Ilimin Gaibi Shin Akwai Wanda Ya San Gaibi Ban Da Allah? Idan muka duba ayoyin Kur'ani mai girma zamu ga suna nuna mana sanin gaibi da ma abin da yake sarari duk na Allah ne; ayoyi kamar: Naml: 65, da An’am: 59. Sai dai idan mun lura zamu ga sanin gaibi da ma'anar da ya zo a wannan ayoyin bai kore samuwar saninsa ga wasu bayi da Allah ya zaba ba, don haka ne zamu iya fahimtar ma'anar babu wanda ya san gaibi sai Allah tana nufin asalin saninsa, da cewa; babu wanda ya san gaibi da kansa sai ubangiji madaukaki. Amma wanin ubangiji idan ya san gaibi to da sanarwar ubangiji ne ba da kansa ba, don haka saninsa da gaibi yana bin sanarwar da Allah ya yi masa ne, da ba shi kyautar wannan ilimi da Ubangiji madaukaki ya yi, don haka ne zamu ga ayar nan ta surar Jinn: 26-28, da sauran ayoyi kamar: Aali Imran: 179, 44, da Yusuf: 102, duk suna nuni da haka. A cikin Kur'ani mai girma ya zo da bayanin annabawa (a.s) da Allah madaukaki ya sanar da su gaibi, idan mun koma wa ayoyi kamar haka: Yusuf: 41, da Aali Imran: 49, zamu ga yadda annabawa suka san gaibi kuma suka Hafiz muhamad Sa'id Thursday, September 24, 2009
|