Musulmi da KiristaIdan wani ya yi zalunci to wannan yana koma wa kansa ne, ba ya shafar wani mutum a duniya ko da kuwa dansa ne, balle kuma zaluncin wani ya shafi wasu al'ummu da suka zo baya wadanda yawancinsu ma ba su san me ya faru a tarihi ba! Babban misali kan haka, babu wani kirista a yau da yake kashe musulmi da zai so don ya yi wannan a yau, a shekaru masu zuwa shi ma sai a hau jikokinsa da 'ya'yansa da kisa, balle shi abin da yake yi yau ba yana kashe jika ko da na wanda yake ganin ya yi wa kakanninsa haka ba ne, sai dai yana kashe wanda shi ma a wadancan lokutan an zalunci kakansa da babansa ne shi ma. Idan wani ya yi zalunci to ana auna kimar abin da ya yi da sakamakon abin ne, don haka idan wani ya bautar da wani, ko ya kwace masa gona, sai ya biya hakkin bautar da shi da ya yi ne, ko kuma ya mayar masa da gonarsa, amma ba ya kashe shi ba. Balle kuma wanda ake kashewa ya zama bai san ma an yi wani abu kwace gonaki ko bautar ba. Hada da cewa: Manzon Allah (s.a.w) yana cewa: "Allah ya tsine wa wanda ya kashe wanda ba shi ya kashe shi ba, ko kuma ya doki wanda ba shi ya doke shi ba"[4]. Mu musulmi idan ya tabbata akwai wani musulmi da ya yi zalunci kan wasu jama'a ko wata al'umma a tarihin wannan yanki to mu ne farkon masu suka da la'anarsa kan abin da ya yi, domin idan ya yi da sunan kansa ne, to ya yi ta'addanci, amma idan ya yi da sunan addininsa ne, to laifinsa ya yi girman da ba zamu taba yafe masa ba! Kuma muna yin tir da abin da ya yi da sunan addini!. 6- Sanya Bom Akwai ra'ayin da yake ganin tuhumar musulmi da kirista suka yi kan Bom ce ta jawo rikicin da ya wakana a wannan ranakun da ya shafi rikicin karshe a Jos, sai dai wannan ya shafi rikicin karshe ne kawai da ya wakana a yankin. Karancin tunani da sanya hankali cikin lamurran da suke faruwa a wannan duniya yana da yawa idan mutum ya duba yadda abubuwa suke gudana. Da zato ne aka kai hari kan Afganistan babu yakini kan wanda ya kai hari kan cibiyar kasuwanci ta duniya domin minti 20 bayan faruwar abin shugaban Amurka ya fadi hasashen wadanda ake zato!, sannan da zato ne aka yaki Iraki babu yakini kan samuwar makamin Nukiliya, haka nan da zato ne ake kai wa juna hari a cikin al'ummarmu. Akwai bukatar a tantance wanda ya sanya Bom domin hukunta shi, amma ba kawai don wani abu ya faru ba, sai kuma a kai hari kan wata al'umma bataji-batagani ba. A wannan duniya an fi ye yawo da hankulan mutane da wasa da su, kuma makiyan al'ummu sun samu sabon salon hada rikici tsakaninsu sai su koma gefe suna dariya. Don haka duk sa'adda suka so tayar da fitina sai su aiwatar da wani abu domin su sanya daya ya tuhumi daya, sai gaba, sai rikici, sai yaki. Wannan wani salo ne da makiya dan Adam suke yin sa aduniya.
|