Sayyid SistaniAYATULLAHI UZMA ASSAYYID ALI AL-HUSAINI SISTANI ( A J Z )SIFFOFINSA
Ya amfana daga sayyid khu’I kusan rabin karni amfani mai yawa wanda yake babu kamarsa a fagen tunani na musulunci da kuma fagage daban daban na ilimomi da mahangai na musulunci masu muhimmanci . wanda malamai da dama suka fita daga makarantarsa da mujtahidai manya masu daraja , wadanda suka dauki nauyin isar da sako da tunani na musulunci da dukkan abinda suke da shi don hidimar ilimi da al’umma ,suka dauki nauyin isar da sakon da yake kunshe da shi da tunani da sadaukarwa . wadanda mafi yawancinsu a yau malamai ne na hauza musamman ta birnin Najafa mai girma da garin Kum mai tsarki daga cikinsu akwai wadanda suke da matsayi mai girma wanda suna iya daukar nauyin tarbiyyatarwa da ilmantarwa da jagoranci na al’umma da marja’anci da kuma shiryar da al’umma a wannan zamani namu. Daga manyan fitattu a cikin wadannan gwaraza a kwai shugabanmu Ayatul-Lahi uzma assayyid Ali Al-Husaini sistani .wanda yana daga manyan futattun daliban sayyid al-khu’I marigayi Allah ya ji kansa wanda suka shahara a ilmi da falala da daukaka da cancanta na matsayi mai girma , wannan maganar tamu zata kasance game da shi nekamar haka: Haihuwarsa da rayuwarsa :
An haife shi a Rabi’ul awwal shekar ta 1349 hijira a Mashhad a cikin gida mai ilimi da addini da tsoron Allah . ya yi karantu a firamare sannan ya karanta mukaddimat da marhala matsakaiciya . ya bi ta da karatun ilmin hankali da sanin Allah a gun manyan malamai har ya kware a kai sosai. Ya halarci karatun bahasul harij a Mashhad yana mai amfana daga ilimin Al-allama Almuhakkik Mirza Al-isfanhani Allah ya ji kansa. Sannan ya cirata zuwa birnin Kum a lokacin marja’in nan mai girma Assayyid Burujardi Allah ya ji kansa a shekarar 1368 hijira. Ya halarci bahasin ilimi na malamai manya a wannan lokaci kamar sayyid Burujardi a fikihu da usul . ya kuma samu da yawa da ga iliminsa da tajribarsa da nazarinsa kan ilimin rijal da hadisi , kamar yadda ya halarci karatu wajan malami assayyid alhujja al-kuhmari Allah ya ji kansa. Sannan sai ya bar garin Kum ya fuskanci cibiyar ilimi da falala wato birnin Najaf mai girma a shekarar 1371 ya kuma halarci karatun manyan malamai kamar Al-imam Al-hakim da Asshaikh Hasan hilli da imam Al-khu’I Allah ya kara musu yarda gaba daya. Kamar yadda ya lizimci sayyida khu’I ya yi karatu a wajansa na fikihu da usul sama da shekara goma kamar yadda ya lizimci karatu wajan Asshaikh Hilli na usul cikakkiyar daura . Ya shagaltu da koyar da bahasul hariji a fikihu a shekara ta 1381 hijira a cikin littafin nan na Makasib na sheikh Al-ansari Allah ya ji kansa .ta haka aka samu littafin nan nasa na sharhin littafin tsarki da mafi yawan hukunce hukunce fur’ua na salla sannan ya biye shi da sharhin littafin urwatul wuska na sayyid Diba’diba’I ta haka ya samu fitar da sharhin littafin tsarki da salla da wani bangare na littafin humusi kamar yadda ya fara bayar da karatu a bahasul hariji na usul a watan sha’aban na shekarar 1384 hijira ya kuma kammala daura ta uku daga usul din a sha’aban na shekarar 1411 hijira mutane da yawa sun yi rikodin din(dauka a rikoda) wannan karatu na sa. Hazakarsa ta ilimi:
Assayyid sistani fifikonsa akan sauran dalibai ya bayyan a cikin bahasin karatu da yake da malamansa ta hanyar karfin ishkali da saurin fahimta da yawan bincike da bibiyar littafan fikihu da na Rijal da ci gaban bincike na ilimi da nacewa da bayar da mahanga a fage daban daban na ilimin Hauza . wanishaida akan haka shi ne shaidar sayyid khu’I gare shi a rubuce da wata shaidar ta Asshaikh Alhilli . wanda sun shaida da matsayin ijtihadinsa har sau biyu masu tarihin 1380 hijira suna cike da yabo akan fifikonsa da iliminsa al’amarin da aka sani ko daga sayyid khu’I ba ya shaidawa ga daliban da ijtihadi a rubuce sai kadai ga sayyid sistani da kuma Asshaikh Ali Aal-falsafi daya daga shahararrun malaman Mashhad. Kamar yadda Asshaikh Al-allama masani hadisi a zamaninsa Aga buzurg Attehrani Allah ya ji kansa ya shaida masa a shekara ta 1380. yana mai yaba masa akan kwarewarsa ta ilimi a rijal da hadisi. Haka nan ya rabauta da shaida daga malamai yana dan shekara talatin da biyar a rayuwarsa. Baiwar tunaninsa da talifansa
Tun kusan shekara 34 daga rayuwarsa ya fara bayar da karatu a bahasul hariji na fikihu da usul da rijal ya kuma fitar da sakamako na ilimi mai yawa ya yi bincike a bahasin makasib da tsarki da salla da hukunci da humusi da wasu sashen ka’idodin fikihu kamar riba da takiyya da ka’idar ilzam ya kuma koyar da usul daura uku . wasu daga cikin wadannan bincike a shirye yake don bugawa. Malamai da yawa sun fito daga makarantarsa ne kamar Allama Asshaikh Mahadi Marwaridi da Allama assayyid Habib Hhusainiyyan da Allama assayyida Murtada al-asfahani da Assayyid Ahmad Almadadi da Asshaikh Bakir Al-irawani da sauran manyan malaman Hauza . kamar yadda ya shagaltu da wallafa littafai masu muhimmai da risaloli domin yalwata laburaren ilimin addini da littafai masu gamsarwa . hade da abin da ya wallafa na bahasin malamansa na fikihu da usul. Wanda ya hada da ; 1- Sharhin littafin urwatul wuska 2- Albuhusul usuliyya 3- Kitabul kada’I 4-Kitabul bai’I 5-Risala fil libas wal mashkuk 6-Risala fi ka’idatul yad 7-Risala fi salatil safar 8-Risala fi kai’datij tajawuz wal farag 9-Risala fil kibla 10-Risala fit takiyya 11- Risala fi ka’idatil ilzam 12-Risala fil ijtihad wattaklid 13-Risala fi kaidati la darar wala idrar 14-Risala fir riba 15-Risala fi hujjiyyati marasili ibn abi umair 16-Nakdi risalati tashihil asatiz lil ardabili 17-Sharhi mashyakhatiz tahzibaini 18-Risaltun fi masalikil kudama’a fi hujjiyatil akhbar. Hada da sauran littafai da dama rubutattu da risala amaliyya ta hukunce hukunce saboda masu taklidi. Hanyar bahasinsa da koyarwarsa
Hanyar koyarwarsa tana da bambanci da yawa da ta sauran malamai na Hauza da masu bahasil hariji misali a fagen usul hanyar koyarwarsa ta kasance kama r haka : 1-Bayar da labarin tarihin bahasi da sanar da asasinsa da farinsa : da yana iya kasancewa daga falsafa kamar bahasin mushtak da tarkibat ko daga Akida ko Siyasa ko bahasin ta’adil da tajrih ko kum a abin ya shafi yanayi n Siyasa da Akida da imamai suka samu kansu a ciki . irin wannan hanya ta binciken tarihin mas’ala ita kan kai mu ga sanin hakikanin abin da ya faru da kewaye wa ga masa’ala da kai wa zuwa ga hakikanin ra’ayoyin da aka yi binciken mas’alar akansu. 2- Kokarin damfara tunanin Hauza da wayewar duniya ta wannan zamani ; kamar a bahasinsa na bambancin da yake tsakanin ma’anar Harafi da Suna da cewa menene hakikanin bambancinsu na zati ne ku na la’akari ne da bambancin hangen da ake yi wa ma’anoni yayin amfani da su ? Anan ya zabi ra’ayi ne na mai littafin Kifaya dacewa bambancin na yanayin yadda ake duba ma’anonin ne ba bambnci ne na zatin ma’anonin ba . kuma ya yi gini ne akan mahangar falsafa sabuwa wato it ace mahangan nan ta yawaitar riska ta mariskai a kwakwalwar mutum da dabi’arsa ta yadda yana iya yuwuwa ga kwakwalwa ta hangi abu daya da mahanga daban daban wani lokaci a matsayin mai zaman kansa wani lokaci kuma a matsayin yana damfare da waninsa . haka ma yayin da ya shiga maganar mushtak da jayayyar malamai kan ismuz zaman sai ya shiga maganar zamani a mahangar falsafa sabuwa haka ma a mahangar sigar umarni da kalmarsa da bahasin tajarri ya shiga nazarin malamai kan yadda malaman zamantakewa suka kasa umarni da nema da cewa sakamakon shi mai nema ya siffantu da neman ta hanyar kasancewar sa yana ganin shi ne sama ko daidai yake da wanda ya nema wajansa ko kuma yana ganin kansa kasan wanda yake nema a wajansa ne. haka nan ya sanya ma’aunin azabtar da mai sabo da cewa saboda shi bawa ya yi tawaye ga umarnin ubangijinsa ne kuma haka yake bisa kashe kashen matsayi da darajojin al’umma a zamantakewarsu ta yadda zaka ga akwai bawa da uban gida da na sama da na kasa da sauransu .wannan kuma bahasi ne kan dabakokin a al’umma ba magane ce ta doka ba wacce ta ginu bisa masalahar al’umma .
|