aikin hannuIyali– Yara da Samari

Kwado

Wannan kwado mai ban al’ajabi yana tashi ne, idan ka yi wannan kwado mai ban al’ajabi zaka iya yin tseren tashin kwado ko kuma ka auna tashin wannan kwadon.

Abubuwanda ake bukata:

Takarda

Almakashi

Kaloli

Da farko sai ka samu murabba’in wata guntuwar takarda sannan sai ka nade takardar ka ninka ta.

Sai kuma ka yanka wani rantangula domin murabba’in ya yi daidai (murabba’in da yake an lankwasa shi kuma ya yi kama da musallas)

­­1 2 3 next