Ja'irci da Zalunci



Ja'irci da Zalunci

Ketare haddi ga wani da zaluntar mutane na daga cikin mafi girman abubuwn da Imamai (A.S.) ke girmama yawan zunubinsa, kuma yin haka na tafiya ne daidai da yadda ya zo a Alkur'ani na daga tsoratarwa game da zalunci da kuma kushe shi kamar yadda ya zo a fadar Allah Ta'ala:

"Kada ka tsammaci Allah mai mancewa ne game da abinda azzalumai suke aikatawa, sai dai kawai yana jinkirta su ne saboda ranar da idanduna za su fiffito." (Surar Ibrahim: 42)

Abinda ke kai kololuwar bayyana munin zalunci da kore shi ya zo a maganganun Amirul Muminin Aliyu dan Abi Talib (A.S.) kamar maganarsa, shi mai gaskiya abin gaskatawa, daga maganarsa a khutuba ta 219 a Nahjul Balagha.

"Wallahi idan da za a ba niSammai bakwai da kuma abinda ke karkashin falaki-falakinta a kan in saba wa Allah game da tururuwa in kwace mata Sha'irin da ta jawo ba zan aikata ba."'

Wannan shi ne matukar abinda zai iya surantawa a kan kame kai daga zalunci da kuma nesantar ja'irci da kushe shi.

Shi ba zai zalunci tururuwa ba a kan konon Sha'iri koda kuwa an ba shi Sammai bakwai to yaya halin wanda ke yin dumu-dumu da jinin rnusulmi, yana handame dukiyoyin Jama'a, yana tozarta mutuncinsu da karimcinsu? yaya za a auna tsakaninsa da cikin Amirul Muminin? Kuma yaya matsayin zai kasance a fikihunsa (A.S.)? wannan shi ne irin ladabin da ubangiji ya yarda da shi wanda addini yake bukatarsa daga kowane mutum.

E ,lalle zalunci na daga mafi girman abubuwan da Allah ya haramta don haka ne yake da matsayci na farko a hadisai da addu’o’in ahlul baiti (AS) wajan zarginsa da kuma kore mabiyansu daga gare shi . wannan ita ce siyasarsu (AS) kuma a kanta salon rayuwarsu yake har ma dangane da wanda ke ketare haddinsu yake wa matsayinsu hawan kawara .

Kissar imam hasan (AS) game da hakurinsa ga mutumin Sham wanda ya yi masa tsaurin ido ya zage shi, shi kuwa ya kyautata masa ya tausasa har sai da shi ya ji laifin abinda ya aikata .

Ka dai rigaya ka karanta abinda ya gabata a addu’ar shugaban masu sujada na daga madaukakan ladubba game da yafewa ga wadanda suka ketare haddi da nema musu gafara wanda kuma shi ne matukar daukakar zuciya, da  cikakkiyar ‘yan adamtaka ,koda yake ketare haddi ga azzalumi gwargwadon irin yadda ya ketara din ya halatta a shari'a, kamar kuma yadda yin addu'a a kansa ya halatta mustahabbi ne, amma halattar abu daban kai hatta a gurin Imamai ma (A.S.) yawaita addu'a a kan azzalumai na iya zama keta haddi da zalunci Imam Sadik (A.S.) na cewa: "Bawa na iya zama wanda aka zalunta sai ya yi ta yin addu'a har sai ya zamanto azzalumin."

wato har ya zamanto azzalumi a kan addu'arsa game da azzalumin, saboda yawaitata da yawa.



1 2 3 next