Tarihin shi'a



Ubangiji Madaukakin Sarki (S.W.T)

Mun yi imani cewa Allah Madaukaki daya ne makadaici babu wani abu kamarsa, wanzazze bai gushe ba kuma ba ya gushewa, Shi ne na farko kuma Shi ne na karshe, Masani, Mai Hikima, Adali, Rayayye, Mai Iko, Mawadaci, Mai ji, Mai gani. Ba a siffanta Shi da abinda ake siffanta halittu, shi ba jiki ba ne, kuma ba sura ba ne, ba jauhar[i] ba ne kuma ba ard[ii] ba ne, ba Shi da nauyi ko sakwaikwaya, ba Shi da motsi ko rashin motsi, ba Shi da guri ba Shi da zamani kuma ba a nuni zuwa gare Shi, kamar yadda babu kini gare Shi, babu kama, babu kishiya, babu mata gare Shi, babu abokin tarayya, kuma babu wani tamka gare Shi.

Maganai ba sa riskar Sa Shi kuwa yana riskar maganai, duk wanda ya ce ana kamanta Shi to ya zamar da Shi halitta ke nan, wato ya suranta fuska gare Shi da hannu da kuma idaniya, (kuma cewa Shi yana saukowa zuwa saman duniya, ko kuma cewa zai bayyana ga 'yan aljanna kamar wata ko kuma makamantan wannan, to lalle yana matsayin wanda ya kafirce da Shi ne wanda ya jahilci hakikanin mahaliccin da ya tsarkaka daga nakasa, kai dukkan abinda muka bambance Shi da sake-saken zukatanmu a mafi daldalewar ma'anarsa to Shi abin halitta ne kamarmu mai komawa ne gare mu kamar yadda Imam Bakir (A.S.) ya fassara shi gare mu da bayani mai hikima da kuma zurfin ma’ana ta ilimi mai zurfi.

Har ila yau ana kirga duk wanda ya ce yana nuna kansa ga halittunsa ranar Kiyama a cikin kafirai[iii] koda kuwa ya kore masa kamantawa da jiki, batun baka ne kawai kuma irin wadannan masu da'awa sun sandare ne kawai a kan wasu laffuza na zahiri na Alkur'ani ne ko wasu hadisai kuma suka karyata hankulansu suka yi watsi da su. Don haka suka gaza yin aiki da zahiri gwargwadon yadda nazari da dalilai suka hukunta da kuma ka'idojin lakabi da kuma aron ma'anar kalma.

Tauhidi (Kadaita Allah)

Mun yi imani ya wajaba a kadaita Allah ta kowace nahiya, kamar yadda ya wajaba a kadaita shi a zatinSa haka nan muka yi imani da cewa Shi kadai ne a zatinsa da wajabcin samuwarSa, kazalika ya wajaba kadaita Shi a siffofi. Wannan kuwa saboda imani ne da cewa siffofinSa ainihin zatinsa ne kuma Shi a ilimi da kudura ba Shi da na biyu a halitta da arzutawa kuma ba Shi da abokin tarayya, a cikin dukan kamala kuma ba Shi da kwatankwaci.

Haka nan mun yi imani da kadaita Shi a bauta bai halatta a bauta wa waninsa ba ko ta wace fuska, kamar kuma yadda bai halatta ba a hada Shi da wani abu nau’in nauo'in ibada, wajiba ce ko kuma wadda ba wajiba ba, a salla ne ko kuma a wasu da ba ita ba na daga ibadoji.

Duk wanda ya yi shirka ya hada wani da Shi a ibada to Shi Mushiriki ne kamar kuma wanda yake riya a ibadarsa yana neman kusacin wanin Allah (S.W.T), hukuncinsa Shi wanda ya yi haka hukuncin wanda ya bauta wa gumaka ne babu bambanci a tsakaninsu.

Amma abinda ya shafi ziyartar kaburbura da kuma gudanar da bukukuwa ba sa daga cikin nau'in neman kusaci ga wanin Allah ko ibada kamar yadda wasu daga masu son suka ga tafarkin Shi'a Imamiyya suke so su raya suna masu jahiltar hakikanin al'amarin, Sai dai wannan wani nau'i ne na kusanci ga Allah (S.W.T) ta hanyar kyawawan ayyuka, kamar neman kusaci gare Shi ta hanyar gaishe da marar lafiya, da raka gawa zuwa kabari, da ziyartar 'yan'uwa a Addini, da kuma taimakon fakiri.

Don zuwa gaishe da marar lafiya Shi a kan kansa alal misali, kyakkyawan aiki ne wanda mutum kan samu kusaci ga Allah ta hanyarsa, ba neman kusaci ga marar lafiyar ba ne da zai zamar da aikata Shi ya zama bauta ga wanin Allah (S.W.T) ko kuma shirka a bautarSa.

Haka nan sauran misalan kyawawan ayyuka irin wadannan wadanda a cikinsu har da ziyartar kaburbura, da gudanar da bukukuwa, da rakiyar gawa zuwa kabari da kuma ziyartar 'yan'uwa. Amma kasancewar ziyartar kaburbura da bukukuwan Addini a matsayin kyawawan ayyuka a shari'a al'amari ne da fannin fikihu ke tabbatar da Shi ba nan ne gurin tabbatar da Shi ba.

Manufa ita ce cewa aikata irin wadannan ayyukan ba sa daga cikin shirka a ibada kamar yadda wasu suke rayawa kuma ba ma ana nufin bauta wa Imamai da su ba ne, abin nufi da su kawai Shi ne raya al'amarinsu, da kuma sabunta tunawa da su, da kuma girmama alamomin Addinin Allah da tare da su "wannan, duk wanda Ya girmama alamomin Addinin Allah to lalle wannan yana daga cikin ayyukan ibadar zukata." Surar Hajj.



1 2 3 4 5 6 next