Mu'amalar TarbiyyaWasu sun dauka yaronsu ba mutum ba ne, ba a hira da shi, ba a yawo da shi, ba a ma kula shi, ana ganin sa kamar ba mutum cikakke ba, wasu ma suna haramta masa soyayyar da yaro yake bukata ga uba. Idan yaro ya rasa soyayyar da ake samu daga uba da uwa sai wannan ya sanya shi yin nesa da su, sai ya samu miyagun samari da wasu lalatattun da zasu nuna masa kauna a waje, su nuna masa halin jin shi mutum ne mai 'yancin kansa, yana jin dadin hira da su, yana ganin yana samun wata kariya daga gare su, kuma yana jin shi mutum ne a wajansu. Sai ya makale musu, su zama abokansa ko ya zama yaronsu, ta haka ne da yawa yara da suka rasa soyayyar iyaye tarbiyya ta lalace. Kamar yadda idan mutanen gida suka nisanci yaro sukan tura shi waje a aikace domin ya samu inda zai samu wannan soyayyar da ya rasa a gida da kan iya jawo lalacewar tarbiyyarsa, haka ma sukan lalace idan aka nuna masu soyayya ta rashin hankali da lissafi da zaka ga wasu iyaye suna nuna wa yaransu. Tsakanin Yara
1- Yana da muhimmanci samar wa yara lokacin annashuwa, da shakatawa, da wasanni; abin haushi a kasashenmu rashin ko in kular masu mulki da halin yara ya munana kwarai da gaske, ta yadda kana iya samun yanki, ko unguwa mai mutane sama da miliyan amma ba su da filin wasa, da na shakatawa, da na wasannin yara. Wannan kuwa sakamakon maciya amanar al’umma da suka yawaita wadanda ba sa jin zafin halin da yara da samari suke ciki, kuma babu ruwansu ko kadan da lafiyarsu ko annashuwarsu da tunaninsu, don haka yana kan iyayen yara su nemi hakkin haka wajan hukuma don walwalar ‘ya’yansu. Idan ka haramata wa yaronka wasanni kana cutar da shi ne, domin hakan yakan dakushe wa yara tunani, sannan yakan iya haifar da dabi’ar son ramuwar abin da ba su yi ba na wasannin yara. Mutum har ya girma yana bukatar yin wasanni sai dai yakan sassaba ne tsakanin manya da yara, da kuma kasancewar dalilin da yakan sanya kowannensu yin wasannin yakan sassaba, shi ya sa har yaro ya zama saurayi, ya manyanta, ya tsufa, ana son ya rika wasannin motsa jiki. Kuma yana hawa kan hukuma a kowane yanki ta samar da wajan shakatwa da wasannin yara, da filin kwallo. Amma abin takaici a kan samu makiya filayen wasannin jama’a ta yadda ita hukuma ba ruwanta da jin dadin al’umma. Wani lokaci kuma wata hukumar tana ware irin wannan ga al'umma, amma da an samu wani maciyin amanar al’umma ya hau kan kujerar mulki sai ka gan shi yana lasar baki yana hadiyar yawu shi ya ga wani babban fili, idan ba a dauki mataki kwakkwara ba yanzu ka ga mayen filin ya kame wannan fili ya rabar. Don haka yana kan iyaye su bar yara su sakata da yin wasanni, su saya wa yaro abin da zai rika debe masa kewa, su yalwata masa filin da zai samu nishadi. Ya zo a cikin surar yusuf aya ta 12, cewa; Ka aika shi tare da mu gobe ya yi annashuwa ya yi wasa…". Sannan wata ruwaya ta zo cewa; wata rana a kan hanya manzon rahama (s.a.w) ya ga wasu yara suna wasa da kasa, sai wasu daga sahabbansa suka so su hana su yin wannan wasan, sai manzon Allah (s.a.w) ya ce da su: "Ku kyale su, hakika kasa kakar (farin cikin) yara ce"[2]. 2- Manzon rahama (s.a.w) yana cewa: Ku yi adalci tsakanin 'ya'yanku, kamar yadda kuma kuke son a kiyaye daidaito a tsakaninku, a cikin kyautatawa, da adalci[3]. Kada ka nuna wa yaranka a fili ka fi son daya a cikinsu[4], a nan da mata da yara duka daya ne, soyayyar da kafi yi wa daya kada ta zama a fili. Ko da zaka yi wa daya wani alheri ba ka yi wa sauran ba, to ya zama bisa wani abu da yake yi su ba sa yi, kuma da ma can ka yi alkawari duk wanda ya kiyaye zaka taimaka masa. Kamar ka saya masa abin hawa don yana zuwa makaranta, kuma duk wanda yake zuwa to shi ma za a saya masa. Tarihin Annabi Yusuf (a.s) shi da babansa (a.s) da wahalar da suka sha ya isa darasi, wannan ba don ya zama laifinsu ba ne, sai don Allah ya fifita shi a kan ‘yanuwansa ne, don haka ne ma da ya yi mafarki duk da baban ya umarce shi da boyewa amma da suka ga ya fi su karbuwa wajan Allah da al’umma sai suka kulla makircin kashe shi, sai dai Allah ya tseratar da Annabinsa Yusuf (a.s). An samu wasu maganganu raunana a tarihi da aka jingina su ga Annabin Allah Ya’akub (a.s), wannan duka badili ne da aka jingina masa, Annabi Ya’akubu (a.s) Ma’asumi ne.
|