sufyan bn lail ya ce: yayin da abin da ya kasance ga Hasan dan Ali ya faru, sai na zo wurinsa a madina. Ya ce: sai suka rika maganar kiran salla gun sa, sai wasu suka ce ai mafarki ne da abdullahi dan zaid ya gani, sai Hasan dan Ali (a.s) ya ce masa: sha’anin kiran salla ya fi haka girma, jibril ne ya yi kiran salla biyu biyu a sama, kuam ya sanar da manzon Allah (s.a.w), an sanar da shi kiran salla ranar da aka yi isra’I da shi, aka wajabta salla .
Daga haruna dan sa’id dan shahid zai dan Imam Ali dan Husain daga iyayensa (a.s) daga Ali (a.s) : manzon Allah (s.a.w) an sanar da shi kiran salla daren da aka yi isra’I da shi ne, kuma aka wajabta salla gare shi .

Daga ciki, saryar da hayya ala khairul amal daga kiran salla da ikama
Hayya ala khairul amal  ya kasance wani bangare daga krian salla da ikama tun lokacin manzon Allah (s.a.w), sai dai a farkon lamari na lokacin halifa na biyu sun kasance suna kwadayin mutane su fahimci cewa yaki shi ne ya fi kowane aiki daraja don su tunkudu zuwa gare shi, sai suka sanya himmar su kansa, sai suka ga kran salla da wannan lafazin na hayya ala khairul amal yana kore wannan hadafin nasu.
Sai suka ji tsoron idan aka bar shi a kiran salla da ikama ka da ya sanya su jin nauyin fita yaki, domin da mutane sun san cewa hayya ala khairul amal da abin da ta kunsa, to da sun takaitu da yin salla don neman ladanta, sai su kawar da kai daga fita yaki.
Sai himmar su ta kasance a wannan lokacin shi ne su yada musulunci, da bude gabas da yamma.
Bude garuruwa kuwa ba ya kasancewa sai da karfafa rundunoni da fadawa cikin sadaukar da kai, ta yadda zasu kutsa cikin yaki su yi imani da shi a matsayin aikin da ya fi kowanne.
Don haka sai suka ga ya fi kawai su kawar da wannan lafazin na hayya ala khairul amal daga kiran salla da ikama. Sai halifa na biyu ya fada yana kan mimbari cewa: (kamar yadda kushji daga manyan masana kalam na ash’arawa ya kawo a karshen bahasin imama na littafinsa sharhut tajrid, cewa: umar ya ce): abubuwa uku sun kasance a lokacin manzon Allah (s.a.w) kuma ni ina hana su, ina haramta su, ina yin ukuba a kan yin su: mutu’ar mata, mutu’ar hajji, da fadin; hayya ala khairul amal .  
Kuma da yawan wadanda suka zo bayansa na musulmi sai suka bi shi a kan wannan haramcin in ban da Ahlul Baiti (a.s) da mabiya ra’ayinsu kamar yadda yake a mazhabinsu, har ma shahidin Fakh Husain dan Ali dan Hasan dan Hasan (a.s) dan Ali (a.s) yayin da ya bayyana a madina a lokacin alhadi daga sarakunan abbasawa sai ya yi umarni da a yi kiran salla, sai aka yi. Kamar yadda abul faraj al’asfahani ya kawo a littafinsa na makatilul dalibin .
Allama halbi ya kawo a babin kiran salla da shar’anta shi a juzu’I na biyu a sairarsa; cewa ibn umar da Imam zainul abiding (a.s) sun kasance suna fada a kiran sallarsu bayan fadin hayya alal falah, suna cewa; hayya ala khairul amal.
Wannan ya zo mutawatiri daga imaman Ahlul Baiti (a.s), sai ka koma wa ruwayoyinsu, da malamai mabiyansu, don samu bayanin ra’ayoyinsu.

Fasali:
Jumlolin kiran salla a gun mu su goma sha takwas ne kamar haka: Allahu akbar, Allahu akbar, Allahu akbar, Allahu akbar, Ash hadu an la ilaha illal Lah, Ash hadu an la ilaha illal Lah, Ash hadu anna Muhammadar rasulul-Lah, Ash hadu anna Muhammadar rasulul-Lah, Hayya‘alas salah, Hayya‘alas salah, Hayya‘alal falah, Hayya‘alal falah, Hayya‘ala khairil ‘amal, Hayya‘ala khairil ‘amal, Allahu akbar, Allahu akbar, La ilaha illal-Lah, La ilaha illal-Lah.
Jumlolin ikama kuwa a gun mu su goma sha bakwai ne kamar haka: Allahu akbar, Allahu akbar, Ash hadu an la ilaha illal Lah, Ash hadu an la ilaha illal Lah, Ash hadu anna Muhammadar rasulul-Lah, Ash hadu anna Muhammadar rasulul-Lah, Hayya‘alas salah, Hayya‘alas salah, Hayya‘alal falah, Hayya‘alal falah, Kad kamatis salah, Kad kamatis salah, Hayya‘ala khairil ‘amal, Hayya‘ala khairil ‘amal, Allahu akbar, Allahu akbar, La ilaha illal-Lah, La ilaha illal-Lah.
Kuma ana son yin salati ga manzon Allah (s.a.w) bayan ambatonsa (s.a.w) kamar yadda ana son sheda ga Ali (a.s) da wilaya baya kammala sheda biyu, a kiran salla da ikama.
Duk wanda ya haramta wannan ya yi kuskure, ko ya ce: bidi’a ce, domin duk mai kiran salla yana gabatar da ita da wata kalma da yake hade da ta fadin Allah: kuma ka ce godiya ta tabbata ga Allah da bai riki da ba. Isra’: 111. Ko wata kalma kamar fadin assalatu wassalamu alaika ya rasulallah!, alhalin wannan duk bai zo a kiran salla ba. Wannan bai zo a kiran salla ba ko ikama, kuma ba bidi’a ba ne, ba haram ba ne, haka nan ma yin shaida ga Ali (a.s) bayan shahadatain suna da dalilai na musamman.
Hada da cewa yin wanta magana maras yawa daga mutane a tsakiyar kiran salla ba ta da wata matsala, ba ta bata kiran salla ko ikama. To ta ina wannan bidi’ar ta zo ko haramcin? Me ye hadafin bata tsakanin musulmi a wannan zamanin!.

Daga ciki, saki uku da abin da suka farar a cikinsa bayan annabi (s.a.w)
Sanannen lamarin shi ne wacce aka saka (saki uku) ba ta halatta ga wanda ya sake ta sai bayan an samu wani aure na shari’a tsakani, wannan kuwa shi ne saki uku kamar haka; ya kasance an rigaye shi da komawa biyu bayan saki biyu, wannan kuwa kamar haka yake: na farko ya sake ta sai ya dawo da ita, sannan sai ya sake sakin ta na biyu sai ya sake dawo da  ita, sannan sai ya sake sakin ta na uku, to a nan ba ya halatta ya dawo da ita sai da auren wani mutum da saki daga gare shi, wannan shi ne saki ukun da ba ya halatta mace ta dawo sai da auren wani mutum daban wanin mijinta, da wannan ne Allah ya saukar da aya a fadinsa madaukaki: “Saki sau biyu ne, ko dai kamewa da kyakkyawa, ko saki da kyautatawa…(har zuwa fadinsa) … idan ya sake ta to ba ta halatta gare shi kuma sai ta auri wani mutum daban”. Bakara: 229 – 230.
Duba abin da malaman larabci da tafsiri suka fada a ann, da lafazin zamakhsahri a littafinsa na Kusshaf  yana mai cewa: saki yana nufin a bar abu a kyale shi, amma saki biyu ko sama da hakan a nan yana nufin a saki a bar abu sannan sai a dawo da shi, sannan sai a sake sakin, wannan kuwa ba ya kasancewa a lokaciguda sai dai maimaitawa kamar fadin Allah ne “Sannan ka sake duba sau biyu…”. Har dai yayin da ya fada game da fadin Allah madaukaki cewa: “ko dai kamewa (wato rike mace) bisa kyakkyawa, ko kuma saki da kyautatawa” Bakara: 229. Sai ya ba su zabi -bayan ya sanar da su yadda zasu yi saki- ko dai su rike matan da kyakkyawan zaman tare da tsayuwa da ayyukan wajibi da suke kan su, ko kuma su sake su saki kyakkyawa gare su. An ce saki biyu wato wani bayan wani ke nan domin babu komawa bayan na uku… har zuwa inda ya ce: “idan ya sake ta” bakara: 230. Wannan sakin da aka fada da maimaitawa ke nan a fadinsa cewa: “saki guda biyu ne” bakara: 229, idan ya gama da ita sai ya sake ta saki na uku bayan wannan guda biyun “to ba ta halatta gare shi bayan nan” bakara: 230, wato bayan wannan sakin “har sai ta auri wani namijin daban” bakara: 230.
Na ce: wannan shi ne ma’anar wannan ayar, kuma shi ne abin da yake cikin tunanin masu ilimi da mafassara baki daya, kuma ba zai yiwu fadinsa madaukaki “idan ya sake ta ba ta halatta gare shi ke nan kuma” ya kasance kamar fadin mai fadi cewa: na sake ki saki uku. Sai dai idan wannan sakin ya kasance guda biyu da kuma komarwa guda biyu a tsakaninsu, kamar yadda yake a fili.
Sai dai umar ya ga yadda mazaje suke wasa da saki suna fainsa na sake ki saki uku da kalma daya, sai ya dora musu abin da suke cewa a kansu don ya yi musu ukuba ko ladabtarwa, kuma tarihohi sun zo da wannan magana a fili daga abin da ya farar.
Abin da ya zo daga Dawus daga abun sahba’ ya ce da ibn abbas: shin fadin saki uku bai kasance daya ba a lokacin manzon Allah (s.a.w) da abubakar? Sai ya ce: haka ne ya kasance, yayin da umar ya zo sai mutane suka rika wasa da kalamr saki sai ya dora musu shi a kansu. Muslim ya zo da shi a littafinsa .
Haka nan ya zo daga ibn abbas ta hanyoyi masu ywa kuma dukkansu ingantattu ne, ya ce: sak a lokacin manzon Allah (s.a.w) da abubakar da kuam farkon shekaru biyu na halifancin umar ya kasance Kalmar saki uku a Kalma daya saki daya. Sai umar dan khaddabi ya ce: mutane sun kasance suna gaggauta wannan lamari da suka nace masa, to mu zamu zartar da shi a kansu, sai ya zartar da shi kansu. Musulim a littafinsa .
Haka nan Hakim ya kawo shi a mustadrak din sa yana mai shelanta ingancinsa bisa sharadin shaihaini . kamar yadda zahabi ma ya kawo shi a talkhisin mustadrak yana mai kawo ingancin wannan magana bisa sharadin buhari da muslim  kuam.
Ahmad dan hambal ya fitar da shi daga masnadinsa . Kuma yadda da yawa daga masanid da sunan daban-daban sun kawo .
Haka nan allama Rashid rida ya kawo a littainsa “almanar” a mujalladi na hudu a shafi na 210, daga abu dawud, da nisa’I, da hakim, da baihaki, sannan sai ya ce: daga abin da ya zo na yin hukunci sabanin annabi akwai abin da baihaki ya kawo daga ibn abbas ya ce: rukana ya sake matarsa sau uku a majalisi daya, sai ya yi bakin ciki mai tsanani kan hakan, sai manzon Allah (s.a.w) ya tambaye shi yaya ka sake ta? Sai ya ce: sau uku. Sai annabi (s.a.w) ya ce: a majalisi daya? Sia ya ce: haka ne. sia annabi (s.a.w) ya ce: wannan ai daya ne, ka mayar da ita idan ka so.
Nisa’I ya fitar daga ruwayar makharama cewa daba bukair daga babansa da mahmudu dan lubaid cewa manzon Allah (s.a.w) an ba shi labarin wani mutum da ya skai matarsa saki uku a zama daya baki daya, sai ya tashi ya  fusata ya ce: yanzu ana wasa da littafin Allah tun ina cikinku! Sai wani mutum ya tashi ya ce: ya ma’akin Allah ba ma kashe shi ba?   (har zuwa karshen abin da ya kawo na abin da ya zo a sunan Nisa’I, don haka ne ma malaman musulunci idan suna magana kan wannan lamarin sukan kawo shi kai tsayi domin an sallama da faruwarsa baki daya.
Haka nan babban malami Khalid Muhammad Khalid almisri ya kawo yana mai fada a littafinsa na Demokradiyya cewa: umar ya bar nassin shari’a mai tsakri na kur’ani da sunna lokacin da ya ga maslahar yin hakan. Yayin da musulunci lokacin ma’aikin Allah (s.a.w) da abubakar yake ba wa wadanda ake lallashin zukatansu wani abu sai umar ya zo ya hana ya ce; ba abin da zamu ba su. Yayin da manzon Allah da abubuakar suke halatta sayar da ummul walad (baiwar mutum da ta haihu da shi), sai umar ya hana wannan. Yayin da musulunci yake ganin saki uku a kalma daya saki daya ne a ittifakin sunna da ittifakin al’umma, sai umar ya rusa wannan ittifakin ya mayar da shi saki uku ne, sia ya bar sunna, ya rusa ijma’in. Demokradiyya: shafi 150.
Haka nan ustaz dakta Dawalibi ya kawo a littafinsa na Usulul fikhu  game da wannan lamarin na saki uku cikin kalma daya, ya ce: daga cikin abin da umar ya farar da shi cikin addini don karffa ka’idar nan ta canjawar zamani da halaye shi ne zartar da saki uku cikin kalma guda, tare da cewa mai saki idan ya kawo shi guda a kalma daya tun lokacin manzon (s.a.w) da abubuakar da farkon halifancin umar ana lissafa shi daya ne kamar yadda ya tabbata a sunna sahihiya daga ibn abbas cewa, sia umar ya ce: mutane sun gaggauta wa wannan lamarin sai ya zartar da maganarsu a kansu.
(Ustaz Dakta Dawalibi ya ce:) Ibn kayyim jauziyya yana cewa: sai dai sarkin muminai umar ya ga mutane sun dage kan wannan lamarin suna wasa da lamarin saki, kuma suka yawaita shi da kalma daya, sai ya ga maslaha shi ne ya yi musu ukuba da zartar da shi, idan suka san haka sai su Diana wasa da saki, sai umar ya ga wannan maslahar a zamaninsa, ya ga abin da yake kan sa na lokaicn annabi da abubukar da wani bangare na halifancinsa, sai ya ga hakan ya fi dacewa da su idan ba su kiyaye ba, kuma sun kasance ba sa jin tsoron Allah kan saki.
Har zuwa inda (Ustaz Dakta Dawalibi) yake cewa: wannan yana daga abin da fatawa take kawowa na canjawa da canjawar zamani . Ya ce: sahabbai sun san siyasar umar, da yadda yake ladabtar da al’ummarsa, sai suka bi shi a kan abin da ya dora masu shi , suka gaya wa wanda ya tambaye su kan hakan . Sai dai shi kansa ibn kayyim ya zo da kansa sai ya kawo wata magana game da bin da ya fada da kwadayin ko za a koma kan abin yake a lokacin manzon Allah (s.a.w) don lokaci ya sake canjawa kuma, saki uku cikin kalma daya kuma ya kasance ya rufe kofar komawa ga hala din da aka toshe kofarta tun lokacin sahabbai , ya ce: idan ukuba ta kai ga fasadin da ya wuce na wanda ake yi wa ukuba, to barin ta ya fi soyuwa zuwa ga Allah da manzonsa .
(Ustaz Dakta Dawalibi ya ce:) Ibn taimiyya ya ce:  da umar ya ga wasan da musulmi suke yi wurin halatta wacce ta nesanta daga mijnta don ta koma masa da ya mayar da lamarin kamar yadda yake a lokacin manzon Allah (s.a.w).
(Ustaz Dakta Dawalibi ya ce:) abin da ibn kayyim da ibn taimiyya suka kawo an abin la’akari cikin wannan lamarin yana sanya lallai ne hukumar misira ta dawo da shi kan abin da yake a lokacin manzon Allah (s.a.w) don aiki da ka’idar nan ta canjawar hukunci saboda canjawar zamani .

Daga ciki, akwai sallar tarawihi (asham)
Sallar asham manzon Allah (s.a.w) bai zo da ita ba, haka ma ba ta kasance lokacin abubakar ba, Allah bai halatta yin jam’I don wata salla ba ta nafila ko wata sunnan in ban da sallar rokon ruwa.
Abin da ya shar’anta jam’I a cikinsa shi ne sallar wajibi ta yau da gobe, da sallar dawafi, da sallar idi biyu, da ta ayoyi (kamar kisfewa), da janaza.
Manzon Allah (s.a.w) ya kasance yana tsayar da sallar daren sa ba tare da jam’I ba, kuma yana kwadaitar da mutane su yi, su ma suna yi kamar yadda suka ga manzon Allah  (s.a.w) yana yi.
Haka nan lamarin ya kasance a lokacin abubakar har sai da ya wuce a shekara ta 13 bayan hijira , umar ya karbi jagoranci bayansa, sia ya yi azumin shekarar farko ba tare da ya canja komai ba, yayin da watan azumin shekara ta goma sha hudu ya zo sia ya zo masallaci a tare da shi akwai wasu sahabbansa, sai ya ga mutane suna yin nafilfili, daga mai tsayuwa sai mai ruku’u, da mai sujada, da mai karatu, da mai tasbihi, da mai harama da takbiri, da mai yin sallama, a wani yanayin da ya ga shi bai yi masa ba, sai ya ga bari ya gyara wannan ya canja shi, sai ya dora musu yin tarawihi (sallar asham)  a farkon daren wannan watan, ya sanya wa mutane jam’I a kan yin ta, kuma ya rubuta yin haka a dukkan garuruwa, ya sanya wa mutanen madina limamai biyu da zasu yi salla da su, limamin maza, da limamin mata. A ruwayoyi mutawatirai.
Kuma haka nan shaihaini sun kawo a littattafansu  cewa: manzon Allah (s.a.w) ya ce: wanda ya yi sallar daren watan ramadhan yana mia imani da neman lada za a gafarta masa zunubinsa, kuma manzon Allah (s.a.w) ya rasu lamarin yana kan hakan ne bai canja daga abin da yake kai ba, sai sai lamarin ya kai ga halifancin abubakar da farkon halifancin umar.
Buhari ya kawo a littafin sallar tarawihi cewa; daga Abdurrahman dan abulkari’  ya ce: na fita tare da umar a daren watan azumi zuwa masallaci, sai ga mutane a rarrabe, har zuwa inda ya ce; sai umar ya ce: ni na ga in hada ku kan mai karatu daya da ya fi, sai ya yi niyya ya dora su kan ubayyu dan ka’abu. Ya ce: sanan sai na fita tare da umar wata rana mutane suna salla da limancin mai karatunsu, sia umar ya ce: madalla da wannan bidi’a.
Allama kasdalani ya kawo a farkon shafi na hudu na juzu’I na biyar na irshadus sari a sharhin sahihul buhari yayin da ya kai ga fadin umar a wannan hadisin: madalla da wannan bidi’a, sai ya ce: ya kira ta bidi’a ne domin annabi (s.a.w) bai sanya musu wannan haduwar ba, kuma ba ta kasance a lookacin abubakar ba, ba ta nan tun farkon dare, ko wannan adadin… zuwa karshen abin da ya kawo. Da misalinsa a cikin tuhfatul bari da sauran sharhohin buhari da aka rubuta.
Allama abul walid Muhammad dan shahnata yayin da yake kawo wafatin umar cikin abubuwan da uska faru a shekara ta 23 hijira yana cewa: shi ne farkon wanda ya hana syar da ummul walada, kuma fakron wanda ya hada mutane kan yin kabbara hudu a sallar jana’iza, shi farkon wanda ya hada mutaune kan yin limanci a sallar tarawihi.
Yayin da suyudi ya kawo wannan a littafinsa na -tarikhul khulafa- ya kawo abubuwan da umar ya farar da nakaltowa daga askari  ya ce: shi ne farkon wanda aka kira sarkin muminai, farkon wanda ya sunnanta sallar asham, farkon wanda ya haramta auren mutu’a, farkon wanda ya hada mutum kan kabbara hudu a salla janaza.
Muhammad dan sa’ad ya ce: yayin da yake kawo bayanin umar a juzu’I na uku daga littafin dabakat yana mai cewa, shi ne farkon wanda ya sanya sallar asham –yin jam’in salla a farkon dare da azumi- kuma ya rubuta umarnin yin haka zuwa garuruwa masu yawa a watan ramadhan a shekara ta sha hudu hijira, ya sanya wa mutane masu limanci biyu a madina daya yana yi wa maza, daya kuwa yana yi wa mata.
Bin abdulbar a littafinsa na al’isti’ab game da umar yana cewa: shi ne wanda ya haskaka watan azumi da yin sallar asham.
Na ce: Kamar dai wadannan suna ganin sanya yin sallar tarawihi da ya yi ya kawo wani abu ne da Allah da manzonsa suka gafala ba su kawo ba!!.
Sai suka gafala daga hikimar Allah da shari’arsa da tsarinas, rashin sanya jam’in sallar nafila yana da falala mai yawa da hikima da suka jahilta, da ga ciki akwai kebewar bawa cikin dare da ubangijinsa yana maikai kuka da bakin cikinsa zuwa gaer shi, yana mai ganawa da shi da abubuwan da suke masu muhimmanci matuka yana mai kawo su daya bayan daya hari sai yakawo karshe, yana mai nacewa yanamai tawassuli da yalwar rahamar Allah madaukaki yana mai kauna, kai fakewa, mai tsoro mai kwadayi, mai komawa mai tuba, mai furushi da laifinsa mai fakewa mai neman tsari, wanda ba ya samun wata mafaka daga Allah sai dia zuwa gare shi, kuma ba shi da wata matsera sai dai zuwa gare shi.
Don haka sai Allah ya bar sunna ba tare da wani kaidin da dabaibayin yin jam’I ba, domin mutane su samu kadaita da Allah da zukatansu, da nishadin gabobensu, wanda duk ya so ya karanta, wanda ya so ya tsawaita, wannan shi ne mafificin lamari, kamar yadda ya zo daga shugaban talikai.
Amma sanya wannan jam’in duk zai takaita wannan amfanin ne, ya karanta fa’idarsa.
Hada da cewa sanya nafila a cikin ja’ain yana hana gidaje nasu rabon albarkar da samun daukakar yin salla a cikinsu, yana hana su na su rabon na tarbiyya da tasowa a kan son su, wannan kuwa saboda samun yin koyi da aikin iyaye, da uwaye, da kakanni, da tasirinsa wurin karfafa yara da zai sanya shi kafuwa a cikin hanklansu da tunaninsu da zukatansu. Hakika abdullahi mas’ud ya tambayi manzon Allah (s.a.w) cewa me ya fi, salla a gidana ko a masallaci? sai annabi (s.a.w) ya ce: shin ba ka ganin gidana da kusancinsa da masallaci, to in yi salla a gidana ya fiye mini yin salla a masallaci, sai dai idan sallar wajibi ce. Ahmad da ibn majah, da ibn khuzaima , suka ruwaito shi a littattafansu. Haka nan ya zo a kitabut targib fi salatin nafila, daga littafin targib wat tarhib na imam zakiyyuddin abdul’azim bn abdul kawiyyu almunzari. Kuma daga zaid dan sabin cewa annabi (s.a.w) ya ce: ku yi salla ya ku mutane a gidajenku domin sallar mutum a gidansa ta fi sai dai idan sallar wajibi ce, nisa’I da ibn majah ya ruwaito shi a sahihinsa. Daga anas dan malik ya ce: manzon Allah (s.a.w) ya ce: ku girmama gidajenku da yin sallarku. Daga gareshi ya ce: misalin gidan da ake mabaton Allah a cikinsa da gidan da ba a ambaton Allah a cikinsa, kamar rayayye ne da matace. Buhari da muslim suka ruwaito shi. Daga jabir ya ce: manzon Allah sa ya ce: idan wani ya gama sallarsa, to ya sanya wa gidansa wani bangare na sallarsa, Allah zai sanya alheri a gidansa saboda sallarsa. Muslim da waninsa ne suka ruwaito shi, ibn khuzaima ma ya ruwaito shi a isnadinsa zuwa abu Sa'id. Haka ma sunan da wasu ma’anonin.
Sai dai halifa umar ya zo da nasa tsarin da aikin, kuma abin da ya kayatar da shi a sallar jam’I na nuni zuwa ga alamar daukaka ya kayatar da shi da wasu fa’idoji masu yawa da malamai suka yawaita bayanai kansu, kuma kai ka san cewa shari’ar musulunci ba ta gafala ta wannan bangaren ba, sai ta kebance shi ga wajibai daga salloli kawai, ta bar nafiloli ga wasu abubuwan na daga maslahohin daban. Kuma “bai kamata ba ga wani mumini ko wata mumina idan Allah da manzonsa suka hukunta wani lamari ya kasance suna da zabi nasu na lamarinsu” ahzab: 36.



1 next