Samun TsiraSamun Tsira
Samun Tsira; hanya ce da zamu iya bi domin samun galaba a kan rundunar jahilci cikin sauki kamar yadda zamu kawo, domin duk wani ciwo yana da magani, wannan ciwon na rai ne ko na jiki. Malaman tarbiyya masana ran dan Adam kuma wasiyyan Annabi (s.a.w) daga alayensa sun sanya hanyoyin da mutum zai bi domin fita daga cikin kangin wannan cutar domin samun rai mai lafiya mai kubuta daga dukkan aibi, ta yadda rai zata zauna da nutsuwa cikin jiki mai lafiya maras aibi. Masu hikima sukan ce: Hankali -wato Rai- mai lafiya cikin jiki mai lafiya. Kamar yadda muka kawo cewa jiki shi ne fagen wannan yakin, sai dai mu sani cewa a nan jiki ba don shi ne yake samun sakamakon munana ko kyawawan halaye ba, ba kuma don cewa shi kadai ne yake fagen wannan gumurzun ba. Sai dai jiki a nan shi kansa rai tana amfani da shi ne domin samun burinta na gyaruwa ko lalacewa, don haka sai ya kasance kamar wuka ce a hannun dan fawa, ko fatanya a hannun manomi Bayan wannan gabatarwa sai mu fara da cewa duk sa'adda wani ya tashi domin maganin rundunar jahilci, ya hau kansa ya fara da sanin cewa a yanzu shi wani fage ne na wannan gumurzu, kuma ya san cewa akwai wadannan mayaka da suke karkashin kwamandoji biyu masu girma wato Hankali da Jahilci, wannan bangaren muna kiran sa "waiwaye". Bayan haka sai kuma ya yarda cewa Saken Zucinsa zai rusuna wa umarnin Hankali ba na Jahilci ba, sannan sai ya daura damarar biyayya ga umarnin Hankali, da yakar duk rundunar jahilci, wannan muna kiran sa da "azama ko himma". Sannan sai ya karfafi azamarsa da wani haske mai cewa a ransa gyara fa zai yiwu, idan ya sake a nan Saken tunani ya yi galaba a kansa ya sanya masa waswasi to ya fadi ke nan, kuma ba zai sake waiwayen hanyar gyara ba. Don haka ne a farko muka gabatar da cewa saken tunani yana da hadari matuka, domin hadarinsa bai Yawancin mutanen kasarmu sun sha kaye ne a wurin Saken tunani, ta yadda da zarar ka yi wa mutane maganar gyara sai su ga ba zai yiwu ba, a nan ne al'ummarmu ta sha kaye ta kasa ci gaba, a nan ne duk lalaci ya fada mana, har wasu suka lalace da jin cewa tun da gyara ba zai yiwu ba ni ma bari in lalace, da wannan ne zamu sake lurasshe da mutane cewa hadarin wannan bangare fa ba karami ba ne. Kafin mu sha magani sai mun yarda da wanda ya yi magana cewa amintacce ne, kuma maganinsa yana da garantin cewa idan mun sha babu wata matsala zamu samu waraka domin ya san dukkan cututtukanmu. Don haka ne kafin mu kai ga magani dole ne mu san cewa akwai Allah madaukaki wanda yake da matukar girma, kuma shi mai iko ne, sannan yana ganin mu duk abin da muke yi, kuma yana sane ba ya mantawa. Sannan shi ne ya yi mana dukkan ni'imomin da muke amfana daga garesu kamar iska, ruwa, yanayi, tufafi, hankali, fasaha, da sauransu, da mutanen duniya sun taru a kan su yi mana lumfashi daya, ko digo daya na ruwa ba zasu iya ba, da sun taru a kan su ba mu kwayar samuwa da sun kasa, to wannan ubangijin da ya yi mana wadannan ni'imomi shi ne yake son mu tashi mu yi tunani domin mu kasance kamar yadda yake so, ba kamar yadda muke so ba. Sannan a wani bangaren yana da karfin kamu mai tsanani idan mun saba, ba zamu iya gujewa azabarsa ba, don haka ne wasu ruwayoyi suka yi nuni da cewa; idan zamu iya fita daga karkashin mulkin ubangiji da ni'imominsa to sai mu saba masa, amma tun da kuwa ba zamu iya ba, babu mu babu saba masa. Don haka duk inda muka je yana nan, ba zamu iya guje masa ba, ba zamu iya tsere wa kamunsa ba, idan kuwa haka ne sai mu ji tsoronsa. Amma maganar magani da muka ce zamu kawo bayaninsa zai kasance kamar haka ne; da farkon dai akwai abin da muke cewa Sharadi, sannan sai Lura, na karshe kuwa shi ne Hisabi. Don haka bayanin namu zai kewaya ne karkashin wadannan abubuwa guda uku: Sharadi: Sharadi shi ne abu na farko kuma yana nufin cewa a kullum mutum zai duba kansa ya kuma duba girman ubangijinsa, sannan sai ya duba wadancan rundunonin Jahilci na shedan ya dauki alkawari tsakaninsa da Allah cewa ba zai aikata ko daya daga cikinsu ba saboda muninsu, don haka ba zai aikata koda mummuna daya ba. Sannan sai ya duba rundunonin hankali wadanda suke su ne kyawawan ayyukan da aka dora masa ya aikata su, sai ya dauki alkawari ga Allah cewa zai aikta su ba tare da takaitawa ba, gwargwadon yadda zai iya.
|