Mu'amalar TarbiyyaKada a ba wa yaro aiken babba, domin wannan yana iya sanya shi ya yi kuskure, kuma idan abu wanda yake da nauyi ne ya fi karfinsa kada a ba wa yaron wannan aiken. Haka nan idan yara suna da yawa kada a rika aiken daya kawai; kamar yara uku ne kuma aike shida ne to ya kamata ne a aiki kowanne aike biyu domin ya zama ba a karya zuciyar daya daga cikinsu da jin an takura masa da aike shi kadai ba, ko kuma a raba musu kwanaki shida ta yadda kowanne yana da kwanaki biyu na aike. Sannan aiken ya zama daidai maslahar yaro da su masu aiken nasa a cikin gida, aike yana danganta da yanayinsa da kuma shekarun yaro. Aiken yaro har ya gaji ko a lokacin makaranta ba shi da kyau. Idan mutanen gida suna da aike da zasu yi wa yaro, to ya kamata ne ya zama bisa tsari, da sanin kayyadaddun aike da za a yi masa a rana. Kula Da Yara
Wani lokaci yaro yakan yi laifi sai wasu jama'a ko makoci su tsawata masa, maimakon Uba ya kamo hannunsa wajan makocin ya yi godiya a gaban yaron, kuma ya nuna wa makoci in ya sake a ci gaba da tsawatawa sai ya yi fada da makocin nasa, da haka sai ya rasa mai kula da halin yaron a waje. Shi ya fita kasuwa ko aiki yaro ya fita waje, Uwa ba ta ganin me yake yi Uba ma haka, sai ya yi ta aikata halin banza, ko ya bi batattun mutane, makota kuma don gudun sharrin uban sai su yi shiru. Akwai irin wannan ga wasu mutane; wani mutum da dansa kan jawo mashin din mutane ana tsawata masa don gudun kada ya fado masa, sai yaron ya shiga gida yana kuka, sai uban ya fito yana cewa: Ina ruwansu ya ma mutu mana! Kada a takura wa dansa! Haka nan a kan samu uwa ta yi irin wannan hali sai makota su kyale danta ya lalace, maimakon su iyaye su gane cewa tarbiyyar yara tana bukatar kowa ya sa hannu; makota, da hukuma, da abokai, da ‘yan’uwa, da mutanen gari, sai su ga su kadai ne zasu iya, ta haka sai su cutar da tarbiyyar yaron da haifar wa al’ummarsa yaro maras tarbiyya. Yin godiya ga masu kula da yara abu ne mai muhimmanci a alakar iyaye da hanyar tarbiyyar yara; yana daga cikin hikima a rika godiya ga mai kawo labari game da yara, da kuma mai kula da tarbiyyarsu don a gyara halayensu. Domin hakan zai iya sanya shi ya karfafu wajan taya ka kula da yaronka da tarbiyyatar da shi. Kuma kuskure ne iyaye su dauka cewa su kadai sun isa tarbiyyar yaro, don haka idan an kawo maganar yaronsu yana da kyau su ba ta muhimmanci. Amma ana iya bincikawa a ji gaskiyar lamari, musamman idan ana da kokwanto a kai, sai dai abin da za a kiyaye shi ne mai kawo maganar ya san an ba ta muhimmanci. Idan ka gano cewa ba daidai ba ne, sai ka dauki mataki a kai ta hanyar da ba zai kasance an hukunta yaro ba, shi kuma mai kawo maganar ba zai ji an dauke shi makaryaci ba. Don haka yana bukatar hikima wurin bincike da yanke hukunci kan abin da yake gudana a irin wannan matsayi, wani lokaci yana bukatar ka yi nuni ga wanda ya kawo maganar inda aka samu kuskuren fahimtar abin da ya faru ba tare da gwale shi ba, ko sanya masa jin cewa; ya fadi karya ne. Warware irin wannan matsalar cikin hikima zai sanya yaro ya ji cewa idan an kawo kararsa kana ba wa abin muhimmanci kuma kana hukunta shi a kai, ida kuwa ba haka ba, to zai zama ka karfafa shi ya ci gaba, domin yakan iya cewa da su: Ku fada din me za a yi min? kuma wannan yana iya kai wa ga lalacewarsa. Mutum ko yaya yake kada a yi sakaci wajan tarbiyyarsa domin ta yiwu idan ya girma shi ne zai iya kawo canji ga al’umma, kuma a sani cewa ta sanadiyyar mutum daya ne duk muka zo duniya saboda haka duk mutum yana da kima da muhimmanci. Mu sani gyara mutum daya, gyara gida ne, gyara gida daya shi ne gyara gari, gyara gari daya shi ne gyara jaha, shi kuma gyara jaha gyara kasa ne, gyara kasa gyara ne ga nahiya, wannan kuma shi ne gyara duniya. Da kowane gida a Duniya ya zama salihin gida da wannan yana nufin Duniya ta zama saliha gaba daya, don haka gyara mutum daya shi ne gyara duniya gaba daya. Bai kamata ba a rika kallon gyara yaro kamar gyara mutum daya ne, domin ba a sani ba me zai zama a cikin al’umma da irin canjin da zai iya kawowa a cikinta, shi ya sa masu hikima sukan ce: Mace saliha tsiran al’umma. Ya zama nauyi na farko da ya rataya a kan mutanen gida kamar Uwa da Uba su kusanci ‘ya’yansu, su zama abokansu a gida domin samun damar ba su tarbiyya, wasu mutane sun dauki ‘ya’yansu kamar abokan gaba ne. Wata rana na ga wani mutum da yake cin abinci da abokansa suna hira, yana waiwaya bayansa sai ya ga dansa[1] sai ya kwada masa mari, sai da ya mike tsaye ya sake faduwa har sau biyu, sai kara masa yake yana cewa: Wato Muhammadu da kai ne a nan! Abin haushi da abokan suka zura masa ido kamar suna ganin abin da ya yi daidai ne, ba su ce masa uffam ba.
|