Hakikar Shi'anci
7- Ni dai duk abin da nake nema wajen mai karatu shi ne kada ya dauka cewa kiran da muke na barin bangaranci da kada ya dauka mu ma mun zo da bangaranci ne wanda ya zama ke nan kamar mun yi gudu mun komo inda muka bari. Wannan kuwa domin sanya takobi gaban takobi ba koda yaushe ne yake nufin kira zuwa ga yaki ba, kai yana iya zama ma kira ga barinsa ne, kuma bayar da magani mai daci ba don kiyayya ba ne koda kuwa maganin ya fi ciwon daci. Don haka ne ma sau da yawa hadafofi kodayaushe sukan samu kansu gaban wasu abubwan da suke yi musu kalubale, kuma matukar hadafi yana girma to da sannu zai nemi wasu hanyoyi a lokuta masu yawa kamar yadda hankali yake doruwa kan hakan, kuma gaskiya take yin halinta a kan hakan.
8- Bayan haka dukkan wannan, kasancewa ta mabiyin tafarkin Ahlu-baiti (a.s) ina kira ga dukkan mai karatu da ya duba abubuwan da suka same su a tarihi da yanayin da suka dade suna samun kansu a kai domin ya kasance masa ma’auni da yake gabansa da zai fassara yanayin tunani da na zamantakewa da ya samu Shi'a, kuma da wannan ne zai nisanci karkacewa daga nau’in hukunci da zai yi musu. Idan ya gan su suna tsanantawa a kan tunanin takiyya to ya sani domin ba su fita daga yanayin hakikanin gaskiyar abin da yake faruwa ba ne kuma ba su saba wa shari’a ba, idan ya ga wasu ayyuka da wasu matakai gun wasunsu to kada ya manta mataki ne na hankali kuma bai kamata ba wani ya auna kansa da ayyukan da wani yake gudanarwa a kansa.
9- Ina takaita dukkan wannan takardu da na rubutu da kiran dukkan bangarorin musulmi da su karanta abin da ya shafi junansu da hankali a aikace, kuma su nisanci sukan juna da bata Sunan wanda ya jawo yayyaga da rusa sahun hadin kan musulmi, sannan kuma su tsaya su karanta sakamakon karanta abin da ya shafi junansu domin samun sakamako mai kyau na wannan yanayi, sannan kuma muna kira duka da hakan ga dukkan musulmi da su sanya tarihi a fagen tuhuma domin mu hukunta shi mu huta da dukkan wannan abubuwan takaici da bakin ciki da ya haifar da muke rayuwa cikinsu, mu sani tarihi yana nan yana aiki a kanmu koda kuwa zamani ya yi nisa tsakaninmu da abin da ya faru a cikinsa. Muna rokon Allah taimakon a kan tafiyarmu gidan rayuwarmu mai tsauri, da kuma haskaka tafarkinmu da haskensa, kuma godiya ta tabbataga Allah a tun farko da kuma karshe.
Shimfida:
Ma’anar Kalmar Shi’anci a Lugga
Kalmar Shi’anci a lugga tana nufin biyayyya da taimakekeniya da jibintar al’amuran juna. Don haka kalmar â€کyan Shi'a a lugga tana nufin mataimaka ko mabiya kuma wannan Sunan yawanci ana gaya wa mabiya Imam Ali (a.s) shi, har sai yakebanta da su ya zama su ake gaya wa.
Kuma da wannan ma’anar lugga ne Kur'ani ya yi amfani da kalmar Shi'a kamar a cikin fadin Ubangiji madaukaki "Hakika daga cikin Shi'arsa akwai Ibrahim" aya 83 saffat. Haka nan fadinsa madaukaki "Wannan yana daga Shi'arsa wannan kuma yana daga makiyansa" 15 kasas.
Shi’anci a Isdilahi
Shi’anci da wannan ma’anar ta isdihalhi yana nufin imani da wasu akidu na musamman. Sannan kuma masu bincike sun yi sabani kan wannan akidu game da yawansu ko karancinsu al’amarin da zamu yi bayaninsa nan gaba dalla-dalla, kuma wannan ma’anar ta fi tafarko fadada. Don haka ne zamu bincike game da ma’anar Shi’anci a ma’ana ta biyu saboda ya shafi kowanne daga cikinsu.
Kasancewar Shi’anci imani ne da akidu na musamman don haka ne ma malamai da masu bincike suka yi bayanin ma’anarsa da sassabawa game da bayanin ma'anarsa, ga wasu nan daga cikin wadannan bayanai:
1- Shahidi na biyu a cikin littafin sharhin Lum’a ya ce: "Shi'a su ne wadanda suke biyayya ga sayyidina Ali koda kuwa bai yarda da jagorancin sauran imamai ba, don haka ya hada da Imamiyya da jarudiyya, da zaidiyya da isma’iliyya banda wadanda suke masu wuce gona da iri daga cikinsu kamar wakifiyya da fadahiyya".
2- shaihul Mufid a littafin mausu’a kamar yadda mawallafi ya cirato daga gareshi ya ce: "Shi'a su ne mabiya Ali masu gabatar da shi da fifita kan sauran sahabban manzon Allah (s.a.w), wadanda suka yi imani da cewa shi ne jagora bayan manzon Allah (s.a.w) da wasiyya daga manzon Allah (s.a.w) ko da nufin Allah da izininsa a bisa nassin shari'a kamar yadda Shi'a imamiyya suke ganin shi, ko kuma da siffantawa kamar yadda Jarudiyya suke gani".
|