Hadisin ManzilaMene Ne Hadisin Manzila? Ya zo a babin darajojin imam Ali (a.s) a littattafai masu yawa kamar Sahih Buhari da Sahih Muslim da Masnad Ahmad bn Hanbal, da Tirmizi, da Ibn Majah, cewa Manzon Allah (s.a.w) ya ce da Ali (a.s): “Kai a wajena kamar Haruna (a.s) ne da Musa (a.s), sai dai babu annabi bayanaâ€. Sai ya tabbatar da duk wata alaka da take tsakanin Musa da Harun (a.s) amma domin gudun kada mutane su dauke Ali a matsayin Annabi sai manzo mai hikima ba tare da wata fasila ba sai ya togace annabta daga imam Ali (a.s). Hadisin manzila "Hadisin Matsayi" Shi ne: Fadin manzon Allah (s.a.w) ga imam Ali (a.s) cewa: "Kai a wurina kamar matsayin Haruna wurin Musa ne, sai dai babu Annabi bayana". Sannan manzon rahama ya fadi wannan hadisi a wurare kamar haka: 1. Ranar hada 'yan'uwantakar Juna tsakanin sahabbansa 2. Ranar Badar 3. Ranar Khaibar 4. Ranar Tabuka 5. Ranar Mubahala
|