Bahasin Kur'ani1- Abu Ja'afar As-Saduk Muhammad bin Ali bin Husain bin Babawaihi Al-Kummi wanda ya yi wafati a shekara ta 381 bayan hijira, yana cewa: "Akidarmu dangane da Kur'ani mai girma wanda Allah ya saukar, wa manzonsa (S.A.W) shi ne wannan Kur'ani da ke tsakanin bango biyu. Wato; daga Fatiha zuwa Nasi, babu kari babu ragi, kuma duk wanda ya jingina mana cewa mun ce Kur'ani ya fi wanda ke hannun mutane yawa, to shi makaryaci ne. Littafin Al'I'itikadat. 2-Imam Khumaini (Allah ya ji kansa) yana cewa lallai mu muna hana samuwar tawaya ko jirkita cikin Kur'ani hani mai tsanani kamar yanda wannan shi ne mazhabar masana daga malaman sunna da shi'a kamar yanda wannan shi ne abin da dukkan bangarori biyu na musulmai suka yarda da shi. A wani wajen kuma a halin yana yin raddi ga wanda ya raya cewa akwai jirkita cikin Kur'ani, sai ya kara da cewa: To muna ce masa: Lallai bacin wannan mummunar magana, kana bacin irin wannan yasasshen ra'ayi ya fi karfin ya buya ga duk wani mai hankali. 3-Sheikh Tusi babban malami masanin fikihu a mazhabar Jaafariyya wanda aka fi sani da sheihut ta'ifa wanda ya yi zamani tun shekaru dubu da suka gabata yana fadi a Mukaddimar Tafsirinsa; Tibyan cewa: Kari ko ragi sam bai dace da martaba da matsayin Kur'ani ba. Hafiz Muhammad Sa'id
|