Gabatarwar Rayuwar Ma'aurata



Gabatarwar Raywar Ma’aurata
Da sunan Allah Mai rahama Mai Jin kai
Godiya ta tabbata ga Allah madaukaki, tsira ya tabbata ga zababben halittar Allah annabi Muhammad da alayensa tsarkaka.
Kuma akwai daga ayoyinsa, ya halitta muku matan aure daga kawukanku, domin ku nutsu zuwa gareta, kuma ya sanya soyayya da rahama a tsakaninku, lalle a cikin wannan akwai ayoyi ga mutane masu yin tunani .
"Su tufafi ne gareku, kuma ku tufafi ne garesu". Bakara: 187.
Mutum halitta ne na al'umma da zaman cikin iyali wanda yake shi ne mafi karancin haduwar zaman tare, amma a lokaci guda kuma mafi zama asasin gina al'umma, wanda wannan asasin an gina shi ne da namij da mace. Sanin nauyin da ya hau kan namiji da mace, da sanin yanayi da ayyuka da alakar yadda za a zauna da juna tsakanin namiji da mace shi ne abin da yake iya karfafa dankon soyayya mai karfi da alaka tsakanin iyali.
Kuma kai mutum! Shin ka san kuwa wajibi ne a kanka ka daukaka himmarka zuwa ga Allah (s.w.t) domin kai ba a yi ka don ka damfaru da duniya mai turbaya ba, "Ina zaku ne" . Shin kuwa ka san cewa kana da wani nauyi da ya hau kanka? "Ku kare kawukanku da iyalanku daga wuta, wacce gumagumanta su ne mutane da duwatsu" .
Wannan littafin na “Rayuwar ma’aurata”  ya kunshi kananan littattafai ne guda uku da na rubuta su a takaice, sai dai sakamakon kusancin abin da suke magana a kai, sai na ga in hada su wuri daya. Littafin farko shi ne: “Mace A Al’adu Da Musulunci”. Da yake kunshe da bayanai ne game da marhaloli da mace ta kasance a ciki daga zamanin da zuwa yau a takaice, da na rubuta shi don hadafin fahimtar ni’imar da Allah (s.w.t) ya yi mana ta wannan Addini da ya aiko mafificin halitta Manzo Muhammadu (s.a.w) da shi, sa’anan kuma zai taimaka wajan sanin matakai da marhaloli na tarihi da mata suka wuce a sauran al’ummu da suka gabata, da fatan Allah ya taimaka mana ya kuma karfafi Musulunci da shi.
Fahimtar da al’umma irin ni’imar da Allah ya yi mana ta wannan Addini da yake mafi kamala da aka aiko mafificin annabawa da shi yana daga cikin manyan hadafofin kawo irin wadannan bincike. Abin da ya rage a kanmu shi ne gode wa Allah (s.w.t) ta hanyar bin Addininsa sawu da kafa da kokarin aikata duk abin da ya zo da shi ta hannun Annabinsa Muhammad (s.a.w) da wasiyyansa (a.s).
Sai kuma littafin nan da na rubuta mai suna “Auren Mace Fiye Da D'aya”  wanda ya kunshi kariya ga hukuncin musulunci da manzon rahama (s.a.w) kan abin da ya shafi auran sama da mace daya da yawaitar matan Mafificin halitta. Musulunci addini ne mai fadi da ya himmantu da warware dukkan matsalolin dan Adam, don haka ne ya kalli dukkan wani janibi na rayuwar mutane. Saboda haka ne muka yi imani da cewa babu wani abu da musulunci bai yi magana a kansa ba, kuma wannan lamarin shi ne abin da na yi imani da shi a bisa bincike game da musulunci.
Sai dai an samu takaitawar musulmi wurin ganin sun ba wa komai hakkinsa, maimakon haka sai suka himmantu da abin da ya shafi ibadoji kawai, babu bambanci tsakanin malaman musulmi a wannan fage na takaitawa. Idan mutum ya dauki littattafan musulmi na addini wadanda malamai suka rubuta babu komai sai babin ibadoji da ma'amaloli da ma'anarsa kebantacciya. Amma fagen siyasa, da zaman tare, da tattalin arziki, da tsaro, da kotu, da ayyukan dauloli, da alakokin dauloli, da siyasar dauloli, babu wani abu da zaka gani a ciki, sai ka ce musulunci bai yi magana kan wannan janibin ba.
Takaitawar da musulmi suka yi wurin bayaninsa ya sanya wasu duniyoyin suna daukarsa a matsayin addini tauyayye da ba shi da wani abin cewa a kowane fage sai na ibadoji da wasu mu'amaloli kamar aure, da ciniki, da haya, da saki, da rantsuwa, da makamancin hakan. Suna masu jahiltar iliminsa da hikimominsa masu kima da daraja, wadanda zasu iya fitar da wannan duniyar daga kangin da take ciki, yana bayar da warwara ga dukkan dan Adam a kowane fage.
Takaitawa wurin fadada magana kan siyasar hukuncin addini da hikimar da take kunshe cikinsa ya sanya hatta musulmi sun jahilci mafi yawan hikimomin hukuncin addini a kan kowane lamari. Don haka ne muka ga masu sukan musulunci suna sukan sa kan kowane fage, wani lokaci sakamakon jahiltar addinin ne, wani lokaci kuma sakamakon an samu wasu masu kiran kansu masanan musulunci suna magana da yawunsa da abin da yake ko kusa bai yi kama da koyarwarsa ba.
Rashin sanin hikimominsa ya sanya an yi masa hujumi ta ko'ina, idan muka duba masu sukan addini kan wannan lamarin da muke son magana kansa na sukan musulunci saboda yardarsa da auren mace sama da daya, ko kuma sukan da masu gaba da shi suke yi wa mafi kamalar mutum a cikin halittun Allah manzon rahama (s.a.w) Muhammad dan Abdullah (a.s). Don haka ne kafin mu ce komai kan wadannan soke-soken muke son kawo wasu bayanai game da musulunci a takaice.
Sai kuma littafi na uku wanda aka bar wa sunan wannan littafin bayan hade su wuri daya, wato “Rayuwar Ma'aurata”  wanda yake nuni da wane namiji ko wace mace ce za a zaba don zama tare, wanda yake kallon al'adun mutanenmu ne na kasar Hausa bisa yadda suke rayuwa, gwargwadon yadda zai dace da al’adun mutanenmu da bayani bisa ra’ayoyi mabanbanta, ba komai muke nema ba a nan sai neman gyara cikin wannan al'ummar tamu da ilmantarwa ko tunatarwa game da wasu muhimman bayanai da ya kamata su mayar da hankali kansu game da gyara zaman tare domin samun al'umma ta gari.
sannan ya kunshi takaitaccen bayani ne game da yadda ya kamata gida ya kasance, da siffofin ma’aurata, da kuma yadda ya kamata su kalli rayuwa, da abin da ya shafi kula da hakkin juna kamar yadda musulunci ya gindaya ba tare da ketare iyaka ba.
A musulunci an yi umarni ne da yin aure ba domin biyan bukatar duniya ko ta sha’awa ba kawai, akwai bukatar gina al’umma saliha da zata ci gaba da daukar nauyin isar da sakon Allah a duk fadin Duniya, wannan yana bukatar taimakekeniya tsakanin ma’aurata, sa’annan akwai samun nutsuwar ruhi da dan Adam yana bukatarsa wanda an sanya shi ne ya zamanto ta hanyar zamantakewa tsakanin miji da mata.
Misali mace koda ta yi ilimi, ta samu komai na wannan duniya da duk wata ni’ima, haka nan ma namiji, idan ba su da mai debe musu kewa ta fuskacin zaman auratayya to akwai wani gibi babba da ba su cike shi ba, wanda ba ya samuwa sai ta hanyar auratayya wacce Kur'ani mai girma ya yi nuni da ita , kamar yadda a zamantakewar tare tsakanin ma’aurata idan aka mayar da kauna da so suka koma kiyayya da gaba, abin yakan fi zama ba tare da mai debe kewa ba muni.
Kamar yadda haka nan ana son yin aure da wuri ga wanda ya balaga matukar ya samu yalwa, domin a cikin rashin yin hakan akwai fitina a bayan kasa da fasadi mai girma kamar yadda ya zo daga Ahlul-baiti (a.s) . Mu sani akwai kamalar da ba ta yiwuwa a san ta ko a kai zuwa gareta sai ta hanyar aure, kuma ba ta samuwa ta hanyar zaman banza da fasikanci. Irin wadannan abubuwan sun hada da: sanin ma’anar ciyarwa, yafewa, soyayya, hakuri, juriya, daukar nauyin mutane, reno, tarbiyyar ‘ya’ya, fahimtar kimar iyaye, tunanin gida da sauransu.
Ayatul-Lahi makarim shirazi yana cewa: Sau da yawa daga cikin abubuwa kamar ma’anar soyayya, da kauna, da yafewa, da kyauta, da baiwa da tausayi, da fansar rai, ma’anarsu ba ta ganuwa da fahimtuwa sai da aure, wanda ta hanyar zaman banza ba tare da aure ba da matar haram ko zaman gwauranci da rashin aure ba za a iya fahimtar hakikaninsu ba, kuma riskarsu tana yiwuwa ta hanyar zamantakewar aure ne kawai .
Muna fatan littafin ya zama mai amfani ga dan Adam a yanayin zamantakewar gida, ta yadda zai zama sanadi na gina al’umma saliha da ci gaban duniyar musulmi baki daya.
Ina rokon Allah ya bayar da ladan rubuta wannan littafi ga iyaye da dukkan bayin Allah salihai malamaina da dukkan wanda ya sanar da ni wani abu da amfaninsa ya shafi duniya da lahira.
Hafiz Muhammad Sa'id
hfazah@yahoo.com
www.hikima.org
Rabi’ul Awwl 1424 H.K
Khurdad 1382 H.SH
Mayu 2003 M