Annabcin Annabi Musa (a.s)
Shin Annabcin Annabi Musa (A.S) Na Duk Duniya Ne Ko Kuwa? Duba zuwa ga wannan maud’in yana bukatar bincike Na farko: Kiran Annabi Musa (a.s) zuwa ga kadaita Allah madaukaki; Na biyu: Kasancewar shari’arsa ta game daukacin dukkan al’ummun duniya ne; Wasu ayoyi masu yawa suna nuni da kasancewarsa an aiko shi ne zuwa ga Banu Isra’il, kamar ayar nan da take cewa: “Yayin da Musa yake cewa da mutanensa ya ku mutane….†Saffi: 5. Da ayar nan da take cewa: “Kuma hakika Musa ya zo muku da ayoyi (hujjoji) sannan sai kuka riki dan maraki…â€. Bakara: 92. Da ayoyi masu yawa da suke nuni da aika Musa (a.s) zuwa ga mutanensa, sai dai wannan ba ya nuni a fili da cewa sakonsa bai shafi sauran al’umma ba, domin ga Annabi Shu’aibu (a.s) an aika shi zuwa ga mutanen “Madyanaâ€, a lokaci guda kuma ga shi an aika shi zuwa ga mutanen garin “Aikaâ€. Duba; surar A’arafi: 85, da kuma Shu’ara: 176-177. Muna iya cewa da’awar Musa (a.s) ta kadaita Allah ta shafi Banu Isra’il da kibdawa ne, kuma muna iya fahimtar wannan daga surar nan ta A’arafi: 105, da 134, da surar Daha: 43, 44, 47, da surar Shu’ara: 16-17, 27, da surar Zukhuruf: 46, da surar Muzammil: 15-16, da surar Zariyat: 38. Da sauran ayoyin da suke nuna cewa an aika Musa zuwa ga Fir’auna da Banu Isra’il ne, kuma kiransa yana nuni da kawar da bautar gumaka, da tsafi, da sihirin Fir’auna da mutanensa, har ma aka yi kure tsakanin Annabi Musa (a.s) da masu sihiri kuma ya yi galaba a kansu. Wannan duk yana nuna mana yadda da’awarsa ta shafi wanin Banu Isra’ila na Kibdawa da makamantansu, sai dai duk da haka ba mu da wani dalili mai gamsarwa a Tana iya yiwuwa da’awarsa ta zo ne domin ta tseratar da Banu Isra’il, sai dai domin da’awarsa ta samu karbuwa to dole ne ya yi tattaunawa da fir’auna domin ya tabbatar masa cewa; daga Allah madaukaki yake, ta yadda za a ce; da tseratar da su zai yiwu ba tare da shan wannan wahalar ba, to da ya yi. Sannan muna ganin cewa; duk sa’adda ya tabbatar wa fir’auna cewa shi manzo ne daga ubangijinsa sai ya kara masa da cewa ka aika Banu Isra’il tare da ni. Daha: 47. Don haka ne ma zamu ga yayin da ya kasa tseratar da su ta hanyar tattaunawa da fir’auna sai ya dauki wata hanyar ta mu’ujiza domin ya tseratar da su. Ayoyin da suka zo kamar haka suna nuni da wannan: A’arafi: 134, Nazi’at: 17-19, Daha: 77, Yunus: 90, Dukhan: 24. Da kuma nuni da cewa; muhimmancin tattaunawa da fir’auna domin a samu tsiran Banu Isra’il ne. Hada da cewa wasu ayoyin sun nuna cewa bayan Nuhu (a.s) an aika annabawa (a.s) masu yawa zuwa ga mutanensu har zuwa
|