Ja'irci da Zalunci



Subhanallah! Ashe yin addu'a ga azzalumi zai zama zalunci idan ya ketare iyaka? To mene ne halin wanda ya fara da zalunci da ketare iyaka, yana ketare haddin mutane, yana keta mutuncinsu, yana kwashe dukiyarsu ko kuma ya yaudare su ya aukar da su a cikin halaka, ko ya kuntata musu ya cutar da su ko kuma ya yi leken asiri a kansu? Mene ne halin makamantan wadannan a fikikun Ah1ul-bait (A.S.).

Lalle makamantan wadannan su ne mutane wadanda suka fi kowa nesa da Allah Ta'ala, suka kuma fi tsananin sabo da ukuba, da mafi munin ayyuka da munin dabi'u.

Taimakekeniya da Azzalumai

Saboda girman hatsarin da ke tattare da zalunci da muninsa har Allah Ta'aIa ya hana taimakekeniya da Azzalumai da kuma karkata zuwa gare su.

"Kuma kada ku karkata zuwa ga azzalumai har wuta ta shafe ku. kuma ba ku da wasu Majibinta baicin Allah sa'an nan ba za a taimake ku "

Wannan ita ce ladabtarwar Alkur'ani kuma ladabtarwar Ahlul-bait (AS) riwayoyi da dama da suka zo daga gare su game da hana karkata zuwa ga azzalumai, da sadarwa da su, da yin haraka tare da su a cikin kowane irin aiki da taimakekeniya da su ko da kuwa daidai da kwatankwacin tsagin dibino.

Babu shakka mafi girman abinda aka yi hani a kansa a musulunci da kuma ga musulmi shi ne sassauci ga azzalumai da rufe ido game da miyagun ayyukansa, da mu'amala da su, ballantana ma cudanya da su da taimaka musu, da taimaka musu a kan zaluncinsa.

Babu abinda ya jawo wa al'ummar musulmi bala'o'i illa wancan karkacewa daga kan tafarki madaidaci da gaskiya, har addini ya yi rauni tare da shudewar kwanaki, karfinsu ya zagwanye,suka kai cikin halin da suke a yau. Addini ya zama bako musulmi kuma ko kuma wadanda suke kiran kansu musulmi suka zamanto ba su da wani majibanci baicin Allah kuma ba su da wani mataimaki gare su hatta a kan mafi rauni daga makiyansu da mafi kaskanci masu yi musu hawan kawara, kamar Yahudawa wulakantattu, ballantana kuma a kan kiristoci mafiya karfi .

Lalle Imamai(AS) sun yi jihadi wajen nesantar da duk wanda ke da alaka da su daga taimakekeniya da azzalumai, sun kuma tsananta wa mabiyansu  game da tafiya tare da ma'abuta zalunci da ja'irci da cudanya da su. Abinda aka ruwaito daga gare su game      da haka a wannan babin ba zai gididdigu ba, daga ciki akwai abinda Imam zainul abidin (A.S.) Ya rubuta zuwa ga muhammadu bn muslim azzuhuri bayan ya gargade shi game da taimakon azzalumai akan zaluncinsu?

Ashe kiransu gare ka yayin da suka  ba su sanya ka dan dutsin nika suna juya zaluncinsu da kai ba .da kuma bango da suke ketarawa ta kanka zuwa bala’insu mai da tsanani na bi ta kai zuwa batansu mai kira zuwa ga zaluncinsu, mai         shiga tafarkinsu, suna sanya shakku da kai  a zukatan malami, kuma suna jan zukatan jahilai da kai zuwa gare su.waziransu da mafiya karfinsu da  mataimakansu ba su kai inda ka kai ba wajen nuna ingancin barnarsu, da shiga da ficen kebatattunsu……………………ka diba zuciyarka domin ba mai dubata baicin kai  ka yi mata hukunci, hukunci irin na mutum abin tambaya.

Girman kalmar Ka yi mata hukunci hukunci irin na mutum abin tambaya" ya yawaita. mutum yayin da son ransa ya gallabe shi sai ya mance darajarsa da ke tare da Shi da sirrin karamarsa, wato ma'ana ya ji cewa Shi abin tambaya ne game da ayyukansa, kuma ya kaskanta abinda zai gudana daga ayyukansa sa'an nan kuma ya raya cewa, shi ba shi ne wanda za a yi masa hisabi ba a kan ayyukasa, wannan na daga cikin asirran zuciyar mutum mai umarni da mummuna.   Don haka imam ya so ya fadakar da Zuhuri game da wannan sirri na zuciya wada yake kunshe a cikinsa don kada wahami ya yi galaba akansa har ya yi sakaci game da abinda yake kansa game da kansa.



back 1 2 3 next