Addinin MusulunciAddinin Musulunci
Kur’ani mai girma mu’ujiza mai dawwama ta Manzon Allah (S.A.W) shi matani ne wanda yake ya zarce matsayin takaita da wuri ko zamani, wannan littafin mai tsarki ya bayar da muhimmanci mai girma ga tarihi, kamar yadda shahid Mudah’hari yake cewa: Kur’ani yana kallon tarihi ta mahanga biyu ne: A - Kallon tarihi a dunkule gaba daya B - Kallon abubuwan tarihi a dalla-dalla Ta mahangar farko tarihi zai tuke zuwa ga aminci da ni’ima da yalwa da mayewar salihai ga duniya. Amma a kan mahanga ta biyu, cancanzawar zamantakewar al’ummu da ya doro a kan sunnar Allah da ubangiji ya sanya. Cigba ko faduwar al’umma, karfi da rauninsu, shugabancin jama’a saliha ko mabarnaciya, dukkaninsu suna bin dokoki ne na al’ummu da alakarsu da wasu al’ummun[1]. Idan mun duba zamu iya tambaya cewa; Wace mahanga ce daga ra’yoyin cancanzawar tarihi da karshen duniya musulunci yake karfafawa? Amma idan muka duba sosai zamu ga musulunci ba ya karfafar kowacce daga wadannan mahangan, ta kamala ce ko ta maimaici ko ta yake-yake. Na farko; Kamalar al’umma da cigabanta ba zai yiwu a dauke shi matsayin wata doka ta gaba daya dawwamammiya ba da za a aiwatar da ita a kowane lokaci[2]. Na biyu; Koda an samu kamalar tafiyar dan Adam da cigabansa a tarihi, amma a mahangar musulunci wannan ba yana zama bisa tilas ba ne. Wato; ba dole ba ne a tarihin dan Adam ya zama kamalar da zai samu a nan gaba tafi ta baya ci gaba, domin idan mun duba zamu ga mutum halitta ne shi da yake da zabin kansa, da ‘yancin zabar abin da ya so. Tafiyar tarihin al’ummu wani lokaci tana yin gaba ne ko ta yi baya, wani lokaci ta yi hagu wani lokacni dama, wani lokacin ta yi sauri wani lokaci kuma sannu-sunnu, wani lokaci ta yi motsi wani lokacin ta tsaya cik waje daya, haka nan ne al’umma wani lokaci take yin sama wani lokaci kuwa ta yi kasa[3]. Na uku; Musulunci yana ganin maimaituwa a tarihin dan Adam maimaici a cikin sunnar Allah, kuma rayuwa da tsayin rayuwar al’ummu wani abu ne karbabbe. Amma wannan tafiyar ba tana nufin tilastawa ba ballantana al’umma ta dawo daga inda ta fara, sai dai yana nufin tarihin yana da wata doka da ka’ida da ba zai iya fita daga cikinta ba, kuma mutum a kowane yanayi ba yadda wannan matsayi nasa na kasancewarsa mai zabi da ‘yanci zai kau[4]. Na hudu; Salsalar tarihi a matsayin musulunci ba ta da wani asasi, wato kowane marhala ba tana damafare da daya marhalar ba ce, domin kowace marhala ana iya sanya ta a mahallin daya marhalar, don haka suna gabata ko jinkirta[5].
|