Mu'amalar Tarbiyya1- Aikin iyaye yana daga cikin abu na farko mai tasiri a rayuwar yaransu da alakarsu da su; yaro dan koyi ne, saboda haka tarbiyyarsa a aikace ta fi karfi da tasiri. Da yarinya zata ga kullun mahaifiyarta tana fada da babanta to tayiwu idan ta je gidan miji abin da zata yi ke nan, don haka a guji duk wani mummunan aiki a gaban yara. A nisanci karya da wulakanta mutane, da gulma, da zagi, da sauransu, a dasa karatun Kur’ani, da yin ilimi, da labarun bayin Allah, da gaskiya, da rikon amana, da sallama idan an shigo gida, da godiya ga mutane in sun kyautata, da girmama su, ta haka ne yaro zai iya daukar kyawawan dabi’u a aikace. 2- Canza wurin rayuwa yana da muhimmanci a alakar iyaye da yaransu; Idan kana unguwa ko wani yanki, ko wani gari, da ka san yaronka lallai zai iya lalacewa to yana kanka ka dauki mataki kwakkwara a kai koda kuwa zai kai ga raba shi da wurin, ko barin mai kula da shi daga gurin. Kamar ka ga yaro ba shi da wasu abokai a unguwar sai na banza, kuma ba zaka iya raba shi da su ba, kuma babu wata hanyar gyara sai dai ka bar wurin, ko kuma shi a sauya masa waje, ko garin da aka san zai gyaru ya tashi salihin mutum, to duk wannan yana kan iyaye su yi kokari a kan haka. Duba ka ga Annabi Yusuf (a.s) da zai rasu ya yi wa ‘yan’uwsa nasiha da su bar kasar Masar suka ki, sai bayan kusan shekara dari bakwai zuwa dari tara kamar yadda yake a tarihi sun sha wahala a hannun fir’aunonin Masar sannan Annabi Musa (a.s) ya samu damar fitar da su daga wannan kangi na wahala. Haka ma Manzo (s.a.w) ya bar Makka zuwa Madina don ya gina al’umma ta gari mai karfi da nagarta, kuma gabanin haka ya umarci musulmi da su yi hijira zuwa Habasha. A hirar da gidan talabijin na IRNA channel na shida ya yi da Shaikh Asifi a ranar asabar 16 August 2003 shehin ya nema daga mutunen Iraki da su bar kasashen turai su koma gida saboda gudun lalacewar tarbiyyar ‘ya’ya da canjawar al’adu da tarbiyya, kuma ya kara da cewa: “Kwanan nan wani daga irakawa ya yi masa waya yana gaya masa amsar da wata shugaban makarantar sakandare a daya daga kasashen turai (Jamus) ta ba shi lokacin da ya je neman kada a sanya ‘yarsa a cikin darasin rawa da kide-kide na makarantar, sai shugaban makarantar ta cire tubaranta, ta kalle shi daga sama har kasa, sannan ta ce da shi: Ku sani idan kun iya kare ‘ya’yanku, ko kun ci nasarar tarbiyyatar da su bisa addininku, to ku sani ba zaku iya kare jikokinku daga daukar al’adunmu ba, kuma kuna ji kuna gani ba yadda zaku yi. 3- Saba wa yaro da wata al'ada yana daga cikin abubuwan da suke muhimmai a alakar iyaye da yaransu; Kada iyaye su saba wa yaro da wata al’ada, kamar kodayaushe duk abin da ya tambaya dole ne ya samu, irin wadannan yara duk ranar da aka hana su ko babu, to wannan yana nufin su tayar da fitina da rigima. Haka ma suna iya daukar na wani wata rana domin ba su san su nema su rasa ba, ya kamata a wasu lokutan a saba wa yaro da sauraro zuwa wani lokaci domin ya saba da sauraron warwarar matsalarsa, amma ya danganta da shekarun wadanda suka san babu ne. Haka ma bai dace ba a saba masa da abin da manya ya kamata su sani kamar kudi, ya kamata ne a saba wa yaro da ba shi abin da zai ci a makaranta kamar biskit, ba a saba masa da ba shi kudi yana kashewa ba, irin wadannan yara in ba a lura ba ranar da ba a ba su ba suna iya dauka ko da iyayensu ba su sani ba. Ba a son idanun yaro su san kudi sosai in ba ya haura kananan shekaru ba. Sai dai wannan ba zai iya hana aikensa ba, amma ya zama an rubuta masa takarda ne da aka nade kudin a ciki. Kiyaye irin wadannan abubuwa yakan iya sanya yaro ya saba da dangana idan babu, hakan yakan sanya shi ya nisanci rashin godiya ga iyayen da ganin sun takaita masa wajan kyautatawa, domin idan sun nuna masa su ma suna jira ne zuwa wani lokaci Allah ya buda musu su ma su ba shi, wannan zai taimaka ya san Allah ne yake bayarwa, sannan zai san iyayensa su ma suna nema daga Allah ne, kuma zai koyi tawakkali da dangana da abin da ya samu, da rage masa kwadayi, ko rashin yarda da hukuncin Allah, haka nan zai kara masa sanin cewa akwai Allah kuma shi ne mai bayarwa mai hanawa. 4- Aiken yara yana daga muhimmin abu a alakar yara da gidansu; yana da kyau kiyaye hutun yaro da damarsa a lokacin da ya kamata a aike shi. Kada a aiki yaro lokacin da zai tafi makaranta, wannan yana iya sanya jin rashin son zuwa aiken, kuma shi babba ya kamata ya fahimci cewa yaro yana da nasa hakki kuma babu wani abu da ya kai makarantarsa muhimmanci. Kada a aiki yaro idan ya gaji, saboda haka idan yaro ya gaji a bar shi ya huta, kamar idan ya dawo daga makaranta a gajiye ko daga wani aike da ya gaji, a nan sai a ce da shi tafi ka huta sannan in aike ka waje kaza, wannan yana sanya yaro ya ji dadin zuwa aike na gaba.
|