Ladubban SoyayyaK- Kauna Inda Ba Ta Dace Ba
229. Daga Imam Ali (A.S) ya ce: Kada ka bayar da soyayyarka idan ba ka samu wuri ba[29]. 230. Daga Imam Ja’afar Sadik (A.S) ya ce: wanda ya sanya sonsa ba a wurinsa ba, to ya jefa kansa wajen yankewa[30]. L- Neman Adalci
231. Daga Imam Ja’afar Sadik (A.S) ya ce: Neman ‘yan’uwa da yin adalci ba ya daga adalci[31]. 6 / 3 Tattararrun Ladubban Zamantakewa
232. Daga Manzon Allah (S.A.W) ya ce: idan dayanku ya yi abota da wani saboda Allah to kada ya yi masa musu, kada ya juya masa baya, kada ya saba masa[32]. 233. Daga Manzon Allah (S.A.W) ya ce: musulmi dan’uwan musulumi ne, kada ya ha’ince shi, kada ya tabar da shi, kada ya aibata shi, kada ya hana shi, kada ya yi gibar sa[33]. 234. Daga Imam Ali (A.S) ya ce: Kada ka yi yaki da makiyinka, kada ka kyari abokinka, ka karbi uzuri koda kuwa ya kasance makaryaci ne, ka bar amsawa da nuna karfi koda kuwa kai kake da gaskiya[34]. 235. Daga Imam Ja’afar Sadik (A.S) ya ce: Haris dan al’a’awar ya ce da Imam Ali (A.S): ya amirul muminin! ni wallahi ina son ka. Sai Imam (A.S) ya ce masa: ya kai Haris, amma idan kana so na to kada ka yi husuma da ni, kada ka yi mini wasa, kada kuma ka makoce ni, kada ka yi mini raha, kada ka kaskanta ni, kada kuma ka daga ni[35]. Hujjatul Islam Muhammad Raishahari Hafiz Muhammad Sa’id Kano
|