Halifancin Imam Ali (a.s)
Idan Ya Kasance Halifancin Imam Ali (a.s) Daga Allah Ne, To Don Me Ya Sa Ba Ta Samu Ba? Idan mun duba sosai zuwa ga wannan tambaya ko kuma mu kira ta shubuha da aka kawo kan wannan mas'alar zamu ga mai tambayar bai bambance tsakanin shar'antawa da samarwa ba. Nufin Allah (s.w.t) kala biyu ne; akwai abin da ake ce masa; Nufi na shari'a, da kuma nufi na samarwa. Halifancin imam Ali (a.s) nufi ne na shari'a da aka dora shi kan bayi. Nufi na samarwa ba yadda zai kasance ya saba da iradar Allah madaukaki, misali idan Allah ya so ya samar da wani abu, babu wani karfi da ya isa ya hana faruwar wannan abu. Idan Allah yana son a misali ya dauki ran wani bawansa, to babu wani karfi da ya isa ya hana, kuma babu wata dubara da ta isa ta sha gabansa, don haka a nan nufin Allah dole ya faru ya wakana, halittunsa sun so, ko sun ki. Ubangiji ya yi nuni da wannan lamarin a littafinsa madaukaki da cewa: "Idan ya yi nufin wani abu, yana cewa da shi ne kasance, sai ya kasance". Surar Gafiri: 68, Yasin: 82. Amma nufin shari'a ba haka yake ba, idan Allah ya so abu a shar'antawa ba a samarwa ba, sai ya yi wahayi ga annabinsa (a.s) ya isar wa mutane sakon. Amma tun da mutane suna da zabi kamar yadda Allah ya halitta su, suna da ikon sabawa ko biyayya. Babban misali a nan shi ne misalin Iblis da ya kauce wa hanya, ya ki yin sujuda ga Adam (a.s), da kuma kaucewar da mutane suka yi na rashin imani da Allah, da rashin biyayya ga wasiyyar manzon Allah (s.a.w) da musulmi suka yi. Allah ya so iblis ya yi sujada ga Adam (a.s), kuma ya so halittunsa su yi imani da shi, ya so a yi riko da wasiyyan annabawansa (a.s), amma babu ko daya daga cikin iradar Allah da ta tabbata, ko ta wakana. Me ya sanya rashin faruwar wannan iradar ta Allah? Shin saboda rauninsa ne da rashin karfinsa ko kuwa? A nan ne muke bayar da amsa cewa; A nan saboda ya halicci mala'iku, da aljanu, da mutane, hatta da sauran halittunsa, da zabin biyayya ne, saboda haka suna iya saba masa, ko kuma su bi shi. Don haka Iblis daya ne daga mala'iku masu daraja, amma sai ya saba ya tabe. Aljanu kuwa muna ganin dalilan Kur'ani sun yi mana nuni da yadda suka kauce wa hanya, mutane kuwa mu daga cikinsu muke, kuma muna ganin kwamacalar da suke kanta, sauran dabbobi kuwa ya zo a ruwayoyi masu yawa cewa; an haramta wasu daga cikinsu ne, saboda ba su yi imani ba. A yanzu wadannan halittun zamu ce, sun fi karfin Allah (s.w.t) ne don haka suka iya saba masa?! A fili yake cewa babu ko daya, sai dai Allah da hikimarsa ne ya halitta su masu zabi, da karfin nasu, da nufinsu, da iliminsu, da ikonsu, duk halittarsa ce, ba zasu iya tabuka komai ba, sai abin da ya shata musu shi, kuma ba zasu iya fita daga ikon da ya ba su ba, don haka ne sai kowannensu ya zauna a matsayinsa. Da wannan bayanin ne zamu gane cewa: akwai bambanci yayin da muke cewa; Allah ya so duniya ta kasance, da fadinmu cewa; Allah ya so mutane su yi imani. So na farko iradar Allah ce ta samarwa, don haka dole ta wakana, amma so na biyu iradar Allah ce ta shar'antawa, don haka ba dole ba ne ta kasance. Ba don komai ba kuwa, sai don tana da sharadin bayinsa su aiwatar da ita kafin ta wakana. Don haka idan ba ta kasance ba, gajiyawar tana komawa ga bayinsa ne, ba gareshi ba. Sabanin irada ta farko a samarwa, wannan idan ta ki wakana, to gajiyawar tana komawa zuwa ga Allah (s.w.t) ne. Don haka ne zamu ga Allah ya so wa al'ummun wannan duniya shiriya, da arziki, da yalwa, da rabauta, don haka ne ya saukar da hukunce-hukuncensa, amma tun da sharadin faruwar haka sai da karbar al'ummun, kuma su al'ummun ba su karba ba, don haka babu ko daya da dan Adam ya samu daga ciki har a yau. Allah ya so wa mutane alheri su kuma sun so wa kansu sharri, ya sanya musu sharadin samun rabauta a duniya da lahira shi ne su yi biyayya ga manzanninsa sai suka kauce hanya, ya sanya musu hanyar mafita sun ki karba. Idan mun ga hukumar wasiyyan Annabi Musa (a.s) da na Annabi Isa (a.s), da na manzo Muhammad (s.a.w), ba su samu damar mulkar al'umma ba, hukumarsu ba ta kafu ba, to wannan duk yana koma wa zuwa ga cewa; al'ummarsu ba ta yarda ba ne, ba ta karbi sakon manzannin ba, ba su amince ba. Don haka rashin kasantuwar iradar da Allah ya zaba musu, gajiyawar da takaitawar tana koma wa zuwa garesu ne. Don haka ne ma muka ga manzon Allah (s.a.w) ya yi nuni da cewa; Al'ummarsa sai ta bi sawun Yahudawa da Kiristoci, kamar yadda wadancan ba su karbi wasiyyan annabawansu ba, haka ma al'ummarsa ba zata karbi wasiyyansa ba. Kuma ya fadi cewa: Duk wasiyyansa sha biyu, da 'yarsa, wannan al'ummar zata yi gaba da su ne, zata yaudari Ali (a.s), zata kashe shi, zata kashe duka sauran imamai daga zuriyarsa, zata karyata su, zata takura su, amma wannan ba zai cutar da su ba, kuma ba zai hana kasancewarsu imamai jagorori ba. Wato kamar yadda idan annabawa (a.s) ba su riki hukuncin al'umma a hannunsu ba, sakamakon al'ummar ta ki yarda da su, wannan ba ya cutar da annabcinsu da jagorancinsu. To haka su ma wasiyyai; wato jagororin al'umma bisa shari'a wadanda su ne halifofin da annabawa suke ayyanawa a matsayin masu halifancinsu bayan wucewarsu, don ba su riki tafiyar da lamarin jagorancin al'umma ba, to wannan ba ya cutar da kasancewarsu halifofin annabawan wasiyyansu. A cikin wannan al'ummar gaba daya babu wani wanda yake da wadannan siffofi sai su imaman shiriya da tsira, wadanda manzon Allah (s.a.w) ya yi wasiyya da su. Su ne wadanda ba su riki mulkin al'umma ba, amma kuma wannan ba ya cutar da kasancewarsu halifofi kuma wasiyyan manzon Allah (s.a.w). Duba: Mu'ujamul Kabir: Dabarani: 2/213, 214, H; 1794, da kuma 2/256, H; 2073. Majma'uz zawa'id: 5/191. Da wannan bayanin zamu fitar da wasu natijoji kamar haka: Manzon Allah ya yi bayanin cewa: Za a yi galaba kan halifofifnsa sha biyu kamar yadda aka yi a kan na sauran annabawa (a.s), kuma mutane ba zasu karbe su ba sai 'yan kadan, sai dai wannan ba ya cutar da jagorancinsu. Cin galaba kan mutum, da rashin biyayya gareshi, da rashin imani da shi, ba sa cutar da annabcinsa idan Annabi ne, ko kuma halifancinsa idan wasiyyin Annabi ne. Don haka ne ma muka ga mafi yawan annabawa da wasiyyansu, an karyata su, an kashe su, an ki karbarsu. Wadanda suka yi jagorancin al'umma daga cikinsu 'yan kadan ne, haka nan wasiyyan Muhammad manzon Allah (s.a.w) su ma haka suka samu kansu kamar sauran!.
Hafiz Muhammad Sa'id hfazah@yahoo.com www.hikima.org Tuesday, October 20, 2009
|