Kiristoci



Kiristoci

Wannan Hadisi ruwaya ce daga Sadiku Ahlil Bait (A.S) game da tattaunawar Manzo da Ma'abota wannan addini wanda a cikinsa akwai usulubi mai kyau na muhawara da ma'abocin wata Akida da ta saba ta da mai muhawara, wanda a cikinta zamu koyi muhawara da mukabala da munazara da hanyar da take mafi kyau kamar yadda aka yi umarni da (Bil lati Hiya Ahsan). Yana kuma koyar da Hanyoyin kafa dalili Mubashir wato dalili na kai tsaye da kuma Gaira mubashir, da kuma Jawabil halli wato Hanyar warwara da kuma Jawabin Nakdi, wato Hanyar kama mutum da abin da ya yarda ya kuma yi imani da shi. A lokaci guda kuma yana iya nuna mana hakikanin manufar wannan Addini da yadda ma’abotansa suke fassara Akidojinsa. Kuma tana nuna mana yadda aka canja koyarwar Addinin da ya gabata, al'amarin da wannan al'umma ba ta tsira daga irinsa ba ta hanyar riko da Raunanan maganganu ko kuma Tafsirin da ya kafu bisa mahanga ta kuskure da yakan kai ga kurakarai wajan fahimtar Addinin Allah.

Da yake mutane a kowane zamani hali daya ne da su, al’ummar karshe ta Manzon Allah (S.A.W) ma ba ta fita daga irin wannan ba, shi ya sa aka samu sabani da ya kai su zuwa ga rarraba zuwa Mazhabobi da Kungiyoyi na Akida daban daban. Amma wani abin da za a gode wa Allah shi ne al’ummar nan ta bambanta da sauran al’ummu, domin su wadancan al’ummu bayan sun yi nesa da Wasiyyan Annabawan sukan kuma yi rashin sa’ar canza Addinin nasu gaba daya a kuma kautar da Akidunsu daga sahihancinta kamar Yahudawa da Kiristoci da Zartush da Sa’ibawa da sauransu. Amma wannan al’umma Allah ya yi alkawarin kare littafinta, shi ya sa ma duk wanda yake ganin wani yana da Alkur’ani daban da wanda yake hannun musulmi to yana ganin Allah Ajizi ne daga alkwarin da ya dauka na kare littafinsa, kuma irin wadannan mutane suna a matsayin wadanda suka kafirce wa Allah ta hanyar kafircewa Ayar Alkur’ani mai girma.

MUNAZARAR MANZO (S.A.W)

Imam Assadik (A.S) ya ce: "Daga Babana Albakir (A.S) daga Kakana Ali Dan Al-Husain (A.S) daga Babansa Husain Shugaban Shahidai (A.S) daga Babansa Ali Dan Abi Dalib (A.S) cewa, wata rana ma’abota Addinai biyar suka hadu a wajan Manzon Allah (S.A.W); Yahudawa da Kiristoci da Dahariyya da Sanawiyya da Mushrikan larabawa.

Sai Yahudawa suka ce: Ya Muhammad! Mu muna cewa: Uzairu (A.S) dan Allah ne, mun zo mu ga me kake cewa, idan ka bi mu to mun riga ka shiryuwa zuwa ga gaskiya, amma idan ka saba mana zamu yi jayayya da kai. Kiristoci suka ce: Mu muna cewa Isa (A.S) dan Allah ne da ya shiga cikinsa ya hade da shi idan ka bi mu mun riga ka zuwa ga gaskiya amma idan ka saba to ma ja da kai . Dahariyya suka ce: Ya Muhammad! mu muna cewa: Halittu ba su da farko ba su da karshe suna nan har abada, kuma mun zo mu ga me kake cewa, idan ka bi mu mun riga ka fahimtar gaskiya idan kuma ka saba mana to ma ja da kai. Sanawiyya suka ce: Ya Muhammad! mu muna cewa haske da duhu su ne masu juya dukkan ala’amura, mun zo mu ga me kake cewa, idan ka bi mu to mun riga ka fahimtar gaskiya amma idan ka saba mana ma ja da kai. Mushrikan larabawa suka ce: Ya Muhammad! Mu muna cewa: Gumaka Ubangizai ne, mun zo mu ga me kake cewa, idan ka bi mu mu mun fika mun riga ka zuwa ga gaskiya da shiriya amma idan ka saba mana to ma ja da kai.

          Sai Manzon Allah (S.A.W) ya ce: Na yi imani da Allah daya ba shi da abokin tarayya, na kuma kafirce wa duk wani abin bauta ba shi ba. Sannan ya ce Allah (S.W.T) ya aiko ni zuwa ga mutane gaba daya Mai albishir da gargadi ga mutane sannan zai mayar da kaidin duk mai kaidi kansa.

KIRISTOCI

Sa’annan sai ya fuskanci Kiristoci ya ce da su: Ku kuna cewa Dadadde Madaukakin Sarki (S.W.T) ya hade da Masihi Dansa (A.S). Me kuka nufi da wannan magana?. Shin kuna nufin Dadadde ya zama Fararre saboda wannan Fararren da ya hade da shi wanda shi ne Isa (A.S) ko kuna nufin Fararren da yake shi ne Isa (A.S) ya koma Maras farko kamar samuwar Dadadde wanda yake shi ne Allah?. Ko kuma ma’anar ya hade da shi ya shiga jikinsa a wajanku yana nufin ya kebance shi da karama da girmamawa ne wacce bai girmama waninsa da irinta ba?. Idan kuka ce: Dadadde ya koma Fararre to kun rushe, domin Dadadde bai yiwuwa ya juya ya koma Fararre. Idan kuma kuna nufin Fararre ya koma Dadadde to kun yi warwarar magana domin mustahili ne Fararre ya koma Dadadde. Idan kuma kuna nufin ya hade da shi domin ya kebance shi ya zabe shi akan sauran bayi to kun yi furuci da cewa Isa (A.S) Fararre ne da ma’anar ya hade shi saboda haka, domin idan Isa (A.S) ya kasance Fararre Allah (S.W.T) ya kasance ya hade da shi da ma’anar ya sanya shi Mafificin halitta a wajansa to Isa (A.S) ya zama daya daga cikin fararru da wannan ma’ana, wannan kuma sabanin abinda ku kuke bayyanawa ne.

Sai Kiristocin suka ce : Ya Muhammad! yayin da Allah ya bayyanar da abubuwan mamaki a hannaun Isa (A.S) to ya rike shi da ne ta hanyar girmamawa. Sai Manzo (S.A.W) ya ce: Ai kun ji abin na gaya wa Yahudawa a irin wannan ma’ana da kuka ambata sannan ya maimaita abin da ya fada wa Yahudawa dalla dalla, sai suka yi shiru banda mutum daya a cikinsu da ya ce da shi: Ya Muhammad! Shin ba kuna cewa Ibrahim (A.S) Khalilul-Lahi ba?. Sai Manzo (S.A.W) ya ce: Mu Muna cewa hakan. Sai ya ce: Idan kuna cewa haka domin me zaku hana mu cewa haka? (Wato Isa (A.S) dan Allah ne). Sai Manzo (S.A.W) ya ce: Maganganun ba su kama da juna ba, domin ma’anar Khalilul-Lahi an ciro shi daga Khulla wato Bukata da Talauci domin shi ya kasance Mabukaci zuwa ga Ubangijinsa ne, Mai yankewa zuwa gare shi, Mai kamewa ga barin waninsa, wannan a lokacin da aka jefa shi wuta da manjanik (majaujawa) ne sai Allah ya aika jibra’il (A.S) da ka je ka riski bawana, sai ya zo ya riske shi a cikin iska, Ya ce da shi: Ka umarce ni da duk abinda kake so hakika Allah ya aiko ni da in taimake ka, Sai Ibrahim (A.S) ya ce da shi: "Hasbiyal-Lahu Wa ni’imal Wakil, Ni ba na tambayar wani wata bukata sai Shi, ban bukata sai gare Shi". Saboda haka sai ya kira shi da Khalilinsa wato Mabukaci Mai yankewa daga komai sai zuwa gare shi, idan ya zama ma’anar Khulla wato ya tsaya akan wasu sirri da babu wanda ya same su, ma’anar Khulla zata zama masani da sirrinsa, anan babu wani kamanta shi da halittarsa. Shin ba kwa gani ne cewa idan bai yanke zuwa gare shi ba bai zama Khalilinsa ba haka ma idan bai san sirrinsa ba bai zama Khalilinsa ba?. Amma wanda mutum ya haifa ko da kuwa ya wulakanta shi ya nesantar da shi daga gare shi ba ya fita daga kasancewa dansa ne domin ma’anar haihuwa ta tsayu da wannan!?. Sa’anan idan ya wajaba domin ya ce da Ibrahim (A.S) Khalili ku kiyasta ku ce da Isa (A.S) dansa ya wajaba kenan ku ce da Musa (A.S) dansa domin mu’ujizar da take tare da shi ba ta gaza ta Isa (A.S) ba. Sai ku ce Musa (A.S) shi ma dansa ne, kuma ya halatta inda haka ne ku ce da shi: Shaihin Allah ko Shugabansa ko Amminsa ko Amirinsa kamar yadda na riga na gaya wa Yahudawa hakan.

Sai wadansunsu suka ce: Ai a cikin Littafi saukakke hakika Isa (A.S) ya ce: “Ni zan tafi zuwa ga Babana kuma Babanku”. Sai Manzon Allah (S.A.W) ya ce: Idan kun kasance kuna amfani da Littafin ne, to a cikinsa an ce: “Ni mai tafiya ne zuwa ga Babana kuma Babanku”, Idan haka ne ku ce da wadanda Isa (A.S) ya yi magana da su gaba daya ‘Ya’yan Allah ne kamar yadda Isa (A.S) yake dansa ta fuskar da Isa (A.S) yake dansa.

Sa’annan abinda yake cikin wannan littafin yana karyata abinda kuke rayawa cewa Isa (A.S) ya zama dansa ta fuskacin kebanta, domin kuna cewa shi dansa ne ta fuskacin kebantarsa da ya yi da abinda bai kebanci wani da shi ba, sannan kun sani cewa abinda ya kebanci Isa (A.S) da shi bai kebanci wadannan mutane da Isa (A.S) ya ce da su “Ni mai tafiya ne zuwa ga Babana kuma Babanku” da shi ba, sai wannan ya nuna cewa bai kebanta da Isa (A.S) ba domin ya tabbata a wajanku cewa Isa (A.S) ya gayawa wanda bai da wannan matsayi irin nasa, sai kuka hakaito maganar Isa (A.S) kuka yi tawilinsa ba bisa ma’anarsa ba, domin shi da ya ce: “Ni mai tafiya ne zuwa ga Babana kuma Babanku”  abinda yake nufi ba shi ne abinda kuka tafi akai ba. Me ya sanar da ku ko yana nufin ni mai tafiya ne zuwa ga Babana Adam (A.S) ko zuwa ga Nuhu (A.S) kuma Allah zai daukaka ni zuwa gare su ya hada ni tare da su, tare da Adam Babana kuma Babanku, kai ba a binda yake nufi sai wannan. Imam Assadik (A.S) ya ce: Sai Kiristoci suka yi shiru suka ce: Ba mu taba ganin mai wuyar kayarwa mai hujjoji masu karfi irinka ba, zamu je mu duba al’amuranmu.

 Imam Assadik (A.S) ya ce: Sai suka ce : “Zamu duba al’amarinmu”. ya ce: “Na rantse da wanda ya aiko shi (S.A.W) da gaskiya kwana uku bai yi musu ba sai da suka zo wajan Manzon Allah (S.A.W) suka musulunta, sun kasance mutane ishirin da biyar ne; Biyar daga kowace Kungiya. Suka ce: Ya Muhammad! Ba mu ga Mai dalili kamar naka ba, mun shaida kai Manzon Allah ne!!.”



1 next