Babar Babanta!Babar Babanta!
An yi wa Fad'ima (a.s) bazata a wata rana da mutuwar Abu Talib ammin Babanta[1] kuma shugaban Bani Hashim a lokacin ne ta san cewa lallai wani rukuni daga rukunan da Babanta (s.a.w) yakan dogara da su ya rushe saboda haka ta ji muryarsa tana rawa saboda bak'in ciki, fukafukin da yakan tashi sama da su guda biyu an cisge d'ayan musamman saboda tsananin bak'in ciki da ya mamaye zuciya da fuska mad'aukakiya. Sai ta ga Babanta mai daraja (s.a.w) yana kuka a farkon ganin haka a rayuwarta da hawaye masu zafi da ke kwarara a kumatunsa masu albarka a lokacin duk wanda yake wannan duniya ya san cewa lallai akwai zafi da yake tafarfasa a cikin jini da tsuka na Annabin rahama don haka ne ma sai ta motsa da jiki mai haske da albarka ta sanya fararen hannayen nan da suke daga aljanna ne aka gina su, tana mai share masa hawaye masu zafi da fari da ke gudana suna d'iga k'asa kamar ‘ya’yan carbi dunk'ule-dunk'ule, wallahi na so a ce suna zuba ne a jikina domin in shafe su a fuskata domin kada ta samu shafa daga shed'an har abada da takan kai ga toshe mahangar tunani, na kuma shafa a jikina domin kada ya sami k'una na wuta!. Ta kasance tana mai shafewa da hannayenta masu daraja har ta kwantar da zogin da yake ji ta saukar da tafasar nan ta k'unk'unar juciyarsa ta kawar da abin da yake ji na rashi mai tsanani. Amma ba a dad'e ba da ‘yan kwanaki kad'an sai ga musiba mafi girma ta sauka ta kasance, alhali ga wancan mikin bai warke ba aka sake tunb'uke wa Manzon tsira d'aya fukafukin da ya rage, alhali da man ya yi rauni da yake zubar jini maras yankewa. Wayyo Allah!! ba a dad'e ba sai na ji wata kalma da ta fito daga baki mai haske da k'amshin da d'igonsa ya fi k'arfin almiskin da yake cikin duniya gaba d'aya, wace kalma ce? Kalma ce mai nauyi daga haske mai baki mai haske da ake cewa da ita Babar Babanta (a.s) tana cewa: Ina Babata!!. Saboda haka jin wannan kalma ta sanya Manzo (s.a.w) ya ji wani suka da ya fi sukan kibiya ciwo domin uwa ce ta hak'ik'a take tambayar mata ta hak'ik'a da suke da wadancan alak'ok'i biyu da mafi girman halitta (a.s) uwa ce kuma ‘ya amma ba tare da an sami abin da masu ilimin falsafa da suke cewa gewayo ba, wato na farko ya koma na k'arshe, ga hawaye yana zuba kamar ana mamakon ruwa mai kwarara, kai al’umma ku ji wannan kalma mai nauyi da ke k'unshe cikin tambayar uwa ga d'an da yake uba gareta da take cewa ina Babata?!!. Sai Manzon Allah (s.a.w) ya yi kuka kuma duk wanda yake tare da shi a cikin gidan ya yi kuka, Fad'ima ta rankwafa ta shiga cikin lullub'ewar uban (s.a.w) kamar yanda ‘ya’yan kaza suke shiga cikin fukafukan babarsu, kalma ce da tafi abin da ya faru ciwo saboda bak'in ciki ne ya sami uwa da take tafi uwa k'ima domin ita uwa ce daga bakin wahayi daga duniya mai tsarki da nisa daga duniyar ‘yan mariskai, da wannan ma’ana ta duniya da ba mai gane hak'ik'anin ma’anarta sai masu ilimi. Ya girman nauyin wannan tambaya a wannan hali mai wahala da bak'in ciki daga gareta (a.s)!! Saboda haka sai fiyayyen halitta (s.a.w) ya fad'a yana mai lallashin halinta da neman kawar da nata bak'in cikin da ba bak'in cikin da ya kai shi ciwo da zafi, ina iya cewa: bak'in cikin da yake ji sai ya ta fi sakamakon ganin halin da take ciki, saboda haka sai hadafinsa ya zama shi ne k'ok'arin kawar da nata bak'in cikin yana mai fad'a da harshe mai laushi da taushin murya domin sanyayawa ga zuciyarta: "'Yata hak'ik'a Babarki ta tafi aljanna kuma hak'ik'a d'an’uwana Jibril (a.s) ya ba ni labari cewa tana nan a wani gida na k'arau ba wahala ba hayaniya a cikinsa[2]". Haka nan Fad'ima ta zama marainiya ba uwa, ta samu d'aci a rayuwa tana ‘yar shekara takwas d'acin da ba ta tad'a samun irinsa ba sai a lokacin wafatin Babanta (a.s).
|