Hukuncin DukiyaDa sunan Allah madaukaki Dukiya ita ce duk wani abu da yake da amafani kuma ake iya amfana daga gareshi domin ci gaban rayuwa, wanda yake karbar a yi musayansa da wani abu. Wannan abin yana iya kasancewa na sanyawa ne, ko ci, ko ajiya, ko hawa, da sauransu. Dokiya ta kasance wani abu ne da yake hanyar biyan bukatun mutane, don haka ne ta kasance wani bangare mai muhimmanci a cikin rayuwar al'umma. Magana kan dukiya wani abu ne mai muhimmanci matuka domin tana nuna mana hanyar da ake samun asasin tafiyar da lamurran rayuwar mutane. Musamman da yake dukiya ta zama ma’auni na musayan abubuwan rayuwa da ake iya mallaka bisa yardar bangarori biyu na mutane. Kuma ana iya mallakar dukiya ta hanyar gado, ko kyauta, ko saya, da sauran hanyoyin da shari’a ta yarda da su. Sannan duk wani abu da zai iya kasancewa a yi musaya da shi, kuma yake karbar a saya ko a sayar da shi, yana iya kasancewa an kira shi dukiya. Akan yi bayanin nau’in dukiya bisa yadda aka yi la’akari da kashe-kashenta ne, sai wasu suka kasa dukiya zuwa ga ainihin abu, da mafaninsa, wasu kuwa suka kasa ta gida biyu: imma dai dukiyar al’umma, ko ta mutum daya. Dukiyar al’umma ita ce dukkan dukiyar da aka sanya ta domin maslahar dukkan al’umma, kamar ta zakka, da humusi, da baitul mali, da haraji, da ganima, da sauransu. Amma dukiya kebantacciya ga wani mutum ita ce wacce wani yake mallakarta, kuma babu mai ikon tasarrufi da ita sai da izinin mai ita. (Riyadus Salihi: Sayyid Ali Dibadiba; j 2, s 40). Muna iya ganin yadda imamai jagororin al’umma wasiyyan manzon Allah (s.a.w) suka ki yarda da taba dukiyar al'umma da wajabcin mayar da ita kamar yadda zamu bayar da misali kan hakan: A ruwayar Ali bn Rashid ya ce: Na tambayi Abul Hasan (a.s) na ce masa na sayi kasa kusa da gidana da dinare dubu biyu, yayin da na biya kudi sai aka ba ni labarin cewa wannan kasar wakafi ce, sai ya ce: “Sayan wakafi bai halatta ba, kuma abin da ka samu ba ya zama naka, sai dai ka bayar da shi ga wadanda aka yi wa wakafinsa. Sai ya ce: Ban san wai mai ita ba. Sai ya ce: Ka yi sadaka da amfaninta (Makasibul Muharrama: Khomain / j 2/ s 268). A fili yake cewa wannan dukiya ta wakafi da yake ita mallaka ce ta al’umma babu wani mai ikon mallakarta koda kuwa ya saya, ya zama dole ya mayar da ita mallakar al’umma gaba daya. Sannan wannan ya taimaka mana wurin sanin hukuncin dukiyar da aka san adadinta, amma ba a san mai ita ba wanda yake nuni da tilascin yin sadaka da ita. Akwai hanyoyi da shari’a ta sanya domin mallaka kowace iri ce kamar raya abu, taskacewa, farauta, bibiya, gado, lamuni, ramuwa, da kuma kullawa kamar ciniki, rance, inshore, juyar da bashi kan wani, sulhu, tarayya, wakafi, wasiyya da sauransu. (Alfikihul Islami fi Saubihil Jadid: Sheikh Mustapah Azzarka; 1 / 60-61).
|