Al-Mahadi (A.S.)



Al-Mahadi (A.S.)

Lalleyin albishir game da bayyanarMahadi(A.S.) daga 'ya'yan Fatima(A.S.) a karshen zamani domin ya cikakasa da daidaitawa da adalci bayan an cika ta da zaluncida jairci tabbatacce ne daga Annabi(SAW) daga hanyoyin ruwaya daban-daban masu yawa kumadukkan musulmi sun ruwaito hadisi game da haka a bisa mababantan hanyoyinsu na karbar ilimi. Kuma wannan ba wani sabonra’ayi ba ne da Shi’a sukakago shi saboda iza su da yaduwar zalunci da ja'irci ya yi zuwagare shi, har suka yimafarki game da bayyanar wani wandazai tsarkake kasa daga kazantarzalunci kamar yadda wasu 'Yanrikirkitarwa marasa insafi ko adalcisuke kintatawa.

Idan da badon tabbatar akidar Mahadi (A.S.) daga Annabi (SAW) ta yadda dukan musulmisuka sani ba ya kumakafu a zukatansu suka yi imanida shi ba to da masu da'awar imani da Mahadi (A.S.) a karnonin farko kamarsu kisaniyawada Abbasawa da wasu daga cikin Alawiyyawada sauransu ba su iya sun yaudari mutane sun yi amfanida wannan akida wajen neman mulkida shugabaci ba, domin sun sanya da'awarsu ta karyagame da Mahadi (A.S.) hanyartasiri a kan jama'a gama garida kuma yada karbuwarsu a kansu (jama'ar).

Mu kuwa duk da Imaninmu da ingancin addinin Musulunci,kuma cewa shi ne cikamakin addinanUbangiji, kuma ba ma sauraren ­wani addini da zai zo yagyara bil Adama, tare da dukan abinda muka ganina yaduwar Zalunci, da yawaitar fasadi a duniya ta yadda baza a iya samun masakar tsinkeba ga adalci da gyara a kasashe mallakakku, tare kuma da abinda muka ganikuru-kuru na nesantarsu da addinin­su da kansu, da kuma jingine hukunce-hukuncen musulunci da dokokinsa a dukan kasashen musulunci da kuma rashin lizimtuwa ga dubban hukunce-hukuncen musulunci amma duk da haka ba­makawa lalle ne mu sauraribudi yayin da addinin musulunci ya dawo da karfinsa.daiyawarsa da gyaran wannan duniyar da ta dilmiye a cikinrashin gaskiyar zalunci da fasadi.

Sa'annan kuma ba zai yiwuba ga musulunci ya dawo da karfinda shugabancinsa a kan bil Adama bakidaya yana cikin halin da yake cikia yau da ma halin yau din na dagasabanin mabiyansa a dokokin hukunce-hukunce da ma ra'ayoyinsu game da shi tare kumada kasancewarsu a halin da suke ciki a yauna daga bidi'ada fandarewa dokokinsa da ma bata a da'awarsu.

Na'am ba zai yiwu baaddini ya koma ga karfinsa sai dai idan mai gyara babba ya bayyanaya shige masa gaba, yanahada kalma guri guda. kumayana soke abinda aka likamasa na dagabidi’a da bata tare da taimakon Ubangiji domin Ya sanyashi ya zama  shiryayyemai shiryarwa, mai girma da Shugabanci na gaba daya  da kuma iko wanda yasabawa al'ada domin ya cikata da daidaituwa da adalci bayan an cika ta da zaluncidaja’irci ya kuma kubutar da duniya daga halinda take ciki.

Saboda haka ne dukan bangarorinMusulmi suka yi imani da wannanjiran, kai hatta ma al'ummun da ba musulnli basai dai kawaibambancin da ke tsakanin mazhabar Imamiyya shi ne,mazhabarja’afariyya imamiyya ta yi imanicewa wannan mai gyara wato mahadi. Mutum ne ayyananne wandaaka haife shi a shekara hijira ta 256 kuma baigushe ba yana nan da rai, shi shi ne dan imam Hasan askari kuma sunansaMuhammad (A.S).

Ba  ya halatta Imamanci ya yanke koYa katse a wani zamani daga zaminai kodakuwa Imamin a boye yake dominya bayyana a ranar da Allah Ya yi alkawari wandakuma wannan daga cikin asirranUbangiji babu wanda ya san su sai Allah.

Ba  zai gagara ba cewa wannan rayuwatasa mai tsawo da dogon zamaninsa su zama Mu'ujiza da Allah Ta'ala Ya bashi. kuma wannan ba tafi Mu'ujizar kasancewarsa Imami yana dan shekarabiyar kawai ba, yayin      da mahaifnsa yakoma ga ubangiji Madaukaki, kuma bata fi Mu'ujizarAnnabi Isa (A.S) girma ba a inda yayi magana da mutane yana cikinshimfidar jaririnsa yana yaro  kuma aka aike shi Annabiga mutane.

Tsawon rayuwa fiye da dabi'a kuwa  ko kuma ga wanda yadauka cewa ta dabi'a cefannin Likitanci ba zai hanata ba kumaba zai shamakanceta ba, saidai kawai cewa ilimin likita, bai kai matsayinda zai iya kara tsawon rayuwarmutum ba. idan kuw-a har ya gaza aiAllah "ta'ala mai iko ne a kan kome. Kuma haka yafaru tabbatacce akan tsawaitarayuwar annabi Nuhu (AS) da wanzar da annabi Isa (AS) kamar yadda Alkur'aniya bayyana. Idan kuwa mai shakkaya yi shakku game da abinda Alkur'aniya ba da Iabari game da shi to musulunci kam sai watarana.

Abin mamaki ne har Musulmiya tsaya yana tambaye-tambayegame da yiwuwar haka alhali kuwa yanada'awar imani da Littafi Mabuwayi.



1 next